Rubutu

Blogs » Tarihin Mutane » Gwagwarmayar Kiki Mordi, yar jarida mai binciken sex for grades

Gwagwarmayar Kiki Mordi, yar jarida mai binciken sex for grades

 • Wata matashiya, haziƙa, ‘yar gwagwarmaya, jajirtacciya wacce yanayin rayuwa ya mayar da ita jaruma, wacce kuma ta samu ɗimbin nasarori da ƙalubale tun a shekarun ƙuruciya – wannan ita ce Nkiru Mordi wacce ake ambato da Kiki Mordi.

  An haifi Nkiru Mordi a ranar 12 ga watan Agusta, 1991 a garin Port Harcourt ta jihar Rivers a tarayyar Nigeria. Ta yi Primary da Secondary ɗinta duk a jihar ta Rivers. Tana tsaka da fafutukar neman gurbin karatu a Jami’ar Nsuka da ke jihar Enugu, kwatsam sai babanta ya rasu, wanda hakan ya zama koma-baya ga burin rayuwarta na karantar ilimin likitanci, wato medicine.

  Bayan wani ɗan lokaci, sai ta sake neman gurbin karatu a jami’ar Benin, kuma ta yi sa’a ta samu. Bata daɗe da fara karatu a makarantar ba sai ta bari, bisa dalilin da ta bayyana na ƙoƙarin keta mata haddi da wani malaminsu ya yi. Daga wannan lokacin Kiki ta fidda rai da cikar burinta, ta haƙura da karatu. Ta fara shawagi a kafafen sada zumunta na zamani in da ta soma rubuce-rubuce na bayyana ra’ayi, da abinda ke damunta, tare da bayyana nagarta da kuma darajar da mata ke da ita.

  Yawan rubuce-rubucen da take yi da kuma binciken ƙwaƙwaf, ya sanya mata sha’awar aikin jarida, daga lokacin ta zama ‘yar jarida mai zaman kanta.

  Ta fara aiki a matsayin mai gabatarwa a wani gidan radio mai taken Muryar Mata, wato WFM, da ke jihar Ogun, wanda ake kama shi a kan mita 91.7. A yanzu haka ma ita ce shugabar sashen yaɗa labarai ta gidan, sannan tana ɗaya daga cikin masu aikawa BBC rahoto a wani shiri nasu mai suna BBC Africa Eye.

  Wasu daga cikin ayyuka da nasarorin da ta samu

  A shekara ta 2015 aka zabeta a matsayin matashiya mai gabatarwar da dukkan alamomi suka nuna cewa gobenta zata yi kyau. Hakan ya faru ne a wani bikin bayar da kyaituttuka na Nigeria Broadcasters Merit Awards, bayan da aka duba wasu rubuce-rubucenta na kafafen sada zumunta da suka yi matuƙar tasiri.

  Bayan aiki da tashar WFM da take yi, Kiki tana binciken bin ƙwaƙƙwafi musamman a kan wani abu na rashin gaskiya da ake son ɓoyewa.

  A cewarta, “’Yansanda sun zo gidanmu bincike, bayan sun gama binciken ba tare da sun samu kowace irin shaida a kan abinda suke zarginmu da shi na cewa mu ‘yan ƙungiyar asiri ne ba, sai suka tafi da mu ofishinsu, sai kuma suka nemi da mu ba su naira dubu ɗari biyu wai don a kashe maganar.”

  Wannan na daga cikin dalilan da suka sanya Kiki soma yin rubuce-rubuce masu jan hankali a kafafen sadarwa, musamman na yin kira ko suka ga hukumomi.

  Rubutu mafi jan hankali da ta yi shi ne mai taken ‘End Police Extortion Now!’

  Bayan shi, ta yi rubuce-rubuce da dama a shafinta na Twetter, kamar irin su:

  “Idan har baka samu ji na a daren yau ba, to ka tambayi state CID Zone 5 ina nake? Ka tafi kai tsaye kawai, ina da wani babban labarin cin hancin da zan bayar”

  Da dai sauran rubuce-rubuce masu jan hankali.

  A shekarar 2016 ta samu nasarar lashe kyautar ƙwararriyar mai gabatar da shirye-shiryen gidajen radio, a kudu maso kudancin Nigeria. Sannan a shekarar dai ta shiga sahun mutanen (mata) da murayarsu ke Amo a kudancin ƙasar.

