Rubutu

Blogs » Harshe da Adabi » Dabarun rubutun labari 01: Raunin labari a sikelin adabi

Dabarun rubutun labari 01: Raunin labari a sikelin adabi

 • Dabarun Rubutun Labari zai rinƙa kawo muku hanyoyin ko dabarun rubuta labaran Hausa ta amfani da salo mai armashi da karsashi. Idan aka bibiyi shafin daga farko har ƙarshe za a sami tagomashin rubuta labarin Hausa wanda zai ja hankalin mai karatu, musamman ga masu sha’awar shiga gasannin ƙagaggun labaran Hausa, shafin zai ba su damar rubuta labarin da zai yi zarra a tsakanin takwarorinsa.

  Kasancewar wannan it ace makala ta farko, abu muhimmi da ya kamata mu sani shi ne yadda ake gane nagartar rubutu da kuma akasin hakan. Kamar yadda ake auna abubuwa biyu a sikeli don fahimtar wanda ya fi nauyi, haka shi ma masanin adabi yake auna nagartaccen rubutu da kuma rarrauna ta hanyar amfani da sikelin Adabi. Akwai abubuwa bakwai waɗanda kiyaye su yake kawo nauyin labari a sikeli, irin nauyin da duk labarin da aka ɗora su a sikeli tare da shi zai iya yin rinjaye ko da kuwa a cikin gasa ne.

  1. Raunin labari a sikelin adabi

  Ta yaya labari yake rasa nauyi a sikelin Adabi? Manazarci ko alƙali zai fahimci raunin labari ne ta hanyar yin la'akari da wasu muhimman gaɓoɓi guda biyar.

  • Rashin ganɗoki a labari.
  • Iya fahimtar akalar labari (abin da zai faru a gaba)
  • Rarraunan salo.
  • Kufcewar salo
  • Rashin haskakken jigo.

  Duk wani labari nagartacce yana da kyau ya kuɓuta daga faɗawa ɗayan abu huɗun nan. Don haka yana da muhimmanci mu tattauna a kan kowannen su don sake fahimtar yadda suke.

  • Rashin ganɗoki a labari

  Ganɗoki a labari shi ne mutum yana karatu ya riƙa jin har ya matsu ya ji ƙarshensa, ya riƙa jin ba ya son ya ajiye littafin. Wani lokacin irin labarin da ya samu ganɗoki mai kyau har hana shagalalle yin salla yake yi a lokacinta. Yana da kyau mu mayar da hankalinmu sosai a kan wannan gaɓar, saboda hatta alƙalan gasa idan suka samu labari mai ganɗoki yana yi musu tasiri, ta yadda suna iya sha'afa da duba kura-kuran marubucin, su yi ta tafiya daɗin labarin yana ɗibar su. Wani lokacin sai sun yi nisa za su tuna cewa ashe fa har da duba kura-kurai suke yi ba nishaɗi kaɗai ba. Ba sai an faɗa ba, duk labarin da ya ja hankalin alƙali zai yi wuya shi alƙalin ya ba wa wannan labarin makin da bai kamata ba, irin haka ne ke jawo sai ka ga labarinka ya fi na wanda ya zo na ɗaya jigo mai kyau, amma shi an ba shi na ɗaya kai ba a ba ka ba. To abin tambaya shi ne yaya za a yi mu samar da ganɗoki a labaranmu? Wannan yanzu ya kamata mu tattauna kafin mu je gaɓa ta gaba.

  Ganɗoki

  Ganɗoki dabara ce da marubuci yake tsarawa wajen riƙe mai karatunsa, ta yadda duk lokacin da mai karatun ya ɗauki labarin yana karantawa zai ji ba ya so ya ajiye shi. Ana samar da ganɗoki ne da dabarar da mai jan kunne yake kira ‘what happens next' ma'ana mai zai faru a gaba?Dabarar ita ce a riƙa yanyanka labari yadda kafin a gama warware matsala guda an sake saƙa wata, ana warware wacce aka sake saƙawa kuma sai wata mai girma da ta fi ta baya ta sake rikitowa. A haka za a yi ta tafiya har a zo ƙarshen labarin.

