Makalu

Blogs » Zamantakewa » Yanayin so da bukatuwarmu gare shi

Yanayin so da bukatuwarmu gare shi

 • Zamantakewar aure, zamantakewa ce mai wahala, matuƙar wahala kuwa. Sai dai da zarar ka fahimci tana da wahalar, sai ta zama mai sauƙi a gare ka. Domin fahimtar tana da wahalar shi zai ba ka damar neman iliminta. Shi kuma iliminta sai ya ba ka damar samun sauƙin ta.

  A shirinshi da ya saba gabatarwa a Zauren Marubuta da ke manhajar Bakandamiya, Malam Hamza Dawaki, na yin sharhi da kawo bayanai masu zurfi daga kusfa-kusfar yadda za ku yi rayuwa mai dadi tare da iyalanku, harma da samari da ‘yammata dake shirin shiga wannan gida na aure.

  Wannan makala, cikin bayanan Malamin dalla-dalla, ta kawo jigo kuma mafarin kome, wato ‘so’.

  Da Sunan Allah Mai Rahma Mai Jin Ƙai

  Bukatuwarmu ga so

  Kalmar so, ita ce kalma mafi muhimmanci a kafatanin kalmomin da suke cikin kamus’. Sai dai kuma a lokaci guda, ita ce mafi rikitarwa. Malamai tun daga kan na addini har zuwa na zamani dukkansu sun yarda cewa so yana da wata gagarumar rawar takawa a cikin rayuwar dan adam. Idan ka so ma, ka iya cewa so shi ne ya zaunar da duniya lafiya.

  Mashahuran wake-wake da littattafai da makaloli da finafinai da ake yawan ambato, dukkansu za ka tarar suna ‘dauke da kalmar so a wurare da dama cikinsu. Ture batun masanan falsafa da dabi’un dan adam, Jagoranmu Annabi Muhammad Sallallahu alaihi wa sallam ya kwadaitar da mu ga yin soyayya!

  Bukatawarmu ga soyayya daya ce daga cikin bukatun ruhi na tun fil azal. Wadanda ba yadda za ka yi ka raba mutum mai lafiyayyen tunani da su. Soyayya ce take ba mu juriyar iya hawa kan dogon dutse, mu ratsa teku, mu yi tattaki a cikin sahara komai sanyi ko tsananin zafinta. Tabbas ba don so ba, da ba mu iya irin wadannan ayyukan ba.

  Ma’aurata da masu neman auren suna amfani da ita: “Ina son ki!” Tsakanin ‘ya’ya da iyaye ka ji ana: “Ina son mamana!” Mutum da wani abin kiwo da yake yi, zai iya cewa: “Ina son magen nan!” kuma ba ta bar ayyuka ko wasanni da muke yi don nishadi ba. Mukan ce: Ina son ‘kwallon ‘kafa, muna son tsereren mota. Ko abinci, tana son taliya, yana son rake, suna son kankana, yana son nama. Muna son yanayi da tsirrai, yana son damina, tana son filawa, yana son bishiyoyi. Balle kuma mutane, muna son ‘ya’yanmu, iyayenmu, matanmu, abokai da kawayenmu, dangi da makwabta. Kai shi kansa ma son muna son sa!

  Karanta dalilai 11 da ke sa namiji ya so mace matuka.

  Matsalarmu da so

  Babbar matsalarmu da so ita ce ba mu iya shi ba. Da gaske ne muna son so, kuma mafi yawan mutanen da muke cewa muna so da gaske ne son su muke yi, sai dai babban matsalar da muke ba wa shi kansa so din ita ce tuƙin ganganci da muke yi a cikinsa.

  Zaton da muke yi wa so kawai tamkar wata dabba ce (jaki ko doki) ta kakanka, wadda in aka ɗora ka ko daga ina ne, aka bar ku, za ta kawo ka har gida kai tsaye, ko da kuwa ba ka yi mata tsaya ko yunƙurin nuna mata hanya ko sau ɗaya ba, domin dama tuni ta san hanyar gidan, wataƙila ma tun kafin a haifeka.

  Amma mota ko mashin da keke ba za su taɓa irin wannan ba. Su, saɓanin doki ko jaki, dole sai ka koye su. Kuma bayan ka koye su, duk lokacin da za ka yi mu’amula da su ma sai ka nutsu kana sarrafa su a sannu. Saboda ka tabbata in ka yi ganganci da su sai ka cutu, maimakon ka samu biyan buƙata.

