Makalu

Blogs » Tarihin Mutane » Waye Ibrahim Taiwo?

Waye Ibrahim Taiwo?

 • An haifi Ibrahim Taiwo a shekarar 1940, a karamar hukumar Wushishi, ta jihar Niger da ke tarayyar Nigeria. (Bincikenmu bai samo rana wata da kuma kwanan watan da aka haife shi ba). Ya taso a garin Kagara, har ma a lokacin da yake makaranta a kan kirashi da suna Ibrahim Kagara.

  Ya yi Primary dinsa a Senior Primary School Minna, sai kuma Bida Middle School. Ya halarci Provincial Secondary School da ke Okene na dan wani takaitaccen lokaci, inda ya samu shaidar kammala karatun babbar secondary.

  Aikin Soja

  Ya fara shiga aikin damara ne a shekarar 1961, inda ya halarci makarantar Military Training College da ke Kaduna. Sannan ya halarci Mons Officer Cadet School Aldershort. A lokacin da yake sansanin soji, ya yi aiki ne a matsayin Mechanical Transport Officer. Ya zama Officer commanding 2 Brigade Transport, a Apapa Lagos. Ya zama Staff Captain Army Headquarters a garin na Lagos. Ya kara zama Officer in charge na 8 Brigade a garin Asaba, sannan Officer in charge of the Transport company a Kaduna.

  A lokacin yakin Biafra shi ne shugaba a bangaren zirga-zirga da kuma rarraba sojojin yaki a kowane sansani  na sojojin Nigeria.

  Rawar da ya taka a lokacin juyin mulkin Nigeria a watan July 1966

  A lokacin  juyin mulkin Nigeria a shekarar 1966, wanda Chukwuma Kaduna Nzeogwu ya jagoranci sojoji, wadanda mafi yawancinsu ‘yan kabilar Igbo ne, juyin mulkin da a shi aka yi asarar rayukan manyan mutanen kasar nan, irin su;  Sir Ahmadu Bello, Sir Abubakar Tafawa Balewa, Samuel Ladoke Akintola, da kuma ministan kudi na wancan lokacin wato  Festus Okotie-Eboh, Ibrahim Taiwo shi ne Captain na rundunar sojojin da aka ajiye don su bayar da tsaro a Yaba da ke Lagos. A tare da shi akwai manya-manyan hafsoshin soji, wadanda suka haxa da:

  2nd Lieutenant Sani Abacha

  Lieutenant Muhammadu Buhari

  Lieutenant Ibrahim Bako

  Lt.  Colonel Murtala Muhammad

  Major Theophilus Danjuma

  Wadannan da ma wasunsu sune suka taka rawar gani wajen ganin abinda ya faru bai faru ba a lokacin juyin mulkin na 1966. Saboda yadda suka nuna damuwarsu a zahiri da kuma badini ga yunkurin sojoji bisa jagorancin Ironsi na hargitsa al’amuran mulki na wancan lokacin, wanda ya assasa juyin mulkin a ranar 15 ga watan Janairu na shekarar 1966.

  Amma kasha! Taka-tsan-tsan bata maganin kaddara.

  A lokacin yakin kuma Ibrahim Taiwo na daga cikin mutane uku  jajurtattu  masu aikin kwaso mutane daga garin na Asaba zuwa mafaka. Sun yi namijin kokari wajen bayar da kariya tare da kubutar da dubunnan mutane a ta’addancin garin Asaba, shi da General Murtala Muhammed, da Ibrahim Haruna. Shi ke kula da kuma tsara yadda aka kwaso dubunnan mutanen da ake zalinta a garin na Asaba, cikin nuna kwarewar aiki ta ban mamaki. Wannan aiki da ya yi ya sanya Nigeria ta shiga cikin kundin tarihi na kasar da ta kware wajen iya kubutar da ‘yan kasa a lokacin yakin cikin gida.

  Har ila yau Kanal Ibrahim ya yi gwamnan jihar Kwara daga shekarar 1975 zuwa 1976.

  Mai karatu na iya duba tarihin Magajin Garin Zazzau, Malam Nuhu Bamalli.

  Rawar da ya taka a lokacin juyin mulkin Nigeria na shekarar 1975

  Taiwo ya taka muhimmiyar rawa a lokacin juyin mulkin da yayi awon gaba da Yakubu Gowon sannan ya kawo Murtala Muhammad.

  A karkashin aikinsa ne aka dinga shigo da sojoji tare da rarraba musu wajen aiki. Sun yi wannan aikin kafada da kafaxa tare da Lt. Col.  Muhammadu Buhari.

  A ranar Laraba 30 ga watan July 1975 aka cire karfin ikon mulkin da General Yakubu Gowon ke da shi, aka maye gurbinsa da General Murtala Ramat Muhammad, a wani juyin mulki mai kama da na ruwan sanyi. A karkashin kulawarsa, tare da aikin shigo da dakarun  soji, gami da rarraba musu wurin aiki, shi da Muhammadu Buhari.

  Mutuwarsa

  An kashe Kanal Ibrahim Taiwo ne a ranar Juma’a, 13 ga watan February 1976, a wani yunkuri na hambarar da shugaban gwamnati na wancan lokacin, wato General Murtala Muhammad, juyin mulkin da Lieutenant Colonel Buka Suka Dimka ya jagoranta, sai dai bai yi nasara ba. Amma a yunkurinsa na kaucewa harin, wasu rukunin sojoji bisa jagorancin Dimka din suka farfasa motar Murtala Muhammad, wanda yayi sadaniyyar rasa ransa tare da na mai taimaka masa na musamman wato Lieutenant Akintunde Akinsehinwa.

  Kanal Ibrahim Taiwo ya rasu ya bar iyali, a ciki har da magajinsa a aiki, wato Brigadier General Ahmad Ibrahim Taiwo.

  Ibrahim Taiwo na daga cikin mutanen da har yau har gobe wasu daga cikin ‘yan kabilar Igbo ke matukar jin haushi, tare da farin cikin mutuwarsa, bisa zarginsa da suke yi na cewa yana da hannu dumu-dumu wajen kashe daruruwan mutane, ‘yan kabilar Igbo din, wadanda basu ji ba basu gani ba a garin Asaba.

  Tarihi ba zai taba mantawa da Colonel Ibrahim Taiwo ba saboda tasirinsa ga ‘yan Nigeria. Akwai tituna da dama da aka sanyawa sunansa a garuruwa mabanbanta a Nigeria, misali: Ibrahim taiwo road Kano, Ibrahim Taiwo road Ilorin, da sauransu.

  Matashiya: Wannan takaitaccen tarihi na Kanal Ibrahim Taiwo an hada shi ne ta hanyar nazarin littattafan tarihi daban-daban. Idan har akwai wani kuskure, sai a rubutowa Taskar Bakandamiya a adireshinmu na imel: admin@bakandamiya.com tare kuma da cikakken bayani mai gamsarwa. In Allah Ya so za mu gyara. 

  Rubutawa: Zaharadden Nasir, daga Kano, Nigeria

Comments

1 comment