  Wannan salo na sa mai karanta labari ya ɓata lokacinsa yana karatu cike da zaƙuwa da son jin me zai faru a ƙarshen labarin ba tare da ya gajiya ba. Dabarar ita ce, kana cikin nuna tauraronka yana matuƙar buƙatar kuɗin da zai yi wani muhimmin al'amari da shi, sai ka nuna cewa ga shi ya tsinci wasu maƙudan kuɗaɗe a jaka. A daidai wannan gaɓar da tauraron yake murna ya samu kuɗi, to shi ma fa mai karatu murna yake yi cewa tauraronsa ya samu kuɗin da zai yi wannan muhimmin al'amarin. Ashe kuma a baya ka nuna cewa tauraron mutum ne mai gaskiya da amana. Kafin ya yi amfani da kuɗin kawai sai ka nuna cewa ga wasu marayu suna cigiyar kuɗin, ashe na kayan gadonsu da aka sayar za a raba musu kuɗin ne. Kun ga kenan dolen tauraron ya ɗauki kuɗin su ya ba su tun da shi mai amana ne.

  To daga nan ne bayan ya ba su kuɗin shi kuma mai karatu zai fara tunanin ‘what happens next,’ ma'ana a ina kenan kuma tauraron zai sake samo wani kuɗin da zai yi wannan muhimmin al'amarin? Irin wannan tunanin shi zai riƙa riƙe makarancin labarinka ba tare da ya sani ba har ya je ƙarshen shi.

  Salo da misalansa a aikace

  Salo ya ƙunshi irin yadda za ka riƙa saƙa maganganu da ayyukanka a cikin labari, don haka ana son salo ya zama ƙaƙƙarfa ko nagartacce, wato ya zamana ana karanta rubutu yanayin salon da aka yi amfani da shi ya riƙa tafiya da hankalin mai karatu. Ba wai salo ya zama rarrauna ko miƙaƙƙe ba irin wanda babu wani abu na armashi a cikinsa.

  Misalin yadda za a fahimci muhimmancin salo a cikin labari shi ne, irin misalin mutane biyu da suka sayi atamfa ko shadda iri ɗaya masu tsada ɗaya. Ɗaya a cikin su ya kai wa tela wanda ya iya ɗinki sosai, ɗayan  kuma ya kai wa tela wanda bai iya ɗinki ba. Duk tsadar shaddar ko atamfar da telan da bai iya ɗinki ba ya ɗinka, ba za ta burge mutane ba har ta ja hankalinsu idan an saka a jiki kamar ta telan da ya iya ɗinki. Za ku yarda da ni cewa atamfa ko shadda mafi araha za ta iya fin ita mai tsadar jan hankali idan ta samu tela mai kyau, to haka shi ma rubutun labari yake. Shi ya sa wani lokacin sai ka ga wani wanda labarin shi bai kai naka samun jigo mai kyau ba amma ya zo na ɗaya a gasa kai ba ka zo ba.

  Marubucin da ya iya salo da ƙirƙira tamkar telan da ya iya ɗinki ne, hakanan marubucin da bai iya fitar da salo da alƙalaminsa ba tamkar tela ne da bai iya ɗinki ba. Shi ya sa mabanbantan marubuta za su iya ɗaukan jigon labari ɗaya amma ka tarar banbancin daɗin labaransu tamkar banbancin garɗin koko da madara. Mu nazarci waɗannan misalan:

  Rarraunan salo

  Na je wajenta jin hirarta mai daɗi ta barni a tsaye ta ƙi fitowa har na fara gyangyaɗi na gaji na tafi.

