Makalu

Blogs » Zamantakewa » Karatu ko aure ya fi muhimmanci ga diya mace?

Karatu ko aure ya fi muhimmanci ga diya mace?

 • Barkanmu da sake kasancewa a wannan fili na muhawara wanda ke zuwa daga taskar Bakandamiya, inda marubutan Hausa suka wasa ƙwaƙwalensu wajen kawo hujjoji masu kare ra’ayinsu a kan batutuwa mabambanta da suka shafi rayuwarmu ta yau da kullum. A yau za ku karanta karawa ta shida, wadda ta wakana a ranar 28 ga watan Nuwamba, 2020 Miladiyya. Karawa ce a kan taken “Tsakanin Karatu da Aure wanne ya fi muhimmanci ga ɗiya mace?”

  Zaƙaƙuran ƙungiyoyin marubuta na Inside Arewa Writers Association da kuma Mizani Writers Association ne suka yi wannan karawa, kodayake wakilan ɗaya ƙungiyar sun yi nusan; ba su zo da hujjojinsu ba har lokacin da alƙalan muhawara suka ƙyanƙyana ƙararrawar rufewa. A biyo mu cikin muhawarar domin ganin ƙungiyar da ta bayyana da kuma wadda ta yi nusan.

  Masu girma alƙalan gasa, masu bibiyarmu da sauran abokan karawata a wannan muhawarar, amincin Allah ya tabbata a gare ku.

  Ina mai matuƙar farin cikin kasancewa a wannan zaure inda zan wakilci ƙungiyata mai suna INSIDE AREWA WRITERS ASSOCIATION wajen kawo ƙwarara kuma gamsassun hujjojina kan cewa aure ya fi karatu muhimmanci ga ɗiya mace.

  GABATARWA

  Assalamu alaikum 'yan uwana, ina mai farawa da sunan Allah mai tsarki da buwaya, tare da neman tsira da amincinsa su ƙara tabbata ga fiyayyen Halitta Annabi Muhammad (S.A.W) da Iyalansa da Sahabbansa baki ɗaya, da dukkannin waɗanda su ka biyo bayansu da kyautatawa har zuwa ranar sakamako. Ina mai roƙon Allah da ya yi mana jagora tare da taimako gami da sanya albarkarsa wajen daidaituwar alƙalami domin rubuta abin da yake dai-dai kuma mai amfani, sannan kuma mai faɗakar da al'umma. A ƙarshe ina roƙonsa da ya kare mu da kariyarsa daga tuntuɓen alƙalami ko harshe wajen rubuta ko furucin abin da ba shi cikin da'irar turba ta farin Jakada ɗan Abdullahi (S.A.W) a wannan Muhawara.

  SHIMFIƊA

  Ilimi shi ne gishirin zaman duniya domin idan babu ilimi to tabbas rayuwa ta gurɓace. Kamar yadda aka sani a Musulunci, ilimi wajibi ne ga namiji ko mace. Mace kamar namiji, akwai buƙatar ta yi ilimi domin ita uwa ce, ita ke rainon 'ya'ya kuma halaye da ɗabi’unta abubuwan kwaikwayo ne ga 'ya'yan. Haƙiƙa ilimin ɗiya mace na da muhimmanci ƙwarai, don idan ka ilmantar da ɗiya mace to ka ilmantar da al’umma. Yana da matuƙar muhimmanci mata su yi karatu kuma ya zama wajibi.

  HUJJOJI

  1. Mace mai ilimi ita ce za ta san yadda za ta tafiyar da gidanta da kyau idan ta na da hankali.

  1a. Mace ita ce uwa, ita za ta sa yaranta a kan hanya, har shi mijinta da kan sa; ita kan koya masa ɗabi’u masu kyau. Idan kuwa ba ta da ilimi, ba ta san abin da ya kamata ba tana iya zama makauniyar jagora ga 'ya'yansu.

  1b. Bugu da ƙari, ta hanyar karatu ne za ta iya taimakon Iyalanta da 'yan uwanta da al'ummar da take rayuwa cikinsu.

  2a. Duk wata mace mai ilimi yana da matuƙar wahala ta din ga samun matsala da mijinta, domin tasan yadda za ta ba shi kyakkyawar kula, da tarairayarsa, da karantar halayensa ta yadda za ta san abin da yake so da wanda ba ya so.

  2b. Mace mai ilimi takan zauna da dangin mijinta lafiya, komai wahalarsu da matsalarsu saboda ta san yadda ake zama da mutane daban-daban.

  2c. Wacce take da ilimi ba sai mijinta ya nemi mai yi wa yaransa jingar su (Homework) ba, da muraja'a ta Islamiyya domin ita za ta musu a cikin gidanta, domin ta wadatu da ilimin.

  KAMMALAWA

  Duba da tarin bayanan da na lissafo da hujjojin da na gabatar domin nusar da al’umma ababe mabambanta za a duba a ba mu maki mafi dacewa.

  Daga ƙarshe ina yi wa Alƙalan gasa, masu bibiyarmu da sauran abokan karawa ta wannan muhawara fatan alkhairi, Allah Ya dafa mana bisa lamuranmu.

  Faridat Sweery, daga ƙungiyar Inside Arewa Writers Association.

  Mizani Writers Association su ne ba su sami damar gabatar da nasu hujjoji a wannan muhawarar ba.

Comments

1 comment