Rubutu

Blogs » Muhawarar Bakandamiya 2020 » Wa yake cin riba a hauhawar farashi, ‘yan kasuwa ko gwamnati?

Wa yake cin riba a hauhawar farashi, ‘yan kasuwa ko gwamnati?

 • A ci gaba da kawo muku karon battar fasahar da marubuta ke yi a muhawarar da Bakandamiya ta shirya ta kuma ɗauki nauyin aiwatarwa, a yau za ku ga yadda Hazaƙa Writers Association da Yobe Authors Forum suka ɓarje guminsu tare da ruwan hujjoji a maudu’I mai taken Wa yake cin riba a hauhawar farashi, ‘yan kasuwa ko gwamnati? An tafka muhawarar ne a ranar 28 ga watan Nuwamba, 2020 a katafariyar manhajar sada zumunta ta Bakandamiya.

  A kafta!

  WAI BAN DA NEMAN ZANCE TA YAYA ZA A HAƊA GWANDA DA GUNA?

  IDAN ANA BABBAKAR GIWA WA ZAI JI ƘAURIN ZOMO?

  Idan ana maganar moruwar ‘yan kasuwa da hauhawar farashi wa yake lissafin gwamnati? Ko daga sunan ya kamata a tantance. ƊAN KASUWA (kasuwar uwa ce fa kacokan gare shi! Kowa ya san kuwa uwa ga ɗanta ai ba za ta tsaya goya bare ba. Ita gwamnati ai sai dai mulki).

  Kafin kawo hujjojina gudun kada mu yi daki-da-ka, ya kamata mu fahimci hauhawar farashi. Malaman ƙididdiga da tsumi-da-tanadi sun bayyana ma’anarsa da, “Tashin farashin kayayyaki saboda ƙaruwar buƙatarsu, da kuma yaɗuwar kuɗaɗe a hannun mutane.”

  Da wannan nake kiran abokan muhawarata, DUK WANDA BAI SAN GARI BA YA SAURARI DAKA. Ko kun san cewa hauhawar farashin ma kamar sitiyarin mota haka yake hannun ‘yan kasuwa, su suke sarrafawa yadda suke so? Kamar yadda za a ƙara hasken fitila ko a rage, haka ‘yan kasuwa suke yiwa farashi, ya danganta da irin ribar da suke son ci. BA NA ƘWAINA SAI DA ZAKARA. Biyo matakalar hujjojina ku fahimta.

  ƊAYA MAFARIN-ƘIRGA

  Tsarin gwamnati na ƙayyade farashi ba ya aiki a Najeriya, wanna ya ba wa ‘yan kasuwar jari hujja damar cin karensu babu babbaka. A karkarata watanni biyu da suka wuce, kafin bijirowar wani bijimin ɗan kasuwa buhun albasa ba ya wuce dubu goma. Amma yana zuwa ya ce duk buhun albasa zai saya a dubu sha-takwas, jin maƙudan kuɗaɗen ya sa mutane suke ta fito da albasarsu yana sayewa, har gona za a bi ka a ƙwaƙwale ta a ba ka kuɗinta. Kafin cikar mako huɗu sai da aka nemi albasa ta sayarwa gabaɗaya aka rasa, duk an sayar wa mutum ɗaya ya ɓoye. Rashinta a gari ya sa mutane suna neman ta RUWA A JALLO! Kuma har a yau da nake rubutun nan buhunta ya haura dubu hamsin. Shin wacce irin riba ce wannan ɗan kasuwar ba zai samu ba?

  Na san abokan muhawara za su yi maganar haraji, to harajin kwata-kwata nawa yake? Kashi biyar (5%) ne ko bakwai da rabi (7.5%) cikin ɗari na kuɗin kayan. Sauran kashi casa’in da biyar (95%) ko casa’in da biyu da rabi (92.75%) duk yana hannun ɗan kasuwa. A hakan ta yaya gwamnati za ta fi shi samun riba? Ai SAMA TA YI WA YARO NISA, sai dai ya bi ta da kallo aradu.

