Makalu

Blogs » Muhawarar Bakandamiya 2020 » Faduwa jarabawa laifin waye tsakanin malamai da dalibai?

Faduwa jarabawa laifin waye tsakanin malamai da dalibai?

 • Barkanmu da sake kasancewa a wannan fili na muhawara wanda ke zuwa daga manhajar Bakandamiya, inda marubutan Hausa suka wasa ƙwaƙwalensu wajen kawo hujjoji masu kare ra’ayinsu a kan batutuwa da suka shafi rayuwarmu ta yau da kullum. A yau za a kasance da karawa ta takwas, wadda ta wakana a ranar 30 ga watan Nuwamba, 2020 Miladiyya. Karawa ce a kan taken “Tsakanin malamai da dalibai laifin waye wajen faduwa jarabawa?” Zaƙaƙuran ƙungiyoyin marubuta na Nagarta Writers Association da kuma Al’umma Writers Association ne suka yi wannan karawa. A biyo mu cikin muhawarar domin ganin yadda muhawarar ta wakana.

  NAGARTA WRITERS ASSOCIATION

  Alkalai, jagorori, masu karatu, abokan fafatawa..., ina nema mana amincin Allah madaukakin Sarki. Na fito ne domin bijiro da karfafan hujjojina a kan cewa, “Faduwa Jarabawa Laifin Malamai ne ba na Dalibai ba!” Na yi mamaki kwarai da na ji cewa akwai wadanda za su dora laifin nan a kan dalibai.

  Hujja Ta Farko

  Rashin kwarewar malamai a fannin abin da suke karantarwa...!

  Kafin nan, zan so da ni da ku mu yi duba zuwa ga ma’anar jarabawa inda take nufin,

  “Gwajin da ake yi wa dalibi domin auna fahimtarsa.”

  Kaso kalilan daga cikin malamai su ke da kwarewa da kuma ilmi a kan fannin da suke koyar da dalibai a makarantu da dama, wanda hakan ya yi tasiri sosai wajen ganin dalibai ba su fahimta ko gane sabgar da Malami ya saka gabansa; za a iske shi kanshi malamin yana da bukatar a koyar da shi wannan fannin. Wasu lokutan kuma sai ya kasance Malami ya dace ne ya koyar da yan aji daya, amma saboda sanayya ko son rai sai a tarar da shi a aji shida tsumu-tsumu! Ta ya za a yi tsammanin samun ‘ya’yan bishiyar da ba a shuka ba? A wannan yanayi kawai za a yi haihuwar guzuma ne, d’a kwance, uwa kwance! Wace jarabawa dalibi zai ci? Na bar muku sani!

  Hujja Ta Biyu

  Rashin samun kyakkyawar alaka tsakanin malami da dalibansa na janyo rashin ganewa ko kyamar darasin da malami ke koyarwa, da zarar hakan ta faru kuwa to ranar jarabawa ba za a wanye lafiya ba; ido zai raina fata, a lokacin ne dalibi zai fara dogon wuya! Yana da matukar muhimmanci malami ya kasance mai sassautawa da kyautata mu’amala tsakaninsa da dalibansa, ko babu komai za su koyi ilmin zamantakewa ta kallon dabi’u da halayensa, uwa-uba kuma darasinsa zai zama gwarzon darasi a wurin dalibai. Ana dacewa da hakan kuwa, to cin jarabawa zai kasance abu mai sauki ga dalibai. Idan kuma aka sami akasin hakan, to malami da kansa ya janyo wa dalibansa turmusuwa da kasa a ranar jarabawa! Kowa dai ya san da muguwar rawa, gara kin takawa.

  Hujja Ta Uku Kuma Ta Karshe

  Lalaci da kasala da son jiki suna taka rawa har da juyi a yayin da aka zo zaman jarabawa, musamman idan duk abubuwan da na wassafa suka taso daga wurin malami. Wasu malaman suna da ra’ayin ‘Wanda ya ci, shi ya iya!’ Saboda wannan tunani nasu sai su rinka wasarairai da aikinsu na ba da karatu, kawai suna jiran ranar jarabawa ta zo su ba dalibi satar amsa ya wuce wurin, idan kuma jarabawar auna fahimta ce da akan tsara a karshen zangon karatu, sai su saukaka tambayoyin yadda dalibai za su lashe, a haka hukumar makaranta ba za ta zarge su da komai ba, tun da an ce bukatar dara, kasawa. To mu dauka cewar jarabawar kammala karatu ce ta WAEC ko NECO ta hadu da lalataccen malami, sai ga shi kuma ranar jarabawar ya kasance azal ta fada wa malamin da zai kawo satar amsa a kwashe bai sami zuwa makaranta ba...! Ko ban ce komai ba an san daliban malam za su rafku da kasa a ranar, tun da ba a koya musu komai ba, sun tsaya tsammanin warabbuka, malam ya ki layya don kai da kafafu! A haka idan dalibai suka fadi jarabawa wane ne sila? Amsa na gare ku

  Da wadannan hujjojin nake so ku aminta da ni kan cewar Faduwar Jarabawa Laifin Malamai ne ba na Dalibai ba!

  Nagode

  Taku, Amra Auwal Mashi, wakiliyar Nagarta Writers Association.

   

  AL'UMMA WRITERS ASSOCIATION

  Assalamu Alaikum! Bayan gaisuwa irinta addinin musulunci, ina mika Godiya da yabo da kirari ga Allah Mai komi Mai kowa da ya bamu ikon yin wannan gasar, abokiyar karawa ta, alkalan gasa duk ina muku fatan alheri.

  Na samu kaina da takaici a lokacin da naji abokiyar karawata na fadin, wai malami shi ne silar faduwar dalibi jarabawa. Ba tare da bata lokaci ba zan fara kawo hujojina kamar haka:

  Hujja Ta Farko

  Laifin faduwar jarabawa a makaranta, ba laifin kowa bane face na dalibai idan aka yi  la'akari da yadda malami ya kan tuntubi daliban bayan ya gama yi musu darasi, sau da yawa dilibai basu fiye mayar da hankali ba musamman idan har ya zama akwai sabani ko rashin jituwa a tsakaninsu, sukan dau karan tsana su daurawa Malami, wannan na bada gudunmawa sosai gurin rashin fahimtar darasi, sai idan har anzo jarabawa su fara ambatar ba a yi musu ba.

  Haka zalika yin aboki ko kawa wacce ba ta mai da hankali a cikin aji, shi ma yana bada gudunmawa sosai gurin faduwa jarabawa.

  Sannan kuma rashin lura da iyaye kan yi a kan yanayin karatun yaro, babu duba littatafansa ko abin daya danganci Karatun, to hakan kan taimaka sosai gurin faduwa, saboda tun farko babu wani tagazawa na taimakawa yaro daga gurin iyaye.

  Wajen yin wasa tsakanin malami da dalibi ma wani gudunmawa ne dake baiwa dalibai faduwa a jarabawa, domin dalilbi zai dauki malami tamkar abokin wasan sa, kamar kowace irin magana ta fito daga bakinsa zai fadi hakan kan sanya malami yaji bacin rai, ko musu, ko makamanci abin da zai dai kawu raini a tsakaninsu.

  Hujja Ta 2

  Lokacin da na ji ana fadin wai malami shi ne silar faduwar dalibi jarabawa na ji takaici matuka dalili kuwa shi ne, akwai tausayi da kauna tsakanin malamai da dalibansu: malamai na iya kokarin su ganin sun koyar da yara kuma sun gane abinda aka koya musu. Amma abin takaicin koda zaka duba aji rabin ajin ba kowa, wasu na wurin kwallo, wasu na wurin shiririta, hakan ba zai hana malami ya koyar da wadanda suke cikin ajin ba, daga baya wani yazo ya ce malam bai sanar da mu ba, in dai har za mu yiwa malamai adalci basu da hannu wurin faduwar dalibi jarabawa.

  Hujja Ta 3

  Ka dauka daga matakin farko wato primary, malami zai shigo aji yana koyar da yara` amma yaran hankalin su baya wurinsa, tunanin su ma bai ko kai gare shi ba. Haka zai gama ya yi tambaya amma abin haushin a rasa yaro daya da zai tashi ya bada amsa, kuma abinda aka gama koya musu ne aka tambaye su tun kafin aje ga jarabawar da ake magana kanta, yaro ya kasa amsa tambaya bayan gama darasi ta ya za ka yi tunanin ya amsata yadda ake so, bayan wasu lokuta ina nufin idan anzo jarabawar. Sai kuma mu dauki laifin mu dora ma malamai bayan su suka fi kowa son yaran da suke koyarwa su fahimta.

  Hujja Ta Karshe

  Za ka shiga manyan makaranta kaga yarinya ta yi wata shiga kai kanka sai ka yi tunanin ba karatu ya kawo ta ba, uwa uba wasu dalibai basu san darajar malami ba, za Ka shigo aji ka sami yarinya nacin cingam wata na charting wata ma hira take malami na koyarwa amma wai a haka ake ganin malamai sune masu laifi, malami ne fa zai cewa dalibai, fita bar mini ajina, dan dalibi ya bata masa rai, maimakon dalibin ya bada hakuri sai kaga ya fita a ajin cikin isa da takama ya bugo kofar ajin kamar zai cireta. Ya zama dole mu san waye malami kafin mu yanke masa hukunci, ya zama dole mu san darajar malamai musan fa duk abinda suke dan mu suke yin shi.

  Daga Aseeya Muhammad, wakiliyar Al’umma Writers Association

Comments

1 comment