A wannan karawar ta hudu (K4) mai taken, ‘Wa ke da laifi a matsalar fyade, gwamnati ko iyaye?’ kungiyoyin marubuta, Rumbilhak Writers Association da kuma Strong Pen Writers Association sun yi ruwan hujjoji domin fito da matsayarsu fili. An yi wannan muhawarar ne a ranar 26 ga watan Nuwamba, 2020, a zauren Marubuta da ke Manhajar Bakandamiya.
Ga yadda muhawarar ta kaya:
Gwamnati ke da laifin afkuwar fyade
Gabatarwa
Assalamu alaikum, alkalan gasa da masu bibiyar mu tare da sauran abokan karawa ta wannan muhawara aminci a gareku.
Na tsaya anan ne domin kare ko sanar da duniya cewa laifin fyade gwamnati ke da laifi saboda dalilai na kamar haka:
Hujja ta Farko
Ya kamata a ce gwamnati ta ɗauki mataki akan kowa idan har aka kama yaro ko tsoho da laifin fyaɗe, saboda gwamnati na da wannan damar da za ta yaƙi kowa ba tare da gazawa ba ko karaya duba da yadda rayuwa ta koma ɓata yara ba’a ɗauke shi a bakin komai ba. Kuma masu aikata laifin nan sun samu dama ganin gwamnati ba ta ɗaukar matakin da ya dace akan wannan babbar matsalar.
Shin gwamnati ko kinsan a rana yarinya nawa a ka yiwa fyaɗe.?
Ko kinsan kalar raɗaɗi da zugin da ke ji a lokacin da aka yiwa yarinya fyaɗe.?
Idan ya zama gwamnatin tasan wannan bata ɗauki mataki ba dole kuwa laifi ya zama nata.
Hujja ta Biyu
Yanzun an wayi gari ana samun cases na fyaɗe har hakan ya janyo kyama ga ƴaƴa mata, da yawa daga cikin yaran da aka yiwa fyaɗe hakan ya janyo masu tsangwama wajen mutane musamman maza, sai ka ji ance ai ƴar isaka ce fyaɗe aka yi mata, ko ace ita takai kanta musamman idan yarinya ta manyan ta, sai kaga ta shiga cikin garari ta dalilin haka ma za ku ga wasu ko makaranta sun daina zuwa saboda tsangwama da ƙiyayyar da ake nuna masu, wajen kawayen su ko kuma sauran mutanan gari ana nuna yarinya ana cewa ƴar iska ce.
Ko gwamnati tasan duk wadannan abubuwan da yake faruwa ta yaya ba za ta zama mai laifi ba? Ku duba irin durƙushewar da ƴaƴa mata suke yi a lokacin da kaddarar fyaɗe ta afka masu, da yawansu sun bar neman ilimi dan gudun abin magana da ake masu, duk wannan ba naƙasu ba ne a rayuwar ƴaƴa mata ba?
Hujja ta Uku
Ta ya ya al’umma za ta kai hakkin dake bibiyarta middin za a dinga cin zarafin ƴaƴa mata musamman yara, da yawa daga cikin masu wannan fyaɗen suna amfani da yara wajen jan ra’ayinsu da yi masu alkhairi. An sha ɗaukar yarinya ‘ƴar shekara ɗaya zuwa biyu ai masu fyaɗe shin suma waɗannan laifin sune? Ko a ɗauke budurwa ta ƙarfi a lalatata itama wannan laifin tane.? Na san wannan amsar ba ta wuce a'a, idan ko har haka ne ya kamata gwamnati ta farka daga nauyayyen baccin da take yi wajen kwatarma ƴaƴa mata hakkinsu akan azzaluman samari har ma da dattawa, sannan muddin magidanci ya ce zai dinga lalata yaran mutane shi ma za a yiwa na shi, amman mu ba haka muke so ba, muna son gwamnati ta ɗauki mummunan mataki akan duk wani azzalumi dake cikin wannan harkar ta haikewa ƴaƴa mata.
Hujja ta Hudu
Gwamnati ita ce mai iko da kowa, ita za ta iya hukunta kowa kuma ko dan waye, amma iyaye basu da ikon hukunci ga wani mutum idan ba ƴaƴansu ba, kenan dole dai gwamnatin ce mai laifi.
Da yawan masu fyaɗe rashin hukunci ne yake sawa su kara yi, kananun yara da basu san komai ba, wasu basu da gata gwamnati ce gatan kowa amma ta bari bata kula ba.
Idan aka kama mai fyade aka kai shi kotu ko da an yanke hukuncin, wasu ba sa haura wata daya sun fito, shin anan lefin waye? Tabbas iyaye ba su da laifi a matsalar fyade laifin yana gurin gwamnati.
Hujja ta Biyar
Iyayen dai suna kokarin kula da yaransu amma da zarar sun fita sai fyaden ya faru, shin da gwamnatin ta bada tsaro ga mata hakan zai faru?
Da wannan nake sallama ga Alkalai da sauran masu bibiyar wannan muhawara tare da abokan karawa, wassalamu alaikum.
Jamila Abubakar Bello daga kungiyar Strong Pen Writers Association (MANAZARTA)
Iyaye ke da laifin afkuwar fyade
Kungiyar Rumbilhak Writers Association, ba su samu damar kare kansu ba, da za mu ji ra’ayinsu kan yadda laifin fyaɗe ya danganta da iyaye. Muna jiran naku ra’ayoyin.
Sai mun hadu a muhawarar karawa ta biyar K5, in sha Allah.
No Stickers to Show