Rubutu

Blogs » Kiwon Lafiya » Alkalumar masana game da cutar sankarar mama (breast cancer)

Alkalumar masana game da cutar sankarar mama (breast cancer)

 • Sankara dai tana aukuwa ne a lokacin da ƙwayar halitta mai illa ta fara hayayyafa fiye da yadda ya kamata. Wannnan hayayyafar ƙwayar halittar ya kan kai ga matakin ciwo mai tsanani, kuma a wasu lokutan ya kan kai ga mutuwa.

  Sankara dai ta kan kama mata da maza a sassa daban-daban na jikinsu. Alkalluma daga Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) sun ce sankarar mama (breast cancer) ita ce sankarar da ta fi kama mata a duniya, inda mata miliyan daya da rabi ke kamuwa da cutar a ko wacce shekara.

  Har wa yau, alƙalumma sun nuna cewar, ita sankarar mamar ce ta fi kashe mata da yawa a duniya. Kuma a shekarar 2015 sankarar mamar ta yi sanadiyyar mutuwar mata 570,000 a duniya.

  A Najeriya, muna da karancin samun tabbacin yawan ko wacce cuta, ko mura ko malariya, balle ciwo mai tsanani kamar sankara. Amman an yi kiyasin cewar mutum sama da 250,000 ne ke kamuwa da cutar a ko wacce shekara a Najeriya.

  Hukumar Lafiya ta Birtaniya (NHS) ta ce da wahala a iya gane musabbabin kowanne irin ciwon sankara wato daji ko cancer a Turance, balle kuma a gangaro kan wanda ke kama mama, sai dai ta ce akwai wasu abubuwa da suke taimakawa wajen karuwar hadarin kamuwa da cutar.

  Kamar yadda hukumar ta NHS ta yi bayani, shekaru ko gado, ko in wani a iyaye ko kakanni ya taba samun ciwon daji kowanne iri ne. Ko kuma in macen ta taba gamuwa da wani nau'in ciwon dajin, ko ta sami wani ƙululu a mamanta. Haka zalika, mace mai girman mama, ko kuma ga macen da ke fara al'ada da wuri, amma kuma shekarun kare al'adar su ja sosai ita ta na da hadarin kamuwa da cutar. ko macen da take da nankarwa, ko mai matukar tsawo, ko wadda ke shan barasa, ko kuma in tururin wadansu na'urorin ya fiye shigar mace, duk na kara hadarin kamuwa da ciwon dajin mama.

  Cibiyar bincike akan ciwon sankara ko daji ta Birtaniya ta bayyana alamomi na farko na ciwon sankarar da ke kama mama da cewa shi ne ƙululu a cikin mama. Sai dai ta ce sau tari ƙululu tara cikin goma a mama baya kasancewa sankara.

  Cibiyar binciken ta kara da cewa akwai wasu alamomi da ba lallai ba ne su ma a ce ciwon sankarar mama ne, amma daga zarar mace ta ga sauyi a fasalin mamanta, ko kuma zubar jini daga maman, ko ciwon mama, ko kuma ƙululu ko kumburi a hammata to ta garzaya zuwa asibiti a kan kari domin a bincikawa.

  Binciken dai ya bayyana cewa a duk shekara akan gano masu dauke da cutar kimanin dubu arba'in da biyar. Kuma shine babban musabbabin mutuwar mata 'yan tsakanin shekaru 34 zuwa 54 a kasar, wadda ita ce ke da mafi yawan wadanda ke mutuwa a saboda cutar a duk duniya kamar yadda binciken ya bayyana.

  A shekara ta 2008, Hukumar lafiya ta Duniya ta yi ƙiyasin cewar akwai mutane miliyan 12.4 da suka kamu da cutar. A yayin da kuma mutane miliyan 7.6 ne suka rasu a sakamakon kamuwa da cutar, wasu miliyan 25 kuma ke fama da cutar na tsawon shekaru biyar. kafin nan da shekara ta 2030 kuwa, kamar yadda hukumar lafiya ta duniya WHO ta yi bayani kimanin mutane miliyan 17 ne za su rasu sakamakon kamuwa da cutar ta cancer, a yayinda wasu miliyan 26 kuma za su kasance masu ɗauke da cutar.

  Rahotannin sun tabbatar da ci gaba da yawaitar masu kamuwa da wannan cuta a ƙasashe masu tasowa wa'yanda yanzu haka suke da masu ɗauke da cutar har kashi 60 cikin 100, lamarin da aka danganta da ƙaruwa ko ci gaba da runguman hanyoyin rayuwa na yanmacin Turai, yankin da ada itace tafi sauran sassan duniya yawan masu ɗauke da masu wannan cuta.

  Sai dai kuma masana harkar lafiya sun bayyana cewar kowane yanki ko nahiyar duniya akwai cutar ta cancer da tafi ƙamari a tsakanin al'uman wannan yanki. Misali ita ce yadda cutar cancer ta mafitsara ta yi ƙamari tsakanin maza a ƙasashe masu tasowa, inda ake samun mutane uku cikin 500 da ke ɗauke da ita. A yayin da cancer ta mama ko mahaifa ta fi ƙamari tsakanin kuma mata. Wannan lamari ne ma yasa Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ta ware rana ta musanman domin faɗakar wa game da illar wannan cuta.

  Masana kimiyyar lafiya sun tabbatar da cewar akwai cutukan sankara ko cancer kimanin 100 da ke addabar jama'a a duniya. kuma kowane ɗaya daga cikin wa'yan nan cutukan na cancer na da na shi alamomi, a yayinda wasu kuma suke kama da wasu. Kaɗan daga cikin alamomin cutar ta cancer dai sun haɗa da yawan nuna laulayi da rama da kuma zazzaɓi ko rage zuwa ban ɗaki kamar yadda mutum ya saba. Sauran alamun cutar ta cancer kamar yadda masana suka yi bayani sun haɗa yawan Tari babu ƙauƙautawa da kuma fitar da jini ko majina a lokacin wannan tari. Wannan alamu dai anfi dangantashi da sankara ta huhu.

