Makalu

Blogs » Kagaggun Labarai » Illar Furuci 6 Na Halima Abdullahi K/Mashi

Illar Furuci 6 Na Halima Abdullahi K/Mashi

 • Ku latsa nan don karanta shafi na 12 da 13.

  Shafi Na 14

  Tana isowa ta dubi Mama tare da mika mata wayar "Ga mamansu Sumayya za kuyi magana."

  Mama ta amshi wayar ta saka akunne ta na fadin salamu alaikum jin shiru yasa ta dubi fuskar wayar tare da fadin "La kinga ta katse."

  Fati ta amshi wayar ta na fadin Network ne yau mtn abin na su babu sauki, dama a jakata ranar da naje Sumayya ba lafiya wai ashe ta saka sakamakon gwajin ta na asibiti a jakata kinsan irin ta ta ce, shine gobe za su koma ta ce ko zan kawo mata...
  "Babu inda za ki." Baba ya tari numfashinta.

  Mama ta ce "Garin yaya har takardun asibiti su ka shiga cikin jakarki?" Fati ta dan razana a zatonta ko Mama ta soma tuhumarta, amma sai ta boye razanar da nuna ko in kula ta ce

  " Ina zan sammusu Maman su ta ce Anty yayar su Sumayya ta taho zata amsa, in ta iso zata kirani in ta sauka a unguwar nan tunda bata san gidan nan ba."

  Mama ta ce "To babu laifi, je ki ciro kafin ta kira." Fati ta juya ta koma cikin jin dadin ta samu damar saka kafa a waje.

  Mama ta kalli Baba. "Ka ga irin gajen hakurin har kana babu inda zataje, to gashi aikowa za a yi." Ya ce "Data canza salo ba." Mama ta bata rai tare da "Fadin shike nan kaci gaba da zargin da ka ke mata".

  Bai sake fadin komai ba sai ma wayarsa da ya dauka ya na dannawa.

  Fati ta koma daki cikin sauri ta saka hijabi da takalmi da naira dari ta jefa wayarta a karamar jaka ta fi ce da sauri sauri gudu gudu.

  KANO

  Acikin makarantar Hassan Gwarzo Fatima da Fadila suna tafe cikin jerin daliban da suka fito dan zuwa masallaci yin sallar isha i daga can su wuce gurin cin abincin dare.

  Fadila ta dafa kafadar Fatima ta ce "Kawata dan Allah in mun dawo suratul Maryam zaki kara min tilawarta." Cikin mamaki Fatima ta waiwayo ta dubi Fadila ta ce "sonawa zan koya miki suratul Maryam?"

  "Wai ma ina hankalinki yake lokacin da ake koya Mana karatu! Gaskiya na gaji."

  Fadila ta marairaice tana fadin "Haba kawata wannan shine karo na karshe akan wannan surar bazan kuma tambayarki ba, da asubahin gobe zan kawo haddarta zan sha duka in ban kawo ta ba."

  Fatima ta yi dan tsaki, sannan ta ce Allah kin saka wani abu a ranki ne wanda ya hana ki rike abinda ki ka zo don shi, wancan satin fa an dakeki kafin ki kawo hadda kuma ada ba haka ki ke ba."

  Fadila ta danyi shiru kamar me nazarin maganar Fatiman.

  Can ta ce. " Ina zaton wannan matsalar tana da nasaba da labarin da Anty matar Yayana ta zo min dashi lokacin ziyara."

  Fatima ta ce "Wane
  labari kenan?"
  Cikin mamaki Fadila ta ce "Ban fada miki ba?" Kai Fatima ta girgiza tare da fadin "Bana zaton munyi maganar."
  Fadila ta ce "To bari in munje kwanciya zan fada miki."

  Bayan sun kammala komai suna zaune bakin gadon Fatima wadda ta zaku ta ji labarin da ya taba lissafin kawarta har ya sa ta kasa rike karatu.

  Fadila ta ce "Ai na zaci na fada miki ashe ba muyi zancan ba, amma na taba baki labarin Ya Hashim ?"

  Fatima ta danyi shiru alamun son ta tuna domin tabbas ta san sunan.

  Can ta ce. "Na tuna da wanda suka taba zuwa da Yayanku har ki ka ce dan wan Babanku ne amma a gidanku ya girma ko yana karatu a Dubai?"

  Fadila ta ce "Shine kuwa a nan BUK ya yi Degree dinsa masters dinsa ce ya yi a Dubai." Yana aiki a Central bank.

  Fadila ta numfasa sannan ta dafa kafar Fatima ta ci gaba da fadin. "Kawata tunda na taso tun ina karama komai na Ya Hashim barge ni ya ke yi daga baya sai na fahimci son Ya Hashim nakeyi, nayi matukar kokari gurin boye wannan son yadda ba bu wanda ya gane har shi.
  Addu "a ta daya kullum nakeyi Ubangiji ya taimake ni ya cusa masa sona ya kasance shine mijina.
  To zuwan su Yaya da Anty sai Anty ke bani labarin wai an saka masa ranar aure da wata yarinyar abokin mahaifinsa ce.

  Na tambayesu kuma ya na sonta ne tunda naga shi bai damu da harkar mata ba.

  Sai suka ce min sosai kuwa, kinga yadda ya ke mutuwar sonta. Fatima kinji masifar dana fada cikinta." Fadila ta kai karshen maganar cikin shashshekar kuka.

  Ga mamakin Fadila sai ta ji muryar Fatima wadda tasani da taushin murya gami da sanyi ta canza zuwa mai kauri.

  "Ke Fadila karki fara kiyi min kuka saboda da namiji!" Fadila ta ware ido cikin mamaki ta na kallon Fatima sai kuma ta sake fashewa da kuka.

  "Fatima ki barni domin bani da zabi a duniya banda wannan kukan kila in samu saukin radadin da ke zuciyata….

  Ku latsa nan don karanta ci gaban labarin.

  Taku, Halima K/Mashi

Comments

1 comment