  Haka ma a shekarar 2019, tana cikin mutanen da aka karrama a The Future Awads Africa, bangaren ‘yan jaridu.

  Kiki tare da wasu mata guda hudu a duniya da suka samu karramawar MTV EMA game da gwagwarmayarsu ta samawa mata yanci a duniya.

  A shekarar ta 2019 ta shirya wani documentary film, mai suna ‘Life at the Bay,’ a garin Legas, wanda director Nora Awolawo ya bayar da umarni.  Film ne da ke bayyana yadda rayuwa take a garin Tarkwa Bay, da kuma yadda matan garin ke faɗi-tashi wajen gudanar da rayuwarsu. A shekarar an zabi film ɗin a cikin finafinan da aka nuna a bikin nuna finafinan ƙasashen Africa, wato Africa International Film Festival.

  Har ila yau, Kiki na cikin mutane biyar da suka samu karramawa ta ‘One Young World Journalist of the Year Award 2020.’

  Kiki tare da yan'uwanta da suka samu karramawar One Young World Journalist of the Year 2020

  Binciken Sex for Grades

  A cikin shekarar ta 2019 ɗin dai, a ranar 7 ga watan October, Mordi da taimakon ‘yan tawagarta masu aiki da BBC a shirinsu na Africa Eye,  suka gudanar da wani binciken sirri a kan yadda malaman jami’a ke lalata ɗalibansu, wanda daga ƙarshen binciken ta saki wani documentary film mai suna  Sex for Grade. Ta fara sakin wani yanki na film ɗin na tsawon minti goma sha-uku, wanda a ciki aka hango fuskokin wasu malamai biyu, ɗaya a Nigeria ɗaya a Ghana, suna ƙoƙarin yin lalata da ɗalibansu, a makarantunsu wato University of Lagos, da kuma University of Ghana.

  Kwanaki kaɗan bayan bayyanar wannan faifan bidiyon, wanda Nkiru ta yi basaja a matsayin ɗaliba mai neman gurbin karatu, jam’ar jihar Lagos ta dakatar da Dr. Boniface Igbeneghu daga aiki har na tsawon watanni shida, ba tare da aiki da kuma albashi ba. Haka irin wannan hukuncin ya tabbata a kan Ransford Gyambo na University of Ghana.

  Haka zalika wannan faifan bidiyon ya jawo hankulan mutane da dama, ciki har da tsohon mataimakin shugaban ƙasar Nigeria Atiku Abubakar, da kuma tsohon shugaban majalisar dokokin ƙasar, wato Bukola Saraki, wadanda suka yi kira ga gwamnati da ta ɗauki matakin gaggawa a kan masu aikata irin wannan mummunan halin na neman ɗalibai a manyan makarantun ƙasar.

  A wata hira da aka yi da ita a jaridar Sahara report, Mordi ta bayyana cewa bayan bayyanar faifan bidiyon, ta samu saƙwannin barazana da matsin-lamba masu tarin yawa.

  A ranar 8-10-2019 Mordi da abokan aikinta masu gabatar da shirin Africa Eye a tashar BBC suka saki cikakken bidiyon baɗalar da malaman jami’a ke yi da ɗalibai, wanda hakan ya kara tona asirin wasu da dama, aka kuma dakatar da wasunsu daga aiki. Kwana ɗaya bayan fitar bidiyon majalissar dokokin ta tarayyar Nigeria ta yi zama tare da yanke zaman gidan yari har na tsawon shekaru sha-huɗu, ga duk mutumin da aka kama da laifin aikata fyaɗe, a matsayin doka.

  A cikin jerin nasarori da wannan bincike ya samu har da kasancewa zababbe a jerin karramawa ta ‘Emmy Awards na 2020.

  Mordi ta samu nasarori, kyaututtuka da lambobin yabo a dukkan ɓangarori da matakan da take taka rawa a rayuwarta. Tun daga shekara ta 2015, har zuwa shekara ta 2020, Nkiru bata yi fashin samun kyautar girmamawa ba.

  Karanta tarihin gwagwarmayar mawaki Fela Ransome Kuti.

  Rubutawa: Zaharadden Nasir, daga Kano, Nigeria

Comments

0 comments