  Wasu daga cikin cutukan na cancer da ake da su dai sun haɗa data mama da mahaifa waɗanda suka fi ƙamari a tsakanin mata. Haka kuma akwai cancer ta huhu da tafi ƙamarai tsakanin masu shan taba sigari, haka kuma akwai sankara ta fatar jiki da ta ciki. Bayan wannan kuma akwai sankara ta jini wato Leukemia da kuma ta ƙashi. Bayan waɗannan kuma akwai sankaran dubura bayan nan kuma akwai Sankaran ƙwaƙwalwa. To amma dai dukkannin waɗannan cutuka na sankara masana harkokin lafiya na ganin ana iya magance kashi 1/3 ko kuma rage lahanin da za su iya yiwa ɗan adam muddin aka gano su akan lokaci. Sannan kuma aka yi anfani da magungunan da suka dace, duk kuwa da yanke ƙaunar da ake ɗorawa duk wanda ya kamu da ɗaya daga cikin wannan cuta ta Sankara.

  Ya ake kamuwa ta cutar sankaran mama?

  Cutar sankara tana da wahalar ganewa kuma ba a san takamaiman dalilin da ke sa a kamu da cutar ba. Wata kwararriyar likita da ta taba aiki a asibitin kasa na Najeriya da ke Abuja, wadda a yanzu haka ta bude nata asibitin, Dr Hajara Yusuf, ta ce har yanzu ba a gano takamaiman dalilin da ke janyo cutar ba.

  Amman ta ambato dalilai da ke taimakawa wajen kamuwa da cutar. Dalilan sun hada da yawan shekaru (a Najeriya macen da ta kai shekaru 50 na iya kamuwa da cutar), da shan barasa, da amfani da sinadarin Estrogen da kwayoyin halittar da ke dauke da bayanai na gado wadanda ke iya haifar da cutar.

  Likitar ta ce sankarar mama da ta mahaifa ne suka fi damun mata."Amman maruru ko kurji da ke iya fitowa kan mama ciwo ne na fata," kurji yana jikin fata ne, bai kai ga abin da ke cikin mama ba.

  DubiBayanai game da cutar kansar mafitsara

  Sai dai kuma ba mata kadai ne su ke kamuwa da cutar sankarar mama ba, maza ma suna kamuwa da cutar. Masana sun ce kashi daya cikin dari na masu sankarar mama maza ne. Akwai bukatar mata su dinga zuwa ana duba su a asibiti akai-akai

  Ƙululu na da wata barazana?

  Likitoci sun ce in har mace ta ji wani kululu ko wani kulli cikin nononta, ya kamata ta garzaya zuwa asibiti domin a yi maganin matsalar tun tana karama.

  Sai dai kuma ba ko wanne kululu ne sankara ba. Sai an cire kululun an gwada kafin a gane cewar sankarar mama ne ko kuma ba shi ba.

  Har wa yau likitoci na son macen da ta lura cewar wani nononta ya fi wani girma ta je asibiti a duba ta domin a iya dakile cutar dajin da wurwuri idan cutar ne.

  Kazalika in mace ta lura cewar kan nononta ya koma ciki ta yadda jariri ba zai iya kama kan nonon ba, ana son ta je a duba domin yana daga cikin alamomin sankarar nono.

  Baya ga haka idan macen da ba ta shayarwa ta ga ruwan na fitowa daga nononta a hade da jini, ita ma ana son ta garzaya asibiti domin a duba.

  Sai dai kuma ba ko wacce mace da ke da daya daga cikin wadannan alamun ne ke da ciwon ba, duk da cewa alamu ne da ke nuna cewa mace za ta iya kasancewa da sankarar mama.

  Karanta wannan makala game da cutar kansar kwakwalwa (brain tumor)

  Ta yaya za a guje wa sankarar mama?

  Masana sun ce za a iya guje wa sankarar mama ne ta hanyar guje wa abubuwan da ke taimaka wa sankarar mama irin su barasa da sinadarin Estrogen da sauransu.

  Da farko yana da kyau mutum ya ci abinci mai kyau. Abinci, ba wanda ake saya a kanti ko ake sarrafawa a zuba a robobi ko gwangwanaye ba, abinci wanda muke nomawa, wanda za a ci.

  Ba wanda ya yi shekara daya a cikin firiza ko kuma firji ba, ko kuma an dauko shi cikin gwangwani daga can kasashen waje, ya dade a tashar jirgin ruwa, sannan kuma a zo da su Najeriya,

  Wace illa sankarar mama ke yi wa yaro? 

  Masana sun ce sankarar mama ba ta yi wa jaririn da ake shayarwa illa domin shi sankarar ba ta yaduwa da jini ko nono. Saboda haka ana ganin mace mai wannan larurar za ta iya shayarwa ba tare da wani fargaba ba.

  Ta yaya ake maganin sankarar mama?

  Ana maganin sankarar mama ne a manyan asibitoci inda ake da kayayyakin aikin da kwararru kan maganin sankara. Ban da maganin sha, ana maganin sanakarar mama ta hanyar cire sankarar mama ya kama da kuma gasa wurin da ya kamu da ciwon ta yadda sankarar za ta mutu.

  Mai karatu na iya duba wannan makala da ita ma tai bayani gamsashshe game da wannan matsala ta cutar kansar mama.

  Rubutawa: Maryam Haruna, a registered midwife, Zamfara, Nigeria

Comments

0 comments