  BIYU IDANUN-DABBA

  Mu bar wancan batun, kasuwancin gabaɗaya ma gwamnati ba ta iya yi ta samu riba sai faɗuwa. Tambayata ita ce, me ya sa gwamnati ta sayar wa da ‘yan kasuwa NITEL? (Na layikan wayar salula). Me ya sa ta sayar da NEPA? Me ya sa ta haƙura da harkar safarar jirage? Me ya sa ita kanta matatar man fetur babbar kadarar da gwamnati ba ta da sama da ita take so ta sayar? Saboda ba ta iya kasuwancin ba faɗuwa take yi, kuma shi kenan gari banza ma ba ta iya samun riba ba sai da farashi ya hauhawa za ta fi haifaffen kasuwanci? ANA SANI AKA BAR JAKI FA AKE DUKAN TAIKI.

  UKU DUWATSUN-MURHU

  Zan sake tambayar abokan muhawara, shin me ya sa a hauhawar farashi gwamnati take sake lodo bashi? Hakan ya nuna cewa ashe hauhawar farashi nakasa ta yake yi ba wai samun ribar ƙanzon kurege da ake faɗa ba, ɗan kasuwa kuwa YADDA AKA DAMA HAKA ZAI BAYAR A SHA. Duk tsadar kaya a haka zai lissafa kuɗin da ya kashe ya fitar da ribarsa. Ashe kenan KO BA A GWADA BA LINMAFI YA FI ƘARFIN BAKIN KAZA. Da fatan hujjojina su samu karɓuwa.

  Na gode.

  Jibrin Adamu Rano, wakilin Hazaƙa Writers Association

   

  Gwamnati ta fi samun riba a hauhawar farashin kaya

  Masu girma jagororin muhawara, masu girma alkalai, abokanen fafatawar mu, masu bibiyarmu, Assalamu alaikum. Kamar yadda za mu kare batun mu kan cewa, ‘Gwamnati ta fi samun riba a yayin da aka sami hauhawar farashin kaya’. Mun ga zai fi kyautuwa mu fara da bayyana ma’anar riba. Kamusun Hausa ta Jami’ar Bayero, (2006:70) ya bayyana riba da cewa, “Karin kudi da dan kasuwa ke samu bayan ya sayar da kaya sama da farashin da ya sayo.”

  A ma’ana ta zahiri na wannan batu, za a ga kenan riba na takaituwa ga sai wanda ya sayo abu ya kuma kara wani kudi a kai, kuma ya sayar da abin ne zai same ta. Amma ga wanda bai da kaya; bare haja, babu yadda za a yi ya sami riba, domin shi bai ma kasa ba; balle ma ya sayar sannan tukucin riba ya biyo baya. Idan kuwa wannan batu haka yake, to mece ce ribar gwamnati a dukkanin wani hauhawar farashin kaya da za a samu? A nan ke nan, ya kyautu mu bayyana wace ce ‘Gwamnati’ Kamusun ta sake bayyana ta da cewa, “Hukumar kasa ko ta jiha’. Fassarar wannan ita ce, wasu mutane ne iko ya ba su damar tafiyar da al’amuran al’umma bisa yadda doka ta tsara.

  Gwamnati ce ke da alhakin kula da tafiyar da dukkanin al’amuran kasa ko na jiha dubi da matakin ta. Ita ke karbar haraji da tsara ko sabunta harkokin kasuwanci da kafa musu ka’idar da ita take ganin ya cancanta. Sannan dukkanin wani dan kasuwa, har ma da gina musu kasuwanni da bayar da tsaro a dukkanin wuraren kasuwanci.

  Game da ita ta fi cin riba a yayin hauhawar farashi, wannan haka yake ba ja ‘wai kare ya mutu a saura’. Domin ganin irin ribar da take kwasa ne ma ya sanya har ake mata kirari da cewa, ‘Gwamnati ba ta asara’. Ma’ana, ba ta faduwa a dukkanin abin da ta yi, ko kuma dai ba ta yarda ta yi abin da ta san zai zame mata faduwa ko asara.

