Makalu

Blogs » Hira da Mutane » Burina bai wuce na fitar da littafi kasuwa ba–Rabi’atu SK Mashi

Burina bai wuce na fitar da littafi kasuwa ba–Rabi’atu SK Mashi

 • Assalamu alaikum warahmatullah. Barkanmu da sake saduwa a sabon shirinmu na Baƙon Mako wanda ni Maryam Haruna tare da abokiyar aikina Hauwa'u Muhammad ke gabatarwa. A yau shirin ya yi tattaki ya zaƙulo muku fitacciya kuma shahararriyar marubuciya mai suna Rabi'atu SK Mashi. Ku kasance damu domin jin ko wacece.

  T1: Muna son jin tarihin marubuciya a taƙaice.

  Rabi'atu SK Mashi: Wa âalaikis salam. Sunana Rabiatu, an haife ni a garin Mashi, na yi primary da secondary a garin Mashi, yanzu haka na tsaya a matakin NCE. A bangaren Islamiyya nayi sauka da hardar fiye da rabi, bana da aure.

  T2: Ko zamu iya sanin dalilin da ya tsunduma ki, cikin harkar rubutu?

  Rabi'atu SK Mashi: Karatu da kuma sha'awar rubutun, tun lokacin da nake karantawa yana matuƙar burgeni, na ji ina so nima na ringa rubutawa ina aika nawa saƙon. Tun a lokacin da nake karantawa, idan naga an yi ba yanda nake so ba, sai inji dama ni ce nake rubutawa ba zan yi hakan ba, na kan samu littafi na rubuta nawa koda ban karasa labarin ba.

  T3:  Wane irin ƙalubale kike ko kuma kika taɓa fuskanta a rubutunki?

  Rabi'atu SK Mashi: To kalubalen dana fuskanta dai bai wuce na wani daya taba satar mun littafi ba ba tare da izini na ba kuma a lokacin da nake rubutashi, lokacin an yi badakala sosai a lokacin, daga karshe ma sai na daina rubuta littafin ma.

  T4: Ko zamu iya sanin zuwa yanzu littatafai nawa kika rubuta kuma wanne ne bakandamiyarki?

  Rabi'atu SK Mashi: Na rubuta littafai zasu kai 18 - 20, Bakandamiyata shi ne HAFSATUL KIRAM.

  T5: Ko zamu iya sanin taƙaitaccen labarin bakandamiyar taki?

  Rabi'atu SK Mashi: Hafsatul Kiram labari ne akan wata budurwa da aka ma auren hadi da dan uwanta mashayi kuma manemin mata. Saboda kyawawan halayen ta tare da kyautata zaton zata iya canjashi, ta karbi auren dan uwanta hannu bibbiyu tasha wahala sosai a hannunsa, ya nuna mata kiyayya sosai kafin ta samu nasarar karkato hankalinsa gareta da kuma samun soyayyarsa.       

  T6: Wane irin buri kike da shi a harkar rubutu?

  Rabi'atu SK Mashi: Burin da nake dashi bai wuce na fitar da littafi kasuwa ba, ina nan da wannan burin insha Allah, bangaren shahara kuma Alhamdulillah duk inda ya kamata in kai na kai, duk da ban yi suna ba sosai, anma dai ina jin dadin yanda aka sanni da rubutu na.    

  T7: Shin kina da wata uwar gida ko kuma uban gida a harkar rubutu?

  Rabi'atu SK Mashi: Gaskiya bana da uwargida ko ubangida a bangaren rubutu, sai dai mutanen da suke kara mun karfin gwiwa ta bangaren rubutu, Abdulazeez (Ililee) Abdul Jega, Najibullahi da kuma Ahmad Funtua.       

  T8. Salon wane marubuci ne ya fi burgeki, har kike ganin zai iya zame miki allon kwaikwayo?

  Rabi'atu SK Mashi: Gaskia salon rubutun Halima K/Mashi, yana matukar burgeni sosai.   

  T9: Wace irin shawara za ki bawa ƙananun marubuta masu tasowa?

  Rabi'atu SK Mashi: Su ji tsoron Allah su tsarkake zuciyarsu akan duk abinda zasu rubutawa, su sama ransu ne zasuyi ne domin fadakar da alumma ko wa’azantarwa da tunatarwa, bawai don neman suna ko kudi ba.   