  Nagartaccen salo

  Na je ba wa ruhina abincin da yake muradi na daɗaɗan kalamanta masu yi min daɗi kamar ana sosa min kunne, ta bar ni a tsaye kamar kwatar raken da aka dasa har idanuwana suka fara nauyi, na fara gani dishi-dishi na yi gaba kafin bacci ya yi gaba da ni.

  Abin lura, duk waɗannan misalan abu ɗaya ake so a ce a cikin su, abin tambaya a nan shi ne wanne daga cikin biyun ne zai fi jan hankalin mai karatu? Ga wasu misalan:

  Rarraunan salo

  Rantsattsiyar motar ta shige cikin asibitin da mai gadi ya buɗe ƙofar. Kallon ƙofar asibitin kaɗai ya isa ka fahimci asibitin masu kuɗi ne.

  Nagartaccen salo

  Rantsattsiyar motar ta sulala cikin asibitin da mai gadi ya buɗe wawakeken ƙyaurensa sululuf irin yadda maciji yake sulalawa raminsa, ba ka jin ko kukanta. Ƙofar da kallon ta kaɗai ya wadatar ka fahimci asibitin na masu yatsu da yawa ne.

  Kufcewar salo

  Shin mene ne kufcewar salo? A yayin da ake jan ruwa a rijiya, cikin rashin zato akan samu igiya ta kufce a hannu ta faɗa rijiya ba tare da zaton mai jan ruwan ba, to irin wannan kufcewa a rashin zato na salon labari shi ne dai kufcewar salo a labari. A cikin taƙaitattun kalmomi ana iya cewa kufcewar salo shi ne: Saɓa, ko rashin cika ƙa'idar komai a komai.

  Kamar sauran duka rauni uku da muka yi a baya, shi ma kufcewar salo yana nakasta labari ya rage masa nauyi a sikelin Adabi. Shi ya sa yake da matuƙar muhimmanci ga marubuci, bayan ya gama rubuta labari ya sake nazartarsa ciki da bai don tacewa da tsefe duk abin da yake na kuskure. Mu kalli waɗannan misalan ta fuska uku, don sake fahimtar abin da ake nufi da kufcewar salo.

  Na farko

  Ana tsaka da tsuga ruwan sama kamar da bakin ƙwarya aka kira Kamal aka sanar da shi cewa matarsa Farida mai tsohon ciki ta yanki jiki ta faɗi, an ɗauketa an tafi da ita asibiti ranga-ranga rai a hannun Allah. Kamal a kiɗime ya miƙe zunbur daga kan tebur ɗin da suke zaune a rumfar Auduwa mai shayi ya fantsama cikin ruwan, duk da yana jin mutane suna tambayar shi ko lafiya zai fita a wannan ruwa. Bai iya tsayawa amsa musu ba ya nufi gurin da motar shi take a ajiye. Tun kafin ya ƙarasa wajen motar ya danna linzamin da yake hannun shi, motar ta ɗan yi wani ƙara daidai lokacin da sakatun ƙofofinta suka ciye. Ya fuzgo ƙofar motar ya afka ciki, ya saka mata ki ya tasheta, bai jira komai ba ya banke ƙofar tare da saka wa motar giya ya fuzgeta da gudu, tayoyinta suka tirji ƙasa suka yi wata irin ƙara gami da tayar da ƙura...

  Abun lura:

  Anya kuwa idan ana yin ruwan sama tayoyin mota za su tayar da ƙura? Wajen ƙoƙarin nuna hanzarin Kamal da marubucin yake yi ne har salo ya kufce masa ya rubuta abin da yake ba zai taɓa yuwuwa ba (mota ta tayar da ƙura ana tsaka da yin ruwa). Wannan misali ɗaya kenan a cikin irin misalai uku da za mu nazarta a wannan gaɓa ta kufcewar salo.

  Za mu dakata a nan sai a biyo mu a kashi na gaba a filin namu na Dabarun Rubuta Labari.

  Jibrin Adamu Rano, daga Rano, Kano, Nigeria

Comments

5 comments