Rubutu

Blogs » Muhawarar Bakandamiya 2020 » Lalacewar tarbiyyar 'yan mata: Iyaye ko kawaye ne silar hakan?

Lalacewar tarbiyyar 'yan mata: Iyaye ko kawaye ne silar hakan?

 • Wannan muhawara ce karawa ta 9, inda zaratan wakilai daga ƙungiyoyin marubuta Hausa, Ana Tare Writers Association da kuma Writers Guild of Nigeria suka yi ambaliyar hujjoji domin kare matsayarsu a kan take mai cewa: Lalacewar tarbiyyar 'yan mata: Iyaye ko ƙawaye ne silar hakan?

  Muhawarar dai ta wakana ne a shafin MARUBUTA da ke manhajar BAKANDAMIYA a ranar 2 ga watan Disamba, 2020. Ga yadda muhawarar ta gudana.

  Assalamu Alaikum. Bayan gaisuwa irin ta addinin Musulunci. Ina miƙa gaisuwata ga masu girma alƙalai, masu girma jagororin wannan muhawarar, mai duba lokaci a kan kari, abokanan fafatawarmu a wannan gasar, ‘yan uwa masu bibiyar muhawara... Sunana Maryam Ahmad Paki daga ƙungiyar Ana Tare Writers Association. Ni ce zan goyi baya a kan cewa “Lalacewar Tarbiyyar yara mata ƙawaye ne sila ba iyaye ba.”

  Kafin in fara cewa komai a kan goyon bayana sai na ƙara jaddada cewa lalacewar tarbiyyar yaran mata ƙawaye ne sila bisa ga manyan hujjoji na masu zuwa:

  1. Hujja ta ɗaya

  Wace ce ƙawa? Ƙawa ita ce wacce kake samu a lokacin da ba ka yi tsammani ba, sannan shaƙuwa ta shiga a tsakaninta yadda za ka iya faɗa mata sirrinka saboda yarda da amana ka kuma rayuwa da ita. Bari in yi amfani da abin da bature yake cewa, “A friend in need is a friend indeed.”

  A wannan ƙayyade wace ce ƙawa da na yi ya sa ƙawaye suka zama ja gaba wajen rushe tarbiyyar yara mata bisa ga yadda matan ke shawara da su saboda yarda da ka yi da su da ɗaukar duk abin da za su faɗa maka. Wannan ya ba wa ƙawayen hanya suka yi amfani da wannan damar suke ɗora ‘yn mata akan tubali mara ɓullewa. Misali idan muka duba wasu ‘yan mata yadda suke ɗaukar shawarar ƙawayensu ba sa ɗaukar ta iyayensu. Yanzu sai iyaye su ɗauki lokaci suna yi wa yaransu faɗa ba za su ɗauka ba, amma da ƙawaye sun musu magana za su ɗauka.

  2. Hujja ta biyu

  Lokuta da dama ƙawaye sun fi kowa ba da gudummawa wajen lalacewar tarbiyya, saboda yadda suke mai da kamilallun 'yan mata zuwa ‘yan iska waɗanda za su addabi al'umma, za ku ga yarinya ta fito daga gidan mutunci da tarbiyya amma daga zaran ta haɗu da fitsararrun ƙawaye lokaci ɗaya za su rushe mata tarbiyyar da iyayenta suka yi shekara da shekaru suna ginawa a kan ɗiyarsu. Kamar yadda Hausawa suke cewa zama da maɗaukin kanwa shi ke kawo farin kai, ko da a farko halayen ƙawayen ba ya burge su, daga baya har su ma su fara ƙoƙarin kwaikwayon halin ƙawayen.

  Idan muka yi duba yanzu rayuwar ‘yan mata sun fi yin ta da ƙawayensu fiye da iyayensu, saboda zuwa makaranta da ake wuni a can.

  3. Hujja ta uku

  Ƙawaye su ne tsani na lalacewar tarbiyyar ‘yan mata duba da yadda suke koya wa ‘yan mata yaudarar samari, shaye-shaye, neman jinsi, bin maza da duk wata ɗabi'a mara kyau. Misali yanzu idan muka ɗauki ƙawaye masu shaye-shaye, idan suka ga yarinya mai kamun kai ce za su biyo mata ta dubara suna faɗa mata daɗin da ke cikin shaye-shayen da amfaninshi kafin su fara bijiro ma da 'yan matan nufin su a kan koya musu shaye-shayen.

  4. Hujjata ta huɗu

  Ƙawaye su suke ɗora ma wasu yara matan buri da son abin duniya ko da a farko ba su da ra'ayin haka. Misali ƙawa za ta fara siyan abu mai tsada kama daga suturu da kayan more rayuwa tana nuna ma ƙawarta ko tana turo mata a social media, tun ba ta sa abin a ran ta za ta fara tunanin hanyar da za ta bi ita ma ta zama kamar ƙawarta ko da kuwa iyayenta ba masu arziƙi ba ne saboda ita ma tana so a gan ta kamar ƙawarta. Wannan shi zai ja yarinya ta fara sa buri da kwaɗayi a ranta wanda shi zai taimaka wajen rushe tarbiyyarta da ta samo tun asali.

  Ko a nan na tsaya na san cewa alƙalai masu adalci za su yi duba da dalilaina tare da yarda da magana ta na cewa ƙawaye su ne silar lalacewar tarbiyyar yara mata ba iyaye ba.

