Makalu

Blogs » Hira da Mutane » Rukayya Ibrahim Lawal ta bayyana dalilanta na fara yin rubutu

Rukayya Ibrahim Lawal ta bayyana dalilanta na fara yin rubutu

 • Assalamu alaikum, 'yan uwa barkanmu da saduwa a cikin wannan shiri mai suna BAKON MAKO, wanda ni Hauwa'u Muhammad da abokiyar aikina Maryam Haruna ke  kawo muku hira da marubuta daban-daban. Shiri ne da ke zakulo muku marubutanmu na wannan gida har ma da na waje kuma ya tattauna da su dan jin irin gudummawa da gwagwarmayar da suka sha a rayuwa da kuma bangaren rubutu. A yau za mu tattauna ne da hazika kuma fitacciyar marubuciyar nan Rukayya Ibrahim Lawal wacce aka fi sani da (Ummu Intisaar) wacce ta rubuta littafin 'Yar Gantali. Da fatan za ku biyo mu a hirar.

  T1: Muna son jin takaitaccen tarihin bakuwar

  Rukayya Ibrahim Lawal: Yawwa ina godiya

  Da farko dai sunana Rukayya Ibrahim Lawal wacce a duniyar marubuta aka fi sani da Ummu inteesar, an haife ni a shekarar 1997, na yi primary school ɗina a Family Support Model Primary School Sokoto daga 2003 zuwa 2009, daga nan na shiga Nana Girl Secondary School Sokoto na yi JSS ɗina inda na fice daga makarantar zuwa Abdul Rashid Adisa Raji Speacial school, a can na yi candy na a shekarar 2015.

  A lokacin ban samu damar komawa makaranta ba sai a 2017, inda na shiga Ummaru Ali Shinkafi Polytechnic Sokoto, ban shekara ba na fice saboda wasu dalilai, nan ma ban kuma shiga wata makarantar ba sai a shekarar 2019 na shiga Shehu Shagari College of Education Sokoto inda na ke karantar ECCE wato (early childhood care and education) yanzu haka ina NCE 2 ne.

  Wannan shi ne takaitaccen tarihina

  T2: Menene ya ja ra'ayinki har kika fara rubutu?

  Rukayya Ibrahim Lawal: Gaskiya abinda ya ja ra'ayina shi ne yanda matsaltsalu suke faruwa a society namu, a lokacin baya akwai wani abun da ke faruwa wanda yake ci min tuwo a kwarya na rasa hanyar magance shi, sai na nemi wata marubuciya na bata labarin domin ta rubuta shi tare da kawo mafita, amma sai ta kasa isar da sakon yanda nake so, ganin hakan ya sa na fara tunanin me zai hana ni na rubuta tunda a baya ina da ra'ayi a kan rubuce-rubucen.

  T3: A wacce shekara kika fara rubutu?

  Rukayya Ibrahim Lawal: Na fara wallafa littafi a November 2019, Soyayyar Meerah shi ne na farko da na fara saki, duk da ba shi ne littafin farko da na rubuta ba, sai dai sauran suna rubuce ne a 40leaves ɗina

  T4: Litattafai nawa kika rubuta kuma wanne ne bakandamiyarki?

  Rukayya Ibrahim Lawal: Littafaina da suka watsu a media yanzu guda biyar ne, sai wani na haɗaka da muka fara nida wata ƙawata

  'Yar Gantali shi ne bakandamiyata.

  T5: Wanne kalubale kika fuskanta a harkar rubutu?

  Rukayya Ibrahim Lawal: To dama a rayuwa ba za'a rasa ƙalubale ba, in ko da akwai kalubalen da na fuskanta bai wuce rashin yawan comment daga readers ba, sai kuma yanda wasu 'yan uwa da kuma abokaina suke sukar harkar rubutun da nake.

  T6: Wanne littafi ne ya fi ba ki wahala lokacin rubuta shi?

  Rukayya Ibrahim Lawal: To a gaskiya Soyayyar Meerah shi na fi shan wahalar rubutawa saboda sai da na rubuta a notebook sannan na zo ina yin copy a waya, sai a sanadin kama shi ma na wahala.

  Littafin da ya fi mun sauƙin rubutawa shine Rashin Gata domin shi gajeren labari ne.

  T7: Wacce hanya kike bi wajen samun jigon labarinki?

  Rukayya Ibrahim Lawal: Ina samun jigona ne daga tunani, wani lokacin kuma idan ana hira na ji wani abinda ya kamata na rubuta sai na ɗauki jigo. Editing ya fi wahalar dani akan rubutun.

  T8: Wane ne ubangidanki a rubutu?