  Hujja ta Farko I

  Idan aka sami hauhawar farashin kaya, Gwamnati na da kaso ta yadda duk wani abu da zai kai ya komo; to tana da ribar da za ta karba.

  Hujja ta Biyu II

  Idan kaya ya hau, Gwamnati na la’akari da wannan ta kara haraji ta yadda dole ne abin da take karba a wuraren kamfanoni ya kara yawa; tare da cewa ita fa babu abin da ta kasa, balle a zo a taya har ma a saya a ba ta riba.

  Hujja ta Uku III

  Idan farashi ya karu, Gwamnati na kara tsananta wa ‘yan kasuwa ta yadda take ganin su ma fa suna lillinka kudi ne, don haka ba za ta yi la’akari da kadan din da suke samu ba, sai ta yi musu kari koda kuwa karin zai kai su ga rasa riba ce.

  Hujja ta Hudu IV

  Ba makawa, ‘yan kasuwa su ne wadanda sikiyarin motar juya farashi ke hannunsu, amma da za ka leka zaurukansu domin lalubo gwalagwalan ribar da suke kwasa, za ka iske duk abin na tafiya a iska ne kurum, domin suna dauke da nauye-nauyen da ke kan kasuwanci; a daidai lokacin da ita kuma gwamnatin ba wani nauyin da yake kanta makamancin nasu a irin wannan bigire.

  Hujja ta Biyar V

  Duk wanda ka ji an ce Gwamnati ta ba shi bashi, to akwai wani kaso da take tatsa a wurinsa. Shin, ko kun san cewar wannan kason da take karba riba ce tsababa a wurin ta. Kar dai a manta har yanzu, ita fa ba ta kasa ba, balle ta shelanta hajarta, har wani ya yi kwadayin saya; kuma ya saya ya ba ta riba.

  Hujja ta Shida VI

  Ba mai musun cewa, man fetur shi ne babbar hajar Gwamnati, tare da haka ba za ka ji ta fadi a kasuwancinsa ba, duk da cewa akan alakanta hauhawar farashi da tsadar man fetur a lokuta da dama. Kenan, a irin wannan Gwamnati ita ke cin kazamar riba idan an yi la’akari da yadda yake samun hauhawar farashi a kasuwannin duniya wanda hakan ke sabbaba hauhawar farashin kaya.

  Kar a manta fa, a yayin da aka sami hauhawar farashin kaya, da zarar ya sauka, mai kasuwancin da yake da tsohon abin da ya saya a farashi mai tsada; muddin yana son ya sayar da kayansa cikin mutunci, to wajibi ne ya dawo da shi farashi mai sauki irin wanda aka dawo da shi. Tambaya a nan, faduwa ya yi ko riba ya samu? Ita fa Gwamnati a nan ba za ta yi la’akari da hakan ta rage masa asara ba.

  Hujja ta Bakwai VII

  Idan muka dauki zamanin cutar COVID-19 a matsayin misali, an sami hauhawar farashi. Amma fa idan aka yi la’akari kusan raba daidai ake yi tsakanin Gwamnati da ‘yan kasuwa. Domin an tsaurara musu, wannan ya sanya wasu suka sami karayar arziki duk da sun sami makudan kudade. Da wannan Gwamnati da yake rumbu ce, sai ta rinka tura wa kamfanonin ‘yan kasuwa tallafi domin su farfado daga doguwar suman da suka yi. Wani aiki sai manya!

  Karkarewa

  Gwamnati ba ki asara! Gwamnati mai babban rumbu!! Idan alkalai da masu bibiya za su nutsu su kuma fahimci wadannan hujjoji da na zayyano da kyau, na san za su yarda da ni dari bisa dari kan wannan batu. Faduwar dan kasuwa tana da alaka da rangwame, karyarwa da zagwanyewar arziki. Amma fa Gwamnati duk ba ka taba ji an ce ta karye ba, tare da cewa abokanen tattaunawarmu na ganin tana faduwa! To me zai jefar da ita?

  Da wannan nake cewa ‘mu huta lafiya’.

  Hafsat Muhammad Grema, wakiliyar Yobe Authors Forum

Comments

3 comments