Rubutu

Blogs » Kagaggun Labarai » Illar Furuci 5 Na Halima Abdullahi K/Mashi

Illar Furuci 5 Na Halima Abdullahi K/Mashi

 • Ku latsa nan don karanta shafi na 10 da 11.

  SHAFI NA 12

  Takwas na dare Fatima tana ta faman daukar hoto a waya tana editing tana yin posting a shafukanta.

  Nafisa ta leka ta kalli fuskar wayar, sannan ta dubi Fati ta ce "Yaya Fati malam ya yi mana nasiha akan daukar irin wadannan hotunan a gantsare ba bu kyau, kuma ya ce duk yarinyar da.....

  "Yimin shiru mayyar sa ido kawai, ni tauraruwa ce, mutane suna son kallon hotunan taurari kuma suna kwaikwayon irin salon daukar hotonmu da irin sa kayanmu."

  Nafisa ta sake duban ta cikin yar dariyar zolaya ta ce "Su tauraruwa manyan gari, to Film ki ke yi ko waka?"

  Fati ta ce. "Ina ruwanki ne wai!" Nafisa ta ce " babu ruwa na."
  Faruk ya shigo da gudu. "Mama tana kiran kowa a zo a ci abinci.'

  Nafisa ta dube shi. " Faruk so nawa zan fada maka, ka daina shigowa da gudu babu sallama ne? Oya koma ka yi sallama tukunna."

  Ya koma ranshi a bace sannan ya sake yin sallama. Nafisa ta amsa sannan ta ce "Gamu nan zuwa yanzu."

  Bayan fitar shi, ta dubi Fati Ta ce " "Tauraruwa ki tashi mu je mu ci abinci." Fati ta ce "Ni ba zan ci da kowa ba."

  Nafisa ta bata rai tare da fadin. " Baba bayason abin da kike yi sam, mu fa kannanki ne amma bakya janmu a jiki ba na jin dadi nima."

  Fati ta maido kallonta ga Nafisa. "Amma ba ki lura da Baba ya fi son ku fiye da ni ba? Ya takura min yasa idon sa a kaina, ku kuma baya yi muku haka, shiyasa nake janye jikina daga cikin ku na tsaya ga Mama wadda ke sona."

  Nafisa ta ce "Yaya Fati duk Baba ya fi son ki kalli can." Ta nuna mata hoton da ke manne a bango.

  Ita ce da Baban a lokacin bikin tunawa da zagayowar ranar haihuwarta, yar shekaru biyar ce lokacin ga cake ga kalolin lemuka sannan ga yar karamar mota wadda Baban ya sai mata .

  SHAFI NA 13

  Fati ta tsurama hoton idanu, tana tuna lokacin a idon zuciyarta. Ta numfasa sannan ta ce "Nafisa hakika Baba ya so ni amma a da, bansan meyasa yanzu ya tsane ni ba."

  Nafisa ta ce "Har yanzu Baba yana sonki fiye da kowa a gidan nan, halayanki ce bayaso in ya ce ki bar abu ba kya bari kuma sai Mama ta na goyon bayanki."

  Fati ta taba baki. "Ni banga wani abu da nike yi ba."

  Nafisa ta ce " Yaya ko ni nasan da dama cikin abubuwan da ki ke aikatawa, kuma har yanzu hankalin su Baba bai kai gurin ba. Kina gudu daga makaranta, kina hotuna marasa dacewa ki na posting din su, kuma ba kya zuwa computer school kuma 'yan ajinmu sun fada min sun ga hotunanki a manne a titi duk da ban gani ba na san cewa ke din ce."

  Fati ta ware ido cikin mamaki tana kallon Nafisa. Sannan ta ce "wai dama Nafisa haka kika sa min ido ke ma?"

  Nafisa ta ce " Ban sa miki ido ba Yaya, abin da kike yi a bayyane ya ke, ki daina ki koma kamar yadda muka taso."

  Mama ta yi sallama. kafin Fati ta furta wani abu. Dukkansu su ka kalle ta tare da amsawa, ta ce "Wai zaman me kukeyi ba za ku zo ku ci abinci ba?" Nafisa ta ce "Mama Yaya ce wai Ita bazata ci da kowa ba."

  Mama ta ce "Kutaso muje."

  Dukansu babu wadda ta ce uffan haka suka mike zuwa gurin cin abincin.

  Katuwar tabarma ce aka shimfida a gurin da aka tanada domin cin abinci. Faruk da Kabir da Amir suna ci a kwano daya. Fati ta kalli abincin.

  Faten doya ne na mangyada ya ji kifi bushashshe.

  Wani irin kallo Baba ya watsoma Fati, ta sunkuyar da kai cikin fargaba. "Sannu da gida Baba." Ta furta cike da in ina. Ya amsa cikiciki. Suka zauna su ka dauki na su kwanon su ka bude kular abincin su ka zuba su ka koma gefe.

  Wayar Fati ta soma ruri ta kalli fuskar wayar, gabanta ya fadi ta kalli Mama da wadda ke cin abincinta, ta maida idanunta ga Baba ya zuba mata idanu cikin tuhuma ta kuma kallon fuskar wayar GIDAN HOTO haka ta rubuta da manyan baki.

  Kiran ya na daf da zai tsinke ta daga. "Hello ya ku ke?" Ta furta cikin nuna rashin tsoronta dan kar iyayenta su fahimci wani abu. Ya ce "Za ki iya zuwa yanzu kuwa?" Ta ce "Akwai wani abu ne?" Ya ce. "E wasu ne za ayi musu hoton tallar atamfa, to yariyar ta karya musu alkawari sun gaji da jiranta.

  Ta mike da sauri ta nufi dakinsu ta na fadin "Yanzu haka kuna tare ne?" Ya ce "Muna tare da su yanzu haka." Ta ce "To ganinan zuwa." Ta shiga kai kawo a cikin dakin ta na tunanin yadda za ayi ta fita. Can dabara ta fado mata cikin sauri ta nufi gurin iyayanta dauke da karyar da za ta shirga musu...

  Ku latsa nan don ci gaban labarin.

  Za ku ji me Fati celebrity za ta fadawa iyayanta! 

  Taku, Halima K/Mashi

Comments

0 comments