  To kamar kuma haka soyayya take. Dole ne ka koye ta, kuma ka koyi yadda ya kamata ka riƙa sarrafa abokin zamanka. Da yadda za ka riƙa tattalinsa ya daɗe, kar ya tsufa da wuri. Da yadda za ka yi masa tuƙi na tsanaki, ba na ganganci da zai gwafgwafje ya raƙwarƙwaɓe da wuri ba. In kuma ba haka ba, to ba mamaki ɗayan abu biyu ya faru:

  Ko dai ka yi karo, ya watse ko ma ya mutu. Ko kuma ku yi hatsarin tare duk ku ragargaje. 

  Yaya son yake ne?

  Idan har yanzu ba ka fahimci cewa kalmar so tana da matukar rikitarwa ba, yi nazarin wannan yanayin:

  Mutum zai yi zina da mace, amma idan ka tambaye shi dalili sai ya ce: “Na yi hakan ne saboda ina son ta.” Amma a wurin maiwa’azi wannan saɓo ne. Matar mashayi ta fusata wataran ta yi masa dukan tsiya! A tunaninta don tana son sa ne. Amma a wurin masu kare hakkin dan adam, wannan cin zarafi ne! Iyaye za su iya takure yaro, su hana ɗansu kusan dukkannin abubuwan da ya ji ransa yana so. Kuma su ce sun yi haka ne saboda suna son sa. Amma a wurin masana tsarin rainon iyali waɗannan iyayen sunansu ragwayen iyaye, wadanda ba su iya tarbiyyar da rainon yaro ba. To wai yaya son yake ne?

  Maƙasudin samar da wannan muƙala, ba wai warware dukkanin sarƙaƙƙiya ko rikitarwar da ke tattare da soyayya ba ne. A’a, manufar ita ce samar da wani lafiyayyen yanayi na soyayya, wanda zai iya taimaka mana cikin zamantakewarmu da iyali da sauran abokan rayuwarmu.

  Soyayya ce ginshikin aure

  Duk da irin juye-juyen da za a yi, daga karshe, dole mu dawo mu yarda cewa wannan soyayyar ita ce kashin bayan zamantakewar aure, musamman idan ana batun lafiyayyen aure.

  Wani magidanci ya ce.

  “Ina amfanin wasu kayan alatu, wani kyakkywan gida da mota da lambun shakatawa da dangoginsu idan har matar mutum ba ta son sa?” Ya kara da cewa. “Ina son soyayyar matata fiye da komai a rayuwa.”

  Ashe kenan, da haka muna iya fahimtar cewa, dukkanin wani kayan alatu da dukiya da kowane ma kyale-kyale da za ka iya tunowa, ba sa iya cike ko maye gurbin so a zuciyar mutum. Watakila kuma wannan shi ya sa sau da yawa muna gani, sai mutum ya zabi talaka a matsayin abokin rayuwa, tare da cewa akwai mai hannu da shunin da yake son sa.

  Wata matar aure ta ce. “Mutum ba ruwansa da kai, ba shi da lokacinka duk tsawon wuni, sai dare ya yi ya zo ya ce zai kusance ka! Na tsani wannan abun!”

  Amma ainihin al’amarin shi ne, ba wai kusantar ce ba ta so ba, babbar damuwarta kawai ita ce, ta rasa soyayya. Don haka, duk wani abu da za a yi tunanin zai burge ta, ba zai iya burge tan ba, mudin dai ba ta samu wannan son ba.

  Bukatuwarmu ga so wani abu ne da baya taba rabuwa da zukatanmu. Kowanne mutum kuma da yake cikin yanayin soyayya, ba zai samu cikakkiyar gamsuwa cewa lallai ana son sa, kuma ya mori nishadin da yake cikin soyayya ba, har sai an tsaya a kusa da shi, an tabbatar masa da hakan.

  Wannan shi ya sa tun lokaci mai tsayi, baƙuntarwa ta kasance daya daga cikin manyan hanyoyin horon dan adam. Shi ne kuma har yanzu ake yi yayin da ake so a gana wa mutum azaba sakamakon wani laifi da ya aikata, kai tsaye kawai sai a kai shi gidan yari a kulle. Wannan ko da babu wani horo da ya shafi duka da danginsa, ya ishe shi azaba, saboda a kalla babu shi ba ganin masoyansa.

  To shi aure an shirya shi ne ta yadda zai zama wani yanayi mafi cikar burin masoya, mafi iya bayar da dama gare su, ta su gwangwaje, su baje kolinsu na nuna wa juna soyayya, saboda suna da cikakkiyar damar kasancewa tare kullum.

  Amma babban abin tambayar a nan shi ne, wai me yake faruwa ne son yake guduwa bayan an yi aure?

  Anan za mu dakata, ku daka ce mu a lokaci na gaba. Muna sauraron naku ra’ayoyin.

  Hamza Dawaki, daga Kano, Nigeria

Comments

1 comment