  Na gode!

  Ni ce taku, Maryam Ahmad Paki daga Ana Tare Writers Association

   

  WRITERS GUILD OF NIGERIA

  Farko

  Abin Mamaki wai kurege da nuna wa zomo ƙanzo. In ban da abokan karawarmu da son jan magana ta ya ma za su ce laifin ƙawaye shi ne silar gurɓacewar tarbiyyar 'ya'ya mata, ai kowa ya san filin sukuwar ingarman doki ba na sukuwar gurgun jaka ba ne. Ƙawaye ba su da gurbi kan tarbiya, laifin na iyaye ne.

  Kun gan ni da zuba, duk cikin yadda nake ɗokin bayyana muku hujjojin da za su tabbatar muku laifin iyaye ne ke jawo gurɓatar tarbiyya har nake ƙoƙarin mantawa ban yi sallama ba.

  Shugabannin muhawara (Bakandamiya), alƙalan muhawara, mai duba lokaci, abokan karawarmu, gami da masu kallo Assalamu Alaikum. Sunana Fatima Aminu Ya'u wakiliyar ƙungiyar Writers Guild, da ke kare manufarmu da ke cewa, “Sakacin iyaye shi ke gurɓata tarbiyar 'ya'ya mata ba ƙawaye ba.”

  Kafin na cigaba, yana da kyau ƙwarai mu fara da sanin abin da ake nufi da tarbiyya, iyaye da kuma ƙawaye, hakan zai taimaka wajen fahimtar hujjojin nawa sosai.

  Da farko, tarbiyya na nufin tattali da kimtsa mutum, ya samu ingantacciyar rayuwa da ke ƙunshe da walwala, don zamtowa mai hankali da kuma samun ilimin iya kyakkyawar mu'amala da kowa.

  Iyaye kuwa su ne waɗanda suka haife mu, suka raine mu, gami da kulawa muka tashi da su, muka saba, halayenmu da ɗabi'unmu yakan kasance mafi tsoka nasu ne.

  Ƙawaye kuma ɗaya bangaren, wasu mutane ne da muke haɗuwa da su a wani lokaci na rayuwarmu.

  Kamar yadda na faɗa tun farko tabbas laifin na iyaye ne ba na ƙawaye ba saboda dalilaina kamar haka:

  Ya zo a hadisi cewa,

  Dukkanin ku (iyaye) makiyaya ne kuma za a tambaye ku kan abin da aka ba ku kiwon su ('ya'yenku)”.

  Idan har wannan shi ne abin da addini ya tanada a game da tarbiyyar yara, me zai hana mu ganin baiken waɗanda ke bugun ƙirjin cewa ba laifin iyaye ba ne lalacewar tarbiyyar 'ya'ya mata? Iyaye musamman uwa ita ce wadda muka shaƙu da ita, muka tashi muna gani, in har tun farko iyaye sun ja ɗiyarsu a jiki, sun tattala ta, uwa ta mai da ɗiyarta ƙawa, ta san duk wata damuwarta, ta zama abokiyar shawararta, shi ma uba ko da bai ja ɗiyarsa sosai a jiki ba, aƙalla bai zama tamkar dodo a gare ta ba, to tabbas babu ta inda ƙawa za ta samu dama cikin rayuwar yarinya bare har ta gurɓata ta, domin sai bango ya tsage kadangare ke samun wurin shiga.

  Sai dai kash! Iyaye da dama kan nuna ko in kula ga rayuwar ɗiyarsu, hakan ya sa ba su san komai a kan ta ba, rayuwar ta da komai ya ta'allaƙa a kan ta ne ita kaɗai, ita ke bai wa kanta shawara ta shawo kan matsalar ta da kanta, wanda ƙaramar kwalwalwa irin ta mace sai ta kai ta ga halaka.

  Inda iyaye sun ja ta a jiki, sun mai da komai nata nasu, to koma mene ne kafin ya yi nisa da kanta za ta faɗa musu. Da yawan iyaye zaton su sutura da abinci kawai ɗiya mace ke buƙata, yayin da wasu ma gabaki ɗaya riƙon sakainar kashi suke ma ɗiyarsu, ba su san ci ko shan ta ba, inda wannan abubuwan da suke kasa ba ta kansa ta faɗa wata hanyar, misali pad mun san dole ne ga 'ya mace, amma iyaye ba su damu da su bai wa ɗiyarsu ba, haka kayan kwalliya wata kan iya yin komai kamar sata ko ma zina don ta samu.

  Rufewa

  A iya saninmu iyaye ke sanya yarinyarsu a makaranta, ƙawaye ba sa taɓa iya cire ta, kazalika iyaye ke iya tura ɗiyarsu talla, ba ƙawaye ba, wanda makaranta hanya ce ta tarbiya mai kyau yayin da talla ce babba ta gurɓacewar tarbiyya. Kenan shakulatun ɓangaro da iyaye ke yi ga ɗiyarsu shi ke janyo lalacewar ta.

  Da waɗannan hujjojin nawa nake son ku yarda iyaye su ne tushiyar gyaruwa ko gurɓatar tarbiyar ‘ya’ya mata a kowacce al'umma.

  Na gode.

  Fatima Aminu Ya’u, wakiliyar ƙungiyar Writers Guild of Nigeria

Comments

2 comments