Rubutu

Blogs » Hira da Mutane » Ba yawan abu ne cigaba ba, nagartarsa ne abin dubawa-Bukar Mada

Ba yawan abu ne cigaba ba, nagartarsa ne abin dubawa-Bukar Mada

 • Barkanmu da sake haɗuwa a sabon shirin na mu na Baƙon Mako. A yau shirin na mu ya yi tattaki wajen zaƙulo muku wani fitacce kuma shahararren marubuci wato Malam Bukar Mada, wanda ya na ɗaya daga cikin waɗan da suka sabunta fassarar shahararren littafin nan mai suna Dare Dubu Da Ɗaya. Don jin wane ne shi da kuma nasarorin da ya samu a harkar rubutu sai ku kasance da mu masu gabatarwa Maryam Haruna da Hauwa'u Muhammad. 

  T1. Muna son jin takaitaccen tarihin bakonmu.

  Bukar Mada: Cikakken sunana shi ne, Abubakar Yusuf Mada. Bukar Mada lakani ne kurum da nake amfani da shi a soshiyal midiya da kuma rubuce-rubucena. An haife ni a garin Mada da ke karamar hukumar mulki ta Gusau a jihar Zamfara, a shekarar 1982. Na fara karatun Islamiya kafin na fara na zamani. Na yi karatun boko, tun daga matakin firamare har zuwa jami'a, inda na kware a fannin da ya shafi nazarin 'yan halitta masu amfani da masu yada cututtuka (Microbiology). Har yanzu ana cikin neman ilmi.

  Ina koyarwa a Kwalejin kimiyyar lafiya (College of Health Sciences and Technology) da ke garin Tsafe, a jihar Zamfara. Ina da aure da 'ya'ya. 

  T2. Me ya ba ka sha'awar fara rubutu?

  Bukar Mada: Na taso da sha'awar karance-karance tun a firamare, wannan ya sa mini sha'awar zama marubuci wata rana.

  T3. Wadanne irin kalubale ka fuskanta lokacin da ka fara rubutu?

  Bukar Mada: To, ni dai sabon marubuci ne, ba kamar yadda kuka yi ta kururutawa ba, wai shahararren marubuci. Don haka har zuwa yanzu babu wani kalubale da na fuskanta, idan ma har akwai shi, to bai wuce na rashin wadataccen lokacin da zan yi rubutun ba.  

  T4. Zuwa yanzu litattafai nawa ka rubuta, kuma wadannene?

  Bukar Mada: Yawancin rubutuna duk gajerun labarai ne. Gaskiya suna da yawa, sun kai hamsin ko sun fi, akwai wadanda na ci gasa da su. Kadan daga ciki su ne:

  1. Kaddara ta riga fata
  2. Sauyin rayuwa
  3. Sawun barawo
  4. Kabilanci
  5. Goje mai dawa
  6. Malam dudu
  7. Mahakurci mawadaci
  8. Kowa ya ki ji
  9. Fadar barci
  10. Hikayar Ali Baba

  Da saura da yawa

  A littafai kuma kammalalle, sai littafin Labarun Dare Dubu Da Daya da muka sabunta fassararsa tare da Danladi Haruna karkashin jagorancin Prof. Malumfashi. Littafin zai kai mujalladi 10, yanzu haka mujalladi na farko na kasuwa, na biyu zai shiga kasuwa daga yanzu zuwa kowane lokaci.

  Akwai kuma wasu littafan da nake rubutawa, Burgami da kuma Karkon Kifi.

  T5. Yanzu lokaci ya canja haka zalika al’umma da dama na mutane ya canja wanda na wasu ya ke zuwa a karkace ta kai yanzu rubutun littafin batsa abun so ne ga wasu mutanen. Shin wane kira zaka yiwa irin wadannan marubuta?

  Bukar Mada: Su ji tsoron Allah a dukkan rubutun da za su yi. Magana ma da mutum ke yi, akwai mala'ikun da ke rubuta ta su ajiye, to balle wanda ya rubuta da alkalaminsa, iyaka su yi copy and paste a cikin littafinsa. Kuma ko bayan mutum ya mutu duk wani rubutu da ya bari a duniya, har kuma rubutun nan ya yi sanadin saba wa Allah, to kuwa marubucin na da nasa kamasho da zai isko shi har cikin kabari. Haka kuma duk wanda ya yi rubutun da aka karanta aka yi amfani da shi ta hanyar da ya dace da addini, to yana da nasa kaso. Don haka marubuta su ji tsoron Allah, su san abin da za su rubuta.  

  T6. Ka samu nasarori da dama duba da irin littafan da kake yi irin wadanda mutane ba sa gajiya da karantawa ne, kuma suna daga cikin wadanda suka yi suna, kusan duk mai karatun litattafai na Hausa ya san su. Shin wadanne irin nasarori ne ka samu wajen rubutunka?

  Bukar Mada: Gaskiya ne, na samu nasarori da dama ta hanyar rubutu. Na hadu da manyan mutanen da ban yi zaton zan hadu da su ba. Na samu kyautuka da dama daga gasa daban-daban da na yi nasara. Mutane da dama sun san sunana kodayake ba su taba gani na ba. Kusan kullum sai na samu kiran waya daga mutane na jihohi daban-daban, suna kira ne kurum domin mu gaisa. Alhamdulillah, rubutu ya yi mini komai.

  T7. Rubutun online da wanda ake bugawa wanene ya fi tsari da ma'ana?

  Bukar Mada: Rubutun littafi ya fi tsari da ma'ana, saboda shi sai an ba wa wasu sun duba sun yi editing kafin a sake shi kasuwa. Amma na online ya fi yawan makaranta, amma kwamacala ta fi yawa a ciki.

  T8. Wasu mutanen suna tunanin cewa babu abin da rubutu ya ke jawowa sai æata tarbiyya shin wacce shawara ya kamata a dinga ba irin waæšan nan mutanen?

  Bukar Mada: Eh to, da ma wasu ke bata wasu. Watakila irin wadannan mutanen suna la'akari ne da irin littafan da ake rubutawa yanzu, wadanda mafi yawancinsu babu komai a ciki sai soyayya da batsa, ko ni ba zan goyi bayan a karanta su ba. Amma akwai littafai da dama wadanda ke koyar da abubuwa da yawa musamman tarbiya da zamantakewar yau da kullum, irin wadannan suna da matukar amfani wajen saita rayuwar al'umma.  

  T9. Shin ya kake ganin tafiyar adabin hausa? Ma'ana irin ci gaban da aka samu game da shi a yanzu?

  Bukar Mada: To, Adabin Hausa, musamman rubutataccen Adabi da muke magana a kai yanzu, zan iya cewa an samu ci gaba amma na mai hakon rijiya. Ci gaban kuwa shi ne, kullum garin Allah ya waye akan samu sabbin marubuta, akan kuma samu sabbin littafan da ke shiga kasuwa. Sai dai ba yawan abu ne ci gaba ba, nagartarsa shi ne abin dubawa. An ce da haihuwar yuyuyu gara da guda kwakkwara. Mafi yawancin marubuta yanzu ba su san ma me suke rubutawa ba, da yawa ba su kiyaye ka'idojin rubutu balle nahawun Hausa, maimakon a yi abin da dalibai za su yi nazