Rubutu

Blogs » Muhawarar Bakandamiya 2020 » Tsakanin zafi da sanyi wanne ya fi amfani ga lafiyar dan adam?

Tsakanin zafi da sanyi wanne ya fi amfani ga lafiyar dan adam?

 • A ci gaba da kawo muku yadda muhawarar Zauren Marubuta na Manhajar Bakandamiya ta guda na, karawa ta uku za ku ga yadda kungiyoyin Nguru Writers Association da Zaman Amana Writers Association suka yi tsayuwar gwamin jaki a taken muhawararsu mai cewa: TSAKANIN ZAFI DA SANYI WANNE NE YA FI AMFANI GA LAFIYAR DAN ADAM? Kowace kungiya ta kawo hujjojinta wadanda ke bayyana alkiblarsu a gwabzawar. Muhawarar ta wakana ne a ranar 26/11/2020.

  Ga yadda muhawarar ta kaya:

  Zafi ya fi amfani ga lafiyar dan Adam.

  Matashiya/Gabatarwa

  Masu girma jagororin wannan muhawara, masu girma alkalai, abokan fafatawarmu a wannan zama, 'yan'uwa masu bibiyar wannan muhawara; assalaamu alaikum wa rahmatullah.

  Kamar yadda aka gani, muna kare Kungiyar Nguru Writers' Association of Nigeria kan batun da za ta kaya da abokiyar muhawararta. Inda mu za mu bayyana cewa, zafi ya fi amfani ga rayuwar dan Adam.

  Nguru Writers Association of Nigeria (NWAN)

  Hujja ta Farko I

  Dalilin da ya sa na ce zafi ya fi amfani ga jikin dan’adam shi ne: a likitance gumi yana da matukar muhimmanci a jikin dan’adam. Kuma shi wannan gumin ba a samun sa sai a lokacin zafi. Akwai wasu kwayoyin halitta a jikin dan’adam (sweat glands); wanda aikin su kawai shi ne su fitar da gumi a jikin mutum, ba dan komai ba, sai dan zafin jikin mutum ya sauka. Hakan na hana shi saurin kamuwa da zazzabi. To kun ga a nan zafi ya amfani lafiyar dan’adam sosai. Wanda a lokaci na hunturu babu wannan damar.

  Hujja ta Biyu II

  Sannan zafi na da matukar muhimmanci ga rayuwar dan’adam ta hanyar walwala da sakewa. A lokacin zafi mutane da dama sun fi samun yancin sakewa; su yi rayuwarsu cikin sauki ba tare da takura ba.  Za ku ga maza na samun damar zama a waje su zanta da abokanan hirarsu, koma a cikin gida  tare da iyalansu. Wanda hakan ba ya samuwa a lokacin sanyi.

  Hujja ta Uku III

  Zafi shi ne lokacin da dan’adam ke samun kansa cikin kyawun jiki, ta yadda jikinsa ba za a ga ya tsattsage ba, musamman mutumin da yake da gautsin fata, wanda kuma fatar kafarsa ke tsagewa.

  Hujja ta Hudu IV

  Sannan a lokacin zafi ba a samun yawaitar barayi masu tsallaka gidajen mutane. Saboda sawu ba ya daukewa da wuri. Sannan lokaci ne na kwanciyar waje, akwai motsin mutane.

  Hujja ta Biyar VI.

  Rashin zafi a jikin mutum na nuni da cewa wannan mutumin ba shi da cikakkiyar lafiya ko ma babu lafiyar gaba daya.

  Daga cikin amfanin zafi ga lafiyar dan’adam, shi ne hanya ce ta gwada temperature (ma’aunin zafi) a jikin mutum, wanda ba a son temperature a jikin mutum ya wuce 36 degree (ma’aunin celcius). Idan ya wuce haka, to akwai matsala, wato ba lafiya.

  Karkarewa

  Masu girma jagorori, alkalai, abokan muhawararmu, sauran masu bibiya. Da wadannan dalilai namu, ya sa lalle za mu fahimci zafi ya fi sanyi amfani ga lafiyar dan’adam, wanda a lokacinsa ake kamuwa da cututtuka; musamman mura wadda take zama silar sauran cututtuka, da rashin samun kuzari da makara wajen ayyuka, da buya daga al’umma.

  Wassalamu alaikum.

  Jiddah Haulat Nguru daga kungiyar Nguru Writers Association

   

  Sanyi ya fi amfani ga lafiyar dan Adam

  Gabatarwa

  Shugabanni gasa, wakilan gasa, alƙalai, ƴan uwana abokan muhawara, ƴan uwana marubuta, masu saurare Assalamu Alaikum.