  Rukayya Ibrahim Lawal: Idan har ubangida shi ne wanda ya koyawa mutum rubutu to ni kam gaskiya ba ni da shi, sai dai daga baya na samu masu dubamin rubutuna bayan na kammala, waɗannan mutanen kuwa sune:

  Yaya Ibrahim Muhammad Indabawa da kuma yaya Yusuf Gumel.

  T9: Wanne tasiri marubuta suke da shi a cikin al'umma?

  Rukayya Ibrahim Lawal: A gaskiya marubuta mutane ne masu matuƙar tasiri acikin al'umma domin kuwa suna aikewa mutane saƙonsu da gyararraki ta hanyar yin amfani da kaifin basirarsu suke warware matsalolin dake addabar wasu mutanen, don haka marubuta suna da matuƙar tasiri.

  Tabbas saƙon da suke aikawa yana isa cikin gaggawa kuwa, domin da yawan mutane sun gyara rayuwarsu a dalilin wasu rubutuka da suka karanta.

  Ni kaina akwai waɗanda suka gayamun sun ɗauki darussa dalilin rubutuna, kai zan iya cewa wannan abun ma ya zama gama gari yanzu don ga shi nan muna gani, ko a hakan na barki nasan kin fahimci saƙon ya isa.

  T10: Wane ne tauraronki?

  Rukayya Ibrahim Lawal: Taurarona a maza shi ne Abdul aziz Sani Madakin Gini, a mata kuwa akwai Halima K. Mashi, idan kuma aka dawo a online akwai Abubakar Auyo da A'isha Ali Garkuwa. waɗannan su ne madubina a rubutu.  

  T11: Wacce shawara za ki bawa marubuta?

  Rukayya Ibrahim Lawal: Shawarar da zan basu ita ce: su tsarkakke alƙalummansu sannan su yi rubutu mai ma'ana da fa'ida wanda ko bayan ransu mutane zasu yi alfahari da su, kuma su dinga lalubo muhimman jigo na abubuwan da suke addabar al'umma a wannan zamani, kuma su guji wulaƙanci domin wulaƙanta ɗan Adam bashi da amfani, ba wai don kana ganin ka zama wani a yanzu ba sai ka tsiri wulaƙanci, wannan abu ne da zai iya rusa ɗaukakar da ka samu.

  T12: A cikin shirye-shiryen Zauren Marubuta na Bakandamiya wane shiri ya fi birgeki?

  Rukayya Ibrahim Lawal: Shirye-shiryen da suka fi burge ni sune:

  Filin koyar da yanda ake rubutun fim, da kuma Wasa ƙwaƙwalwa sai wannan shirin da ake gabatarwa a yanzu wato Bakon Mako.

  T13: Su waye taurarinki a wannan zaure?

  Rukayya Ibrahim Lawal: To taurarina anan su ne, yayana Abu Hisham, Lawan Dalha, Rahama Lawan da ke kanki harma da sauran mutanen wannan dandalin kowa na burge ni.

  T14: Mene ne burinki a harkar rubutu?

  Rukayya Ibrahim Lawal: To burina shi ne na zama babbar marubuciya wacce duniya za ta yi alfahari da irin rubutukana, kuma rubutuna ya tasirantu a zuciyar mutane ta yadda zasu gyara.

  T15: Film da littafi wanene ya fi saurin isar da sako?

  Rukayya Ibrahim Lawal: Film ya fi saurin isar da sako. Abinda yasa shi ne ina ganin cewa kamar a fim ɗin saƙunan da nake son turawa zasu fi saurin isa tare da tasirantuwa a zuciyar masu kallo.

  T16: Wacce shawara za ki iya ba wa sabuwar marubuciya?

  Rukayya Ibrahim Lawal: Shawarata a gare ta ita ce, ta nutsu ta mayar da hankali sosai gurin samo jigo mai kyau da ma'ana domin shi rubutu abu ne da bai kamata a faɗa masa haka kawai ba ba tare da sanin yanda yake ba. Ta kuma shiga bincike da natsari akan harshen Hausa da ƙa’idojin rubutu domin ta samar da labari mai ma'ana da daɗin karatu, matuƙar ta yi hakan to rubutunta zai samu karɓuwa nan da nan.

  T17: Wacce shawara za ki ba wa marubuta masu dauko labari su kasa karasawa?

  Rukayya Ibrahim Lawal: To a ganina tun farko bai shiryawa yin rubutun ba ne, ko kuwa ba shi da takaimamen abin rubutawa, ko ya saka kasala da kuma sarewa a cikin lamarin wannan shine zai sa ya kasa ƙarasawa.

  Shawarata a gare su shi ne, su jure su cire tsoro ko fargaba, su nace tare da jajircewa kuma su kaifafa tunaninsu tare da yin bincike akan abinda zasu yi rubutu akai.

  Tsara tambayoyi da gabatarwa: Hauwa'u Muhammad tare da Maryam Haruna

Comments

1 comment