Rubutu

Blogs » Muhawarar Bakandamiya 2020 » Rubutu da waka wanne ya fi isar da sako da amfani ga mutane?

Rubutu da waka wanne ya fi isar da sako da amfani ga mutane?

 • A ci gaba da kawo muku yadda muhawarar Zauren Marubuta na Manhajar Bakandamiya ta gudana, karawa ta bakwai za ku ga yadda kungiyoyin Proficient Writers Association da Yobe Writers Association suka yi tsayuwar gwamin jaki a taken muhawararsu mai cewa: TSAKANIN RUBUTU DA WAKA WANNE YA FI SAURIN ISAR DA SAKO DA KUMA AMFANI GA MUTANE? Inda kowace kungiya ta kawo hujjojinta wadanda ke bayyana alkiblarsu a gwabzawar. Muhawarar ta wakana ne a ranar 30/11/2020.

  Rubutu ya fi waƙa saurin kai saƙo

  HUJJA TA 1

  Bayan sallama irin ta addini musulunci watau Assalamu Alaikum, mu ‘ƴan kungiyar PROFICIENT WRITERS muna so mu nuna goyon bayan mu akan cewa rubutu ya fi waƙa saurin kai saƙo.

  Rubutu wata hikima ce, da wasu mutane kan yi amfani da ita, domin koƙarin fahimtar da mutane wata manufar tasu .

  A kiyasin masu bincike a duniya, sun nuna cewa babu wata hanyar sadarwa da ta fi rubutu.

  Haka zalika babu lokacin da kwakwalwar ɗan adam take aiki, da kuma dad’a wasa kanta, kamar lokacin da take karanta rubutu, walau labari ko wa’azi, ko labarai na yau da kullum.

  HUJJA TA 2

  Ɗan adam kan iya fahimtar saƙon da aka rubuta masa cikin sauki idan dai ya iya had’a haruffan da aka yi rubutun da shi,

  ko da mutum bai iya karatu ba, wani kan karanta masa, kuma ya fahimci saƙon yadda ya kamata.

  Amma waka fa. Lokuta da yawa idan karin waƙar bai yi daɗi ba mutum ma ƙin saurara yake yi.

  Saboda haka, ita waƙa sautin ne yake jan ra’ayin mutum, har ya hakura ya saurara.

  Rubutu kuwa indai ka fara karantawa, gwagwarmaya ce take afkuwa tsakanin kwakwalwa da kuma tunanin mutum, ya kuma farfaɗo da zuciyarsa, ta raya masa san ganin kwal uwar daƙa.

  HUJJA TA 3

  Akwai lokuta da yawa, da kuma mutane da yawa da ba su fahimtar haruffan da ake rera waƙar da su, balle har su kai ga samun natsuwar fahimtar saƙon da a ke kokarin aikawa, sabanin rubutu da duk inda ka hada haruffa guda biyu, akwai ma’ana da kuma saƙon da zasu yi kokarin sadarwa.

  Ga misali, akwai wani shaharren mawaƙi da ya rasu mai suna Micheal Jackson, da yawa mutane sun san shaharar da ya yi a fannin waƙa, amma akwai baitin waƙarsa da sai bayan sama da shekaru talatin da yinsa aka saka gasa, akan duk wanda ya fadi me yake cewa a baitin wakar zai samu kyauta, mun fi mu dari da muka shiga gasar, amma ba wanda ya ci gasar, sai da aka kawo waƙar a rubuce muka ga “mama say mama say makosa” yake cewa

  Mu kuma muna yin wakar da cewar “mama sa mamasa masa gussa”

  A zaton mu wani yare yake a cikin waƙar, ashe wai turanci ne.

  To kuwa saƙon da aka ɗauki sama da shekara talatin bai isa inda aka aika shi ba, ai tabbas ya zama shirme.

  HUJJA TA 4

  Kuma, mu duba yanayi, ko guraren da aka fi buƙatar rubutu,

  Littafi na nishadi, rubutu ne da ke kai saƙo,

  Makaranta, rubutu ne ɗan aike daga malami zuwa dalibai,

  Ma’aikatu rubutu ne da ke tasiri wajen bayar da bayanin yadda ake so a gudanan da ayyuka,

  Fina-finai na talabijin, sun wanzu ne daga rubutu,

  Kai ita kanta waƙar in har ana son tayi tasirin da ake bukata, to sai an rubuta ta kamar labari, kana a dora mata kari. Saboda haka lokuta da yawa waƙa na samuwa ne daga rubutu, rubutu na iya aikin waƙa ta tsarata kafin a rerera. Amma waƙoƙin  da suka doru a doron labari ba su da yawa.

  Saboda haka in dai kai sako ne babu kamar rubutu, waka ita tafi tasiri a nishadantarwa ga rukunin mutane, saboda akwai wadanda karanta rubutu ya fi saka su nishaɗi sama da waƙa.

  HUJJA TA 5

  Idan muka yi duba da addininmu mai girma Allah Subhanahu wa Ta’ala, rubutu ya yi matukar tasiri a yaduwarsa.

  A rubuce aka ɗinga ajiye AlQUR'ANI mai girma, kuma rubutun aka ɗinga amfani da shi wajen wanzar da saƙonsa ga dukkanin jama’ar duniya.

  A rubuce sahabban Manzon Allah (S. A. W.) suka dinga aje mana hadissai. Haka zalika manƴan malaman da bamu taba sanin su ba, mun ƙaru da ayyukan da suka yiwa addinin islama, saboda rubutaccen al’amari da suka bar mana.

  Da waƙa ce da tabbas an sauya saƙon, saboda dole a lankwasa kalma tayi daidai da amsa amon waƙar, kuma ita waƙa ‘ƴar yayi ce, yayinta na wucewa, ba mai sake bi ta kanta sai mutane kalilan.

  Amma rubutu kuwa zai iya kasancewa ka na wani bincike a wannan zamani, amma ka ɗauko rubutun da wani ya yi sama da shekara dubu ka karanta ka kuma fahimci saƙon.

  Mallam Mai Ahalari ya dau shekaru daruruwa da mutuwa, amma littafin da ya isar da sakon yana nan, ana kuma fahimtar saƙon da ya isar ta hanyar rubutu,

  amman Malam Mai Ishiriniya bai fi shekara arbs’in da mutuwa ba,

  amma da za a je tambayi wanda bai kai wadannan shekarun ishiriniyar ba zai ce bai santa ba.

  Sarauniya Mangu, daga Kungiyar Proficient Writers Association

Comments

1 comment