  Sunana A’isha Sa’eed Abubakar (Aishan Umma) ni ce wakiliyar ‘ZAMAN AMANA WRITER’S ASSOCIATION’. A yau muna gabanku tare da bada amanna cewa lallai SANYI YA FI ZAFI  MUHIMMANCI GA LAFIYAR ƊAN ADAM, saboda hujjojina kamar haka:

  Hujja ta Farko

  Shi sanyi ni’ima ce kuma rahma ne ga al’umma, duba da tushen sanyin da zafin, yanayin jikin al’umma da yawa ya bambanta da na wasu.

  Da yake yanayin jinin jikinmu mai ɗumi ne, hakan ya sa jikin ba ya iya jure wa yanayin zafin da ya kai 37 a ma’aunin salshiyas.

  “YO AI GUNTUN GORO YA FI BABBAN DUTSE”

  A yayin da zafin muhallin da muke zaune ya ƙaru, jiki ba ya iya jurewa zafin, ta yadda idan zafin gari ya daɗe har ya fi na cikin jikinmu yawa zai zama barazana ga lafiyarmu.

  Idan zafi ya kai sama da 37°C yana da haɗari sosai. Ko da a lokacin da zafin yake a 30°C ya kamata mu fara ɗaukar matakin kare kanmu.

  Mutane kan fuskanci jiri da ciwon kai har da suma idan zafin ya kama su.

  Hujja ta Biyu

  Illar zafi ga jiki:

  Da farko-farko yakan haddasa kumburi da kuma ƙurajen zafi.

  Tsananin zafi kan haddasa ƙuraje da ɗaɗewar fata waɗanda ke buƙatar kulawar likita.

  Bugun zuciya.

  Idan mutum ya kamu da cutar tsananin zafi na tsawon lokaci to zai iya haifar masa da bugun zuciya.

  “Yin gumi zai janyo kafewar ruwan jiki, wanda kuma yake rage yawan jini a jiki. Kazalika shi ke saka zuciya ta kasa tunkudo jini da karfi yadda ya kamata,” kamar yadda Ony Stubbs, shugaban cibiyar ya faɗa Australian Heart Foundation.

  Cutar tsananin zafi na faruwa ne yayin da ɓangaren hypothalamus a cikin ƙwaƙwalwa, wanda yake da alhakin kula da ayyukan sauran sassan jiki kamar yin gumi.

  Hukumar kula da ayyukan kiwon lafiya a Birtaniya (NHS) ta ce: “Cutar tsananin zafi kan faru yayin da zafin jiki ya wuce 40C, wanda hakan ke hana ƙwayoyin halitta da sauran sassan jiki yin aiki yadda ya kamata.”

  Idan hypothalamus ya gaza yin aiki, jikin ɗan adam kan gaza yin aiki yadda ya kamata, saboda haka sai ya kasa bayar da kulawa ga yanayin gumin jiki.

  Waɗanda abin ya shafa za su iya fuskantar matsalar numfashi da ciwon kai da ɗimaucewa. Idan dai har ba a samu kulawar gaggawa ba, to gaɓoɓin jiki ka iya daina aiki wanda kuma zai iya kai wa ga mutuwa,” in ji NHS.

  Mutuwa.

  Dubban mutane ne ke mutuwa a kowacce shekara saboda cutuka masu alaƙa da yanayin zafi.

  Yo ai “HANGEN DALA BA SHIGA BIRNI BA. KUMA KALLON KITSE A KEWA ROGO”. Ban da haka babu abinda ma zai sa mutum ya yi tunanin zafi zai fi sanyi muhimmanci a jikin ɗan Adam.

  Sanyaya jiki ka iya bayar da kariya daga cutar tsananin zafi

  Mutane ka iya mutuwa cikin ‘yan sa’o’i idan zafin gari ya wuce 38°C zuwa 42°C tare da daukewar iska, inda a lokacin nan jiki ba zai iya jurewa ba.

  Amma idan mutum ya samu waje me sanyi, inuwa ko ƙasan bishiya zai taimaka masa wajen rage masa zafin jiki da ka iya illa.

  Hujja ta Uku

  Mutum zai iya kare kansa daga haɗarin kamuwa da cutar tsananin zafi ta hanyar yin wanka akai-akai domin ya ji sanyi.

  Sannan da sanyi zakuga yawaitar masu wari yana raguwa, amma da zafi sai dai muce SubhanAllahi!

  Da wannan nake so alƙalai suyi duba da hujjojina su gane cewa sanyi ya fi zafi  muhimmanci ga jikin ɗan Adam. TO MENE NE MA HAƊIN KIFI DA KASKA?

  Bissalam

  Aisha Saeed Abubakar (A’ishan Umma) daga Kungiyar Zaman Amana Writers Association

  A nan aka kammala muhawarar karawa ta uku, muna jiran ra’ayoyin ku ga dukkan bangarorin biyu.

  Ku latsa nan don karanta muhawa ta hudu.

Comments

0 comments