Makalu

Blogs » Kiwon Lafiya » Me ku ka sani game da cutar Hepatitis?

Me ku ka sani game da cutar Hepatitis?

 • Idan aka ce Hepatitis, to ana nufin ciwon hanta kenan a Hausance. Hepatitis ya kasu iri daban-daban har guda biyar, inda suka hada da; Hepatitis A, da Hepatitis B, da Hepatitis C, da Hepatitis D, da kuma Hepatitis E.

  Hukumar Lafiya ta Duniya ta ce kimanin mutum miliyan 325 ke fama da ciwon hanta nau'in B da C a duniya. A yayin da ciwon hanta nau'in B kawai ke lashe rayuka 900,000 duk shekara.

  Har wa yau, hukumar lafiyar ta ce, kaso 10 cikin 100 ne kawai na masu fama da cutar hanta nau'in B da kuma kaso 19 cikin 100 na masu fama da ciwon hanta nau'in C suka san suna ɗauke da cutar.

  Wannan na nuni da miliyoyin mutane da ke fama da ciwon hantar amma basu sani ba, kuma hakan na faruwa ne saboda ƙarancin zuwa asibiti domin gwajin ciwon hanta akai-akai.

  Haka nan, kaso 42 cikin 100 ne kawai na yaran da ake haifa a faɗin duniya suke iya samun allurar rigakafin ciwon hanta nau'in B bayan haihuwarsu. Saboda haka hukumar ke sake jaddada kira game da yaɗuwar cutar daga uwa zuwa jariri cewa, ya kamata dukkan jarirai su sami rigakafin ciwon hanta nau'in B bayan haihuwarsu.

  Sai dai kuma bincike ya nuna cewa Hepatitis A, Hepatitis B, da kuma Hepatitis C su ne suka fi wanzuwa tsakanin mutane.

  Alamomin ciwon hanta

  1. Ciwon ciki
  2. Zafin Jiki
  3. Amai
  4. Tashin zuciya
  5. Kasala
  6. Baƙin fitsari
  7. Idanuwa su yi kalar dorawa da jiki
  8. Ƙaiƙayin jiki
  9. Bahaya kore

  Ga ɗan bayani akan cutar Hepatitis A,B,C,D,E a kasa:

  Hepatitis A

  Kwayar cuta mai suna Hepatitis A virus ce ke haddasa shi. Ana kamuwa da shi ne ta hanyar gurɓataccen abinci ko ruwan sha wanda ya gaurayu da kashin wani mai ɗauke da cutar, wanda ƙwari ke yaɗawa, sannan ya fi yaɗuwa ne a ƙasashen da tsaftar muhalli ke da karanci.

  Hepatitis B

  Ƙwayar cutar hepatitis B virus ce ke haddasa wannan rukuni na ciwon hanta, wanda ke yaɗuwa a cikin jinin mutumin da ya kamu da ita. Ana kamuwa da shi ne idan aka sanya wa mutum jinin mutumin da ke dauke da shi, yin amfani da allura ko reza, ko wasu karafa masu dauke da kwayar cutar. Haka zalika ana dauka daga uwa zuwa danta, da kuma saduwa da wanda ke dauke da cutar.

  Ku karantaCutar kansar mama: Hatsarurruka da hanyoyin kariya daga cutar

  Binciken lafiya ya nuna cewa cutar hanta wato Hepatitis B ta zamo cutar da ke kisa a boye.

  Masana harkar lafiya sun ce cutar ta fi kisa fiye da cutar Malaria a shekara. Binciken ya ce kimanin mutane miliyan 257 ne ke fama da cutar samfurin 'B' a duniya, kuma Najeriya na daga cikin kasashe biyar da ke da kashi 60% na masu fama da wannan cutar. An ware ranar 28 ga watan Yulin ko wace shekara a matsayin ranar ciwon hanta ta Hepatitis.

  Hepatitis C

  Ana kamuwa da shi ne ta kwayar cutar Hepatitis C. Yana yaduwa ne ta hanyar sanya wa mutum jinin wanda ke dauke da ita.

  Hepatitis D

  Ana kamuwa da shi ne ta kwayar cutar Hepatitis D. Yana shafar mutumin da ya riga ya kamu da cutar hepatitis B ne, domin yana bukatar kwayar cutar hepatitis B kafin ya iya tsira a jikin mutun. Yana yaduwa ta hanyar sanya wa mutum jinin mai dauke da ita da kuma saduwa da wanda ke dauke da cutar. Dadewar wannan cuta na iya sa mutum kamuwa da cutar dajin hanta.

  Hepatitis E

  Ana kamuwa da shi ne ta kwayar cutar hepatitis E. Sannan akan kamu dashi ne ta hanyar cin danyen naman alade. Wannan baya dadewa a jikin mutum, sannan baya bukatar kowani magani, amma ya kan munana a cikin wasu mutane.

  Wasu daga cikin matakan kariya sun haɗa da:

  1. Tattaunawa da likita kan ɗaukar alluran rigakafin ciwon hantar.
  2. Kada a yi amfani da allura, reza ko burushin goge baki da wani ya ke amfani da su.
  3. Ga masu juna biyu, tattauna da likita kan yadda za a kare yaɗuwar cutar zuwa jariri.
  4. A yi amfani kaɗai da abubuwan yanka jiki (kamar askar aski ko askar tiyatar likita) da aka tsabtace su daga dukkan ƙwayoyin cuta.
  5. A lizimci amfani da kwaroron roba (condom) ko da yaushe yayin saduwa da wanda ke ɗauke da cutar ko haɗarin kamuwa da cutar.
  6. Idan zai yiwu,a zaɓi shan ƙwayar magani maimakon yin allura.

  Haka nan mutum na cikin haɗarin kamuwa da ciwon hanta

  1. Idan an taɓa yi maka aiki/tiyata a jiki ko a haƙori da kayan aikin da ba a tabbatar da an tsabtace su daga dukkan ƙwayayyakin cuta ba.
  2. Idan an taɓa ƙara maka jinin da ba ai masa gwajin cutar hantar ba. Kuma aka tabbatar babu cutar.
  3. Idan mahaifiya na ɗauke da cutar yayin da aka haife ka.
  4. Idan kana ɗauke da cutar ƙanjamau ko cuta mai karya garkuwar jiki.
  5. Idan an yi maka allura da allurar ko sirinjin da aka yi wa wani allura da ita.
  6. Idan kana cin abinci ko abin sha da ya lalace ko mara tsabta.
   Tabbatar an yi maka gwajin ciwon hanta domin sanin matsayinka a yau!

  Dubi:Cutar Typhoid: Alamunta, hanyoyin kamuwa da kariya daga gare ta

  Gwaje-gwaje

  A jerin gwaje-gwajen jini da ake kira hepatitis viral panel ana yin su ne don wadan da ake zargin suna da cutar hanta. Hakan zai  iya taimakawa wajen gano:

  1. Sabon kamu da cutar
  2. Tsohuwar cutar da ke aiki har yanzu.
  3. Wanda yana da cutar amma bata nuna ba.

  Ana yin waɗan nan gwaje-gwaje ne  don ganin yanda  hanta ta lalace ga waɗan da cutar hepatitis B ta yi tsanani.

  • Albumin Level
  • Gwajin aikin hanta (Liver function test).
  • Prothrombin time

  Hakanan za a yi gwaji don auna matakin HBV a cikin jini (ƙwayoyin cuta).  Wannan yana bawa mai kula da lafiya damar sanin yadda maganin ya ke aiki.

  Mutanen da ke cikin haɗarin kamuwa da cutar hanta ya kamata a bincika ta hanyar gwajin jini.  Ana iya yin wannan koda lokacin da basu da alamun bayyanar cutar ne.

   Mutane daga ƙasashe inda yawancin mutane suke da cutar hepatitis B. Waɗannan ƙasashe ko yankuna sun haɗa da Japan, wasu ƙasashen Bahar Rum, sassan Asiya da Gabas ta Tsakiya, Afirka ta Yamma da Sudan ta Kudu.

  Jinya (treatment)

  Cutar hepatitis wacce ta girma, ko mai tsanani ne, baya buƙatar magani.  Ana kallon hanta da sauran ayyukan da jiki ke yi ta amfani da gwajin jini.  Ya kamata ga mai cutar ya sami hutu isasshen hutuk shan ruwa mai yawa, da cin abinci mai kyau.

  Wasu mutanen da ke fama da cutar ciwon hanta akai akai za a iya ba su  magungunan ƙwayoyin cutar don kawar da ita.  Wadannan magunguna na iya ragewa ko cire hepatitis B daga cikin jini.  Daga cikin magungunan shine allura da ake kira interferon.  Hakanan suna taimakawa wajen rage haɗarin cutar cirrhosis da ciwon hanta.

  Ba ko yaushe ba ne bayyane mutanen da ke fama da cutar ciwon hanta ta B ya kamata su karɓi maganin ƙwayoyin cutar ba.  Zai yiwu ku sami waɗannan magunguna idan:

  1. Aikin da hantar mutum ke yi ya tsananta.
  2. Bayyanar alamun cutar na lokaci mai tsawo.
  3. Mutum wanda ya ke da matakin HBV a cikin jininsa.
  4. Mace mai ciki

  Don waɗannan magunguna suyi aiki da kyau, ana buƙatar ɗaukar su da muhimmanci kamar yadda likita ya umurta.  Ba duk wanda ke da ciwon hanta ne idan ya  shan waɗannan magunguna za su yi masa aiki da kyau ba.

  Idan har hanta ta gaza aikinta yanda ya kamata har tai kai ta samu matsala sosai, za a iya la'akari da sai an yi dashen wata.  Dashen hanta shine kadai magani a wasu lokuta.

  Sauran matakan da za a iya ɗauka:

  • Guji shan giya.
  • Binciki likita kafin shan kowan magani .  Waɗan nan magunguna sun haɗa da acetaminophen, aspirin, ko ibuprofen.
  • Ciwon hanta mai tsanani, ko kuma cirrhosis, na iya haifar da hepatitis B.
  • Wasu mutane suna amfanuwa da halartar ƙungiyar tallafawa cutar hanta.
  • Outlook (Tsinkaya)
  • Cuta rashin lafiya mafi yawanci yakan tafi bayan makonni 2 zuwa 3. Sannan ya kan dawo daidai cikin watanni 4 zuwa 6 a yawancin mutane.

  Allurar rigakafin ciwon hanta

  Allurar riga kafin ciwon hanta wasu allurori ne guda uku zuwa hudu da ake yi na tsawon watanni shida. Ba'a kamuwa da ciwon hanta matukar an yiwa mutum alluran riga kafin cutar.

  Rukanan mutanen 13 da aka shawarta suyi allurar rigakafin ciwon hanta sun hadar da:

  • Jarirai sabuwar haihuwa
  • Kananan yara da kuma masu tashen balagar fari wadanda ba a yiwa rigakafi ba bayan haihuwar su.
  • Wadanda suke aiki ko kuma rayuwa a alkaryoyin da babu ci gaba.
  • Wadanda ke zama ko kuma rayuwa cikin masu cutar Hepatitis B
  • Ma'aikatan lafiya da kuma ma'aikatan bayar da agajin gaggawa da kuma wadanda ke alaka da jini.
  • Wadanda suka kamu da kowace irin cuta ta hanyar saduwa, da suka hadar da cuta mai karya garkuwar jiki wato HIV.
  • Masu yawaita saduwa da mutane daba-daban musamman karuwai.
  • Masu abokin saduwa mai dauke a cutar musamman miji ko mata.
  • Masu yiwa kawunan su alluran kwayoyi na maye.
  • Mutane masu matsananciyar cuta hanta.
  • Masu matsananciyar cutar koda.
  • Matafiya masu niyyar kai ziyara yankunan da cutar hanta ta yi kamari.
  • Maza masu neman 'yan uwan su maza.

  Ku karanta:Kansar mafitsara: Ire-ire da hanyoyin kariya da kamuwa da ita

  Karin wadanda suka kamata a yi wa rigakafi

  • Yara da manya da ke cikin haɗarin kamuwa da cutar hepatitis B ya kamata su sami rigakafin hepatitis B.
  • Ya kamata jarirai su fara shan allurar riga kafin cutar hepatitis B lokacin haihuwa. Ya kamata su sami dukan allurar daga watanni 18 zuwa shekara uku a cikin jerin shekaru 6
  • Yaran da shekarunsu ba su kai 19 ba da ba su yi allurar rigakafin ba ya kamata a yi musu alluran.
  • Yaran da aka haifa da iyayen da ke dauke da cutar hepatitis B ko kuma suka kamu da cutar a baya ya kamata su sami allurar rigakafin cutar hepatitis B ta musamman a cikin awanni 12 da haihuwa.
  • Allurar rigakafin cutar hepatitis B ko kuma maganin hepatitis B na rigakafin globulin (HBIG) na iya taimakawa wajen rage kamuwa da cutar idan ka karba ta tsakanin awanni 24 da saduwa da kwayar.
  • Matakan don kauce wa mu'amala da jini da ruwan jiki na iya taimakawa hana yaduwar cutar hepatitis B daga mutum zuwa mutum.

  A nan muka kawo karshen wannan makala. Allah Ya ba mu lafiya da zaman lafiya. Kuma kar ku manta, wannan makala an rubuta ne domin karuwan ilimi, idan mutum bai da lafiya likitanshi ne kawai zai ba shi magani. 

  Rubutawa: Maryam Haruna, a registered midwife, daga Zamfara, Nigeria

Comments

2 comments