Rubutu

Blogs » Kagaggun Labarai » Tekun Labarai: Afuwa ƙwaya Ce, Ka Shuka Ɗaya Ka Girbi Goma

Tekun Labarai: Afuwa ƙwaya Ce, Ka Shuka Ɗaya Ka Girbi Goma

 • Ku latsa nan don karanta labarin Dogaro Ga Allah Jari.

  Cikin ƙasashen Mongol an yi wani babban Sarki mai yawan jarumai ana kiran sa Bihikatu. Shi wannan Sarki jarumi ne amma mugu ne na ƙin ƙarawa. Tun da yake bai taɓa yin afuwa ga wanda ya saɓa masa ba. Ba a taɓa ganin dariyarsa ba sai a kan ƙeta. Don haka jama'a ke shayinsa ƙwarai da gaske. Wata rana ya fita farauta shi da mutanensa, sai wani hadiminsa ya ɗauki mashi ya jefa sama. Mashin kuwa ya dawo sai ya karci Sarki a kunnensa har ya tsarga shi biyu. Sarki ya fusata ya ce a nemo wanda ya jefa mashin nan. Aka shiga aka taho da wannan hadimin mai suna Yatari, aka gurfanar gaban Sarki. Sarki na ganin sa ya ce a tafi a kashe shi.

  Yatari ya kada baki ya ce, "Allah ya ba ka nasara, wallahi ba da sanina na jefo mashin inda kake ba, iyakar sanina wajen babu kowa, ban san kana wurin ba. Ina neman afuwarka domin girman Allah. Ka ji ƙaina, sai Allah ya ji ƙanka a ranar ba ka buƙatar komai sai jinƙan." Da wannan sai Sarki ya ji sanyi a ransa, ya yafe wa Yatari aka sallame shi.

  To shi wannan hadimin, ɗan Sarki ne da ya yi wa ubansa laifi ya gudu, ya je ƙasar Sarki Bihikatu yana masa hidima. Ana nan sai ubansa ya samu labarin inda yake, ya aiko masa da takarda yana mai cewa ya yafe masa laifin da yayi masa amma bisa sharaɗin ya koma gare shi. Da saƙon ya same shi sai ya shirya ya sulale ba tare da sanin Sarki Bihikatu ba, ya koma wajen mahaifinsa. Uban ya karɓe shi da girmamawa ya ba shi muƙami, sannan ya yi masa aure gudun kada ya sake guduwa.

  Wata rana Sarki Bihikatu ya shirya jirgi tare da jama'arsa, suka shiga ruwa domin farautar kifi suka nausa. A tsakiyar teku sai guguwa mai ƙarfi ta taso, ta buga jirgin nasu da wani ƙaton dutse. Jirgin ya farfashe, jama'a duka suka hallaka, wasu kuma suka warwatse cikin ruwa. Sarki Bihikatu ya kama wani allon jirgi, da ƙyar ya tura shi zuwa wata gaɓar teku. Ya kwanta a nan cikin wahala bai san inda kansa yake ba, duk kayan jikinsa sun yayyage ana ganin tsiraicinsa. Wannan gaɓar tekun da ya tsinci kansa kuwa, nan ne garin da uban Yatari ke mulki. Da gari ya waye mutane suka fito, sai suka ga wani mutum a kwance an kashe shi, gefe ɗaya kuma ga wani matsiraici nan kamar mahaukaci a kusa da gawar. Sai suka ce, "wannan mahaukacin ne ya kashe mutumin nan." Suka kama shi suka kai wajen Sarki. Wahalar da ya sha a teku ta sa ko magana ma ba ya iya furtawa. Sarki ya yi umarnin a kai shi kurkuku a ɗaure, kafin a duba al'amarinsa.

  A cikin kurkukun Bihikatu ya yi ta nadamar abubuwan da ya aikata wa mutane na zalunci da rashin afuwa. Yana cikin wannan halin sai wata tsuntsuwa ta sauka bisa katangar gidan da yake. Da yake shi mutum ne mai son farauta sai abin ya motsa masa. Ya ɗauki wani dutse mai kaifi ya jefe ta da shi. Tsuntsuwar ta tashi, dutsen kuma ya wuce kai tsaye wani ɗan Sarki ƙanin Yatari na wasan doki, dutsen ya same shi a goshi ya faɗo daga dokin jini na ta zuba.

