Rubutu

Blogs » Kagaggun Labarai » Illar Furuci 7 Na Halima Abdullahi K/Mashi

Illar Furuci 7 Na Halima Abdullahi K/Mashi

 • Ku latsa nan don karanta shafi na 14.

  Shafi Na 15

  Fatima ta sauke ajiyar zuciya sannan ta dubi Fadila "Dan girman Allah ki min shiru muyi magana, wallahi dan ke ce amma bana tattauna maganar jinsin namiji in har shi din ba ahalina ba ne."

  Fadila ta numfasa cikin dashashshiyar murya ta ce "Fadamin wata shawara da za ta sa zuciya ta tayi sanyi."

  Fatima ta ce "Tambayarki zanyi ko ya taba cewa ya na sonki?" Fadila ta girgiza kai tare da fadin "A a, sai dai ina kallon bani da wata makusa don haka kowane namiji zai iya cewa ya na so na."

  Fatima ta ce. "Kin tafka kuskure sosai! Amma ga shawara me zai hana ki share batunsa ki saka karatun ki a gaba, duk shekarunmu nawa nema kam da zaki damu da namiji, ni a halin yanzu maza ko birge ni basayi matsawar ba 'yan 'uwana bane ko a yan uwanma bana son wanda zai nemi wuce guri, ke kanki kin sani ko fara a malami ya cika yimin yanzu zan dauki matakin daina gaida shi... Ta numfasa sannan ta ci gaba da fadin.

  "Fadila ki yi tunani sosai kar ki kai kanki ga halaka kan wanda bai san kina yi ba, ki shafe babinsa ki kalli gobenki ki yi kokari ki zama cikin matan da al ummar ki da zauri'arku za suyi alfahari da ke."

  Cikin kuka Fadila ta kwantar da kanta a cinyar Fatima ta damki gefen hijabin Fatima cikin wani irin kunci wanda ba za ta iya fassara shi ba, ta ce Bazaki taba fahimtar halin da nake ciki ba, tare da soyayyar Ya Hashim na girma da shi na soma mafarki ranar da balaga ta fara riskata, sonsa a jinin jiki na yake!"

  Fadila ta fara shafa mata kai cikin tausayawa.

  Fadila ta ci gaba da fadin ki taya ni da addu a Allah ya ya ye min ko kuma ya saukaka min ya zo ya so ni nima."

  Fatima cikin siririyar murya ta ce "To ya isa tashi ga wata shawara." Zaraf Fadila ta tashi zaune ta na kallon Fatima.

  "Kin manta jiya bayan mun idar da salla malam ya yi mana nasiha har yake cewa dukan wanda ke da wata matsala mai sarkakiya acikin mu ya yi sallar istihara sannan ya barwa Allah zabi kintuna?"

  Fadila ta mike da sauri cikin rawar jiki tana fadin na tuna bari kawai inyi tun yanzu, domin in ban manta ba bai fada mana cewa ga lokacin yi ba, ko da wane lokaci za a iyayinta. Zan bawa Allah zabi dan shine mai karfin ikon sarrafa zukatan bayinsa."

  Fatima ta ce "Haka ne." Tabi Fadila da kallo wadda ta nufi daura alwala duk namiji ya susuta ta, abinda ta ke ganin ba zai yiwu gare ta ba, domin namiji in ba dan uwanta bane kallo ma bai isheta ba.

  Ciki kwanakin da su ka biyo baya Fatima ta tsaya sosai dan ganin ta ceto Fadila daga cikin wannan hali ta hanyar ba ta shawarwari da nace mata sai ta rike haddarta hakan ya taimaketa matuka amma fa game da son Ya Hashim za ta ce sai abinda ya karu. Domin dan ma makarantar basa barin kwakwalwar dalibi ta huta sam.

  Tun karfe hudu su ke tashi suyi wanka su gyara shinfidunsu lokacin salla yanayi zasu nufi masallaci daga can su wuce karatun Kur’ani masu hadda kuma su shiga. Bakwai za su shiga karin kumallo da sun fito sai aji haka daki daki har yamma.

  Haka dai Fatima ta yi ta fama da Fadila har tsawon sati biyu. Abin ya kan lafa kuma ya na tashi kamar mai aljanu.

  Fatima Muhammad tana jin dadin rayuwar makarantarta sosai, sannan ta na godiya ga iyayanta da suka tsaya mata dan ta samu ilmi wanda zai amfane ta duniya da lahira. Burinta shine ta zama kwararriyar likita ko kwararriya a kan magungunan sai dai tabarwa Allah zabi.

  Abuja

  Tanti Dije ta na kwance akan kujera a falo tana kalon tashar sunna TV sama sama taji kwankwasa kofa dan haka ta kalli hanyar kicin ta kwalawa Jummai kira, ta fito daga kicin tana cewa "Gani Tanti."

  Ta ce. " ki duba kofa na ji kamar ana kwamkwasawa." Jummai ta bude Hajiya Asiya ta shigo da sallama. Tanti ta amsa tare da mikewa zaune ta dora da fadin "Antyna ta kaina kece haka da rana face fece."

  Hajiya Asiya ta nemin guri ta zauna tare da yaye mayafinta ta na fadin "Bari ke dai zuwan na danki ne shi ya taso ni."

  "Allah ya sa lafiya!" Inji Tanti ta fada ta na kallon Hajiya Asiya zuciyarta tana fada mata kan batun Fatima ne Ashir ya taso mahaifiyar sa.

  Jummai ta dire tire kato dauke da ruwa da leman roba gefe kuma ga kayan marmari dangin Ayaba da abarba.

  Suka sake gaisawa take kuma Hajiya Asiya ta shiga zayyanawa Tanti sakon Ashir. "Yaro ya hana mu sakat ko wane lokaci magiya yanzu yau tun safe ya ke shige da fice shifa sai nazo muyi magana kwakkwara ki masa alkawarin bashi Fatima."

  Tanti ta yi shiru tana sauraron wannan mawuyaciyar maganar kuma tana nazari.

  Hajiya Asiya ta tsiyayi lemo a kofi ta daga ta shanye ta dire kofin sannan ta dubi Tanti.

  "Hadiza Ashir dai danki ne na tashin alkiyama domin dan zumucin ki ne kuma cikin Ummanki ke da ubansa ku biyu ne iyayanku suka haifa baki da bukatar sai kin yi wani bincike akansa ko halinsa."

  Haba Hajiya Asiya ya ki ke irin wannan magana haka in har Ashir ya na da wata uwa ai abayana take, domin babansa ma yanzu ubane a gurina tun da iyayan namu sun mutu sun barmu, batun in bincike ko na san halin Ashir wannan ma ai batsa kike yi.

  Nazari nake yi akan ita kanta Fatima halinta da dabi arta, Ashir ya san komai na yi masa bayani duka na ce ya hakura zuwa ta gama sakandire muga ko zata canza.

  Hajiya Asiya ta ce "Mecece matsalar ta ne?"

  Tanti ta ce "Bata son soyayya batayi bata son namiji ya kulata matsawar shi din ba, ahalinta ba ne."

  "To menene dalilinta?" Hajiya Asiya ta tambaya cikin mamaki.

  Tanti ta ce "Oho ni dai na barshi a kiruciya ne kawai duk da ina girmama ra ayin yaro tun yana karami."

  Hajiya Asiya ta ce "Wannan ai duk laifinki ne, ke ce zaki fada mata cewa jinsin maza da mata dan juna akayi su...

  Zan dakata anan sai mun hadu a ci gaban labarin.

  Taku, Halima Abdullahi K/Mashi

Comments

0 comments