  T10: A wane yanayi rubutu ya fi yi miki daɗi? 

  Rabi'atu SK Mashi: To bazan iya cewa ba, saboda ni bana da kebabben lokacin yin rubutu, ina yinsa ko yaushe ya zomin, cikin dare da asuba ko da rana, koda cikin mota ne ina iyayin rubutu na a duk sanda ya zomin, shiyasa ba ko yaushe nake typing ba sai naji ina jin yinsa.

  T11: Shin adabin hausa ya tasirantu da adabin wani yare? idan e, wanne irin tasiri ya yi? idan kuma bai tasirantu ba me ya sa?

  Rabi'atu SK Mashi: Adabin Hausa ya tasirantu da yaren Larabci ne.

  T12: Kasancewar rubutun novel da rubutun film kamar danjuma ne da danjumamai shin kina sha'awar rubutun film? idan hakane me ya sa? idan ba haka bane saboda me?

  Rabi'atu SK Mashi: Ina da sha'awa sosai, ina so kamar yanda nake rubutawa ana karantawa na rubuta a hau, na zauna ina kallon wasu da yanayin dana tsara musu, kuma suna fadin kalaman dana rubuta a bakinsu.

  T13: Wacce irin shawara za ki bawa sababbin marubuta? A matsayinki na marubuciya da ta kwana biyu a harkar rubutu.

   Rabi'atu SK Mashi: Ta yi bincike sosai kafin tayi rubutu, sannan ta tabbatar tana da jigo mai kyau, kuma ta tsara labarin cikin salon da zai kayatar

  T14: Mene ne yake jawo wa ki ga marubuci ya ɗauki rubutu amma ya kasa ƙarasawa, wacce irin shawara za ki bawa irin waɗannan marubutan?

  Rabi'atu SK Mashi: A rashin tsara labarin daga farko har karshe kafin a fara. Rashin samun kwarin gwiwa daga wurin makaranta, gajiya, da tunanin wani labarin da suke ganin zai fi wancan samun karbuwa ko zasufi jin dadin rubutashi  

  T15: A wacce ƙungiya kike rubutun, kuma meye manufar ƙungiyar taku?

  Rabi'atu SK Mashi: Ina kungiyar Nagarta Writers Association, manufarmu ita ce kawo gyara ga yin rubutu mai tsari da ma'ana, taimakawa kananun marubuta masu tasowa.

  T16: Me zaki iya cewa akan lamarin kasuwancin online na littafi?

  Rabi'atu SK Mashi: To gaskiya abun yayi matukar burgeni da yanda marubuta ke cin moriyar fasaharsu, kuma abun ya samu karbuwa sosai ga makaranta har ma da marubutan saboda yanda har masu buga littafin suka fara dawowa siyayyar online, wannan ci gaba ne sosai ga rubutu.

  T17: Kin taɓa sayar da littafi? idan kin sayar wanne ne?

  Rabi'atu SK Mashi: A gaskiya ban taɓa siyarwa ba, anma ina saka ran siyarwa a gaba insha Allah.

  T18: Kin ce an taɓa satar miki littafin da kike rubutawa, shin wanne mataki kika ɗauka akan satar da aka yi miki?

  Rabi'atu SK Mashi: Ba ni ce na dauka mataki ba kungiyata ce, manyan kungiyata sun sameshi an yi maganar fahimta sosai kuma ya bada hakuri akan hakan

  T19: Kun taɓa yin gamayya wajen rubuta littafi ke da wasu ya sunansa?

  Rabi'atu SK Mashi: Mun yi gamayyar rubuta littafi da wasu ba mutum daya ba. Mun rubuta BANI BANE nida Amratu A Mashi, mun rubuta A YINI DAYA da wani dana kasa tuna sunansa, mun rubutu DODON JATAU tare da RAZ, Amrah A Mashi da kuma Zahra BB, mun rubuta MASARAUTARMU tare dasu, da wani shima na manta sunansa, sai kuma mun rubuta AMANAR AURE da HAKA SO YAKE tare da Abdul Jega, mun rubuta MAFARIN SO... Mun rubuta DUNIYA GIDAN KASHE AHU tare da Mrs Umar.

  Tsara tambayoyi da gabatarwa: Maryam Haruna tare da Hauwa'u Muhammad

Comments

1 comment