  Fadawa suka garzaya neman wanda ya yi wannan jifa, aka gano shi, aka cukumo wuyansa zuwa ga ɗan Sarki, ya ba da umarnin a kashe shi. Nan da nan aka zarga masa igiya aka ƙunƙunce hannayensa, za a rufe masa ido ke nan sai ɗan Sarki ya ga kunnensa a yanke, sai ya ce, "dama can kai mai laifi ne, ga kunnenka nan a yanke shaidar ka taɓa aikata laifi a baya aka yi maka haka." Bihikatu ya ce, "ba haka ba ne wallahi, dalilin yankewar kunnena shi ne abu kaza." Ya ba shi labarin sarautarsa da yadda aka yi kunnensa ya tsage. Yayansa Yatari na ciki yana jinsu. Da ya ji Bihikatu na ba da labarinsa sai ya fito ya ce, "ko kai ne Bihikatu?" Ya amsa, "ƙwarai kuwa ni ne."

  "Ka shaida ni?"

  "A'a ban shaida ka ba."

  "Ni ne wanda ka yi wa afuwa yayin da na yi jifa da mashi ya yanke maka kunne." Ya yi umarnin a kwance shi, ya tafi da shi wurin mahaifinsa, ya nuna shi yana mai cewa mahaifinsa, "shi ne Sarkin da ya yafe min alhali bai taɓa yi wa kowa afuwa ba.” Sarki ya marabce shi, ya zaunar da shi, sannan ya shirya masa liyafa.

  Bayan ya huta Sarki da 'ya'yansa suka shirya masa dukiya mai yawa tare da bayi da hadimai suka aika da shi zuwa garinsa ya ci gaba da mulkinsa."

  Yaro ya dubi Sarki ya ce, "to Allah ya ba ka nasara ka ji yadda afuwa take tsiruwa ta girma har ta hayayyafa ta zama bishiya. Da a ce Sarki Bihikatu ya kashe Yatari, babu shakka shi ma da ya rasa ransa. Ita afuwa komai ƙanƙantar ta ba ta taɓa tafiya haka a banza." Da Sarki Shamsuddini ya ji haka, sai ransa ya yi sanyi ya ce, "a mayar shi kurkuku kafin gobe mu gani."

  RANA TA 8

  Tun cikin dare Wazirai ke ta tattaunawa a tsakaninsu game da al'amarin wannan yaro. Babbansu ya ce, "kun ga dai wannan yaron na son ya faskare mu a wajen Sarki da surutunsa. To kuwa muddin muka yi sakaci ya samu kansa to mu kashinmu ya bushe. Don haka ku tashi mu tafi gaba ɗaya mu yi wa Sarki magana da murya ɗaya domin ya kawo ƙarshensa mu huta."

  Sarki na jin haka ya tunzura ya fusata iya wuya, ya daka tsawa ya ce “a kawo yaro gabana!” Aka shigo da shi a ɗaɗɗaure. Wazirai suka kalle shi gaba ɗayansu suka ce da shi, "tir da halin maci amana irinka!" Sarki ya ce a yi maza a kirawo hauni saboda yau ya makara zuwa fada. Wazirai suka hau kokawa tsakaninsu, kowa na cewa a ba shi takobi shi zai fille wa yaro kai. Yaro ya dube su ya ce, "don me kuke gaggawa domin sharri, alhali ba ku da hujja a kan da'awarku? Ko dai hassada da makirci ke damun ku?" Sarki ya ce masa, "dube su ka gani mana, Wazirai na ne su goma, gaba ɗayansu sun haɗu a kan ka aikata laifi, babu ɗayansu da ya goyi bayanka." Yaro ya yi murmushi ya ce, "ya Sarkin zamani, ka rabu da sabgar waziran nan naka, domin babu abin da ke damun su sai hassada da ha’inci da makirci. Muddin kuwa ka yarda da zancensu irin wannan da ba su da masaniyar komai a kai, to babu shakka wata rana za su sanya ka kuka da idanunka. Haka nan kuma za su iya jefa ka cikin nadama a lokacin da bata da amfani. Ni ina jiye maka tsoron yin nadama irin ta Aylanu Shahu, saboda makirci da sharrin waziransa." Sarki ya ce, "mene ne labarinsa?" Yaro ya ce, "bari ka ji."Da gari ya waye gaba ɗaya Wazirai  suka faɗi gaban Sarki suka ce, "Allah ya ja zamaninka, ka tuna cewa ka ɗauke mu aiki ne domin ba ka shawara da duba maka game da al'amarin da zai sa ka samu nasara a mulkinka. Mun duba sha'anin wannan yaron babu alheri ko kaɗan tare da shi, muddin ba ka kashe shi ba. Wannan ya tabbata abin kunya na ƙarshe, Sarki ya kama mutum kwance kan gadonsa amma ya ƙyale shi saboda kaifin bakinsa. Mun tabbata da wata niyyar fasiƙanci ya je wurin. Ya Sarkinmu, idan ba za ka iya kashe shi ba saboda tsoronsa da kake ji, to muna baka shawarar ka kore shi daga ƙasar da kake mulki, kuma ka hana kowa ya raɓe shi."

  Ku latsa nan don ci gaban labarin.

  Danladi Z. Haruna

Comments

0 comments