Rubutu

Blogs » Kiwon Lafiya » Yadda za ku kare kanku daga cutar sankara, wato cancer

Yadda za ku kare kanku daga cutar sankara, wato cancer

 • Cutar sankara, ko cancer a Turance, cuta ce dake haifar da wani tsiro a jikin bil'adama wanda ke shafan ƙwayoyin halitan bil'adama wanda kuma ke kaiwa ga nakasar wani ko dukkan ɓangaren na jikin bil'adama. Kuma sauda yawa ma dai hakan kan kai ga rasa rayukan masu ɗauke da wannan cuta.

  A shekara ta 2008, Hukumar Lafiya ta Duniya, wato World Health Organization (WHO), ta yi ƙiyasin cewar akwai mutane miliyan 12.4 da suka kamu da cutar cancer. A yayin da kuma mutane miliyan 7.6 ne suka rasu a sakamakon kamuwa da cutar. Wasu miliyan 25 kuma ke fama da cutar na tsawon shekaru biyar. Ana sa ran kafin nan da shekara ta 2030 kuwa, kamar yadda hukumar ta WHO ta yi bayani, kimanin mutane miliyan 17 ne zasu rasu sakamakon kamuwa da cutar ta cancer, ayayinda wasu miliyan 26 kuma zasu kasance masu ɗauke da ita.

  Rahotannin sun tabbatar da cigaba da yawaitar masu kamuwa da wannan cuta a ƙasashe masu tasowa wa'yanda yanzu haka suke da masu ɗauke da cutar har kashi 60 cikin 100, lamarin da aka danganta da ƙaruwa ko cigaba da rungumar hanyoyin rayuwa na yanmacin Turai, yankin da ada itace tafi sauran sassan duniya yawan masu ɗauke da masu wannan cuta.

  Sai dai kuma masana harkar lafiya sun bayyana cewar kowane yanki ko nahiyar duniya akwai cutar ta cancer da tafi ƙamari a tsakanin al'uman wannan yanki. Misali itace yadda cutar cancer ta mafitsara ta yi ƙamari tsakanin maza a ƙasashe masu tasowa, inda ake samun mutane uku cikin 500 dake ɗauke da ita. Sai kuma cancer ta mama ko mahaifa wacce tafi ƙamari tsakanin mata. Wannan lamari ne ma yasa hukumar ta WHO ta ware rana ta musanman, wato World Cancer Day, domin faɗakarwa game da illar wannan cuta. Wannan rana kuwa ita ce 4 ga watan Feburairu na kowane shekara.

  Masana kimiyan lafiya sun tabbatar da cewar akwai cutukan sankara ko cancer kimanin kala 100 dake addabar jama'a a duniya. kuma kowane ɗaya daga cikin wadannan cutukan na cancer na da nashi alamomi, a yayinda wasu kuma suke kama da wasu.

  Kaɗan daga cikin alamomin cutar ta cancer dai sun haɗa da yawan nuna laulayi da rama da kuma zazzaɓi ko rage zuwa ban ɗaki kamar yadda mutum ya saba. Sauran alamomin kuwa, kamar yadda masana suka yi bayani, sun haɗa da yawan tari babu ƙauƙautawa da kuma fitar da jini ko majina a lokacin wannan tari. Wannan alamu dai an fi dangantashi da sankara ta huhu.

  Wasu daga cikin cutukan na cancer haɗa da ta mama da mahaifa waɗanda suka fi ƙamari a tsakanin mata. Haka kuma akwai cancer ta huhu da ta fi ƙamarai tsakanin masu shan taba sigari. Sai kuma akwai sankara ta fatar jiki data ciki. Bayan wannan kuma akwai sankara ta jini wato leukemia da kuma ta ƙashi. Bayan waɗannan kuma akwai sankarar dubura da ta ƙwaƙwalwa.

  To amma dai dukkannin waɗannan cutuka na sankara masana harkokin lafiya na ganin ana iya magance kashi 1/3 ko kuma rage lahanin da zasu iya yiwa ɗan adam muddin aka gano su akan lokaci, kuma aka yi amfani da magungunan da suka dace, duk kuwa da yanke ƙaunar da ake ɗorawa duk wanda ya kamu da ɗaya daga cikin wannan cuta ta Sanka

  Mai karatu na iya duba bayani game da cutar hepatitis.

  Matsayin da cutar sankara ta taka

  Idan kana dauke da cutar sankara likita zai so sanin matakin da takai daga inda ta fara; ana kiran sa "cancer stage" a Turance. Za ka ji mutane suna cewa cancer dinsu tana stage 1 ko stage 2. Sannan matsayin cancer dinka shi zai taimaka wajen sanin maganin da za a doraka akai.

  Kowace irin cancer akwai gwajin da ake yi domin gane matasayin da ta kai. A dokar gwajin mataki na cancer mataki na 1 da mataki na 2 yana nufin cancer bata yi karfi sosai ba. Mataki na 3 da mataki na 4 kuma ta yadu sosai. Mataki na 4 shine makura wajen yaɗuwar ta.

  Alamomin cutar Kansa

  1. ƙarancin numfashi
  2. Tari da ciwon kirji wacce alama ce ta cancer hunhu ko na bargo. Ciwon kirjin yakan kasance daga kirjin zuwa kafada sannan ya sauko zuwa hannu
  3. Zazzabi da saurin kamuwa da ciwo. Wannan ana kiranta leukemia a Turance hakan yana faruwa ne dalilin asalin kwayar halittar jinin mutum ta tabu.
  4. Fama wajen hadiye abu. Wannan yana nuni da an kamu da sankarar makoshi ko kuma esophageal cancer a Turance.
  5. Fitowar kurji mai ruwa a wuya, hammata da gwiwa.
  6. Yawan zubda jini.
  7. Kasala da yawan gajiya
  8. Kumburin ciki
  9. Rashin sha'awar abu da kuma daukewar dandano
  10. Ciwon ciki da mara
  11. Fitar jini daga dubura
  12. Rama ta lokaci guda
  13. Yawan ciwon ciki
  14. Nono yayi ja ya kumbura alamace ta breast cancer
  15. Canjawar kan nono
  16. Nauyi da kuma ciwo na fitar hankali a lokacin al'ada wannan alama ce ta uterus cancer. Ana bukatar yin hoto (transvaginal)
  17. Kumburin fuska
  18. Canjawar farce zai iya kasancewa lung cancer idan kuma ya kode yayi fari to alam ce ta liver cancer
  19. Ciwon baya a bangaren dama yana nuni da liver cancer ko breast cancer
  20. Fesowar kuraje a jikin mutum

  Kuna iya duba wata makala da ta yi bincike akan cutar sikila, wato sickle cell anemia.

  Ga karin bayani akan sankarar bakin mahaifa

  Ita dai sankarar bakin mahaifa na samuwa ne a daidai bakin mahaifar mace, wato mashigar mahaifarta.

  Wannan cuta ta fi shafar matan da ke jima'i musamman wadanda ke tsakanin shekarun 30 zuwa 45. Yawanci maza ne ke dauke da ƙwayar cutar a jikinsu wadda kan janyo masu wasu irin ƙuraje a baki. Idan namiji mai dauke da wannan ƙwayar cuta ya sadu da mace lafiyayya tana iya ɗaukar wannan cuta har ta zamar mata kansa a bakin mahaifarta.

  Hukumar Lafiya ta Duniya, WHO, ta ce ita ce kansa ta huɗu mafi shahara a mata.

  A shekarar 2018, an yi kiyasin cewa mata 570,000 suka kamu da ita a faɗin duniya, kuma a cikin matan guda 311,000 ne suka mutu sanadiyyar cutar.

  Amma shekaru goma sha biyar da suka gabata, an gano riga-kafin wannan cuta wadda ke iya bai wa mata kariya daga kamuwa

  Alamomin sankarar mahaifa

  Alamun kamuwa da cutar sankarar bakin mahaifa ba su cika bayyana ba, kuma ba sa haddasa wata matsala har sai ta kai makura. Akwai alamu kamar fitar jini lokaci ko bayan saduwa, ko kuma a tsakanin jinin al'ada ko kuma wani sabon fitar jini bayan mace ta wuce lokacin yin jinin al'adar.

  Duk da cewa fitar jinin da ba na al'ada ko na haihuwa ba, ba yana nufin cutar sankarar bakin mahaifa ba ne, amma yana da muhimmanci mace ta je ta ga likita.

  Me ke janyo sankarar bakin mahaifa?

  Ƙwayar cuta ta HPV ita ta fi haifar da wannan cuta. HPV wata ƙwayar cuta ce da ake iya saurin yaɗawa ta hanyar saduwa tsakanin mace da namiji.

  Ana iya magance wannan kansa idan aka gano ta da wuri. Shi ya sa ake so mata su riƙa zuwa asibiti ana tantance su akai-akai. Tantancewa na bayar da damar gano cutar da wuri kuma a hana ta yaduwa. Amma idan har cutar ta yi yawa a bakin mahaifar ana iya yin tiyata a yanke mahaifar gaba ɗaya sannan a yi gashin radiotherapy don ƙone ƙwayoyin cutar.

  Matakan kariya daga cutar

  Hanyoyin da suka kamata a bi wajen daukar matakan kariya daga cutar sankarar bakin mahaifa su ne zuwa ganin likita akai-akai don bincika bakin mahaifar, binciken da aka fi sani da "smear test". Lokacin yin wannan bincike za a dauki wani samfuri na kwayoyin da ke jikin bakin mahaifar sannan a auna su da madubin likitoci da ke gano cuta.

  Mace za ta iya rage kaifin yiwuwar kamuwa da cutar sankarar bakin mahaifa ta hanyar daina shan taba sigari, saboda a cewar masana, mutanen da ke shan taba sigari na da wahalar samun kariya daga kamuwa da kwayar cutar HPV da ka iya haddasa sankarar bakin mahaifa.

  Akwai kuma riga-kafin kamuwa da kwayar cutar ta HPV da ake kira Gardasil, da ke bayar da kariya daga nau'ukan kwayar cutar HPV hudu da akasari ke haddasa kansar.

  Riga-kafin cutar sankarar bakin mahaifa

  Ƙwararru sun gano riga-kafin cutar sankarar bakin mahaifa wadda ke bai wa mata kariya daga kamuwa da wannan cuta. Haka kuma, ana iya yi wa maza wannan allurar don hana ƙwayar cutar yin tasiri a jikinsu sannan ta hana su yaɗawa ga matansu.

  An fi so a yi wa yarinya mace da ba ta haura shekara 9 ba wannan allura, wannan na nufin a lokacin ba ta riga ta fara saduwa da namiji ba.

  Ga matan da suka fara saduwa, likitoci na ba da shawarar su riƙa zuwa asibiti ana tantance su duk bayan shekara uku don tabbatar da cewa ba sa dauke da cutar.

  Duba cikakken bayani akan cutar ciwon sanyin mata, wato vaginal infection.

  Rubutawa: Maryam Haruna, a registered midwife, daga Zamfara, Nigeria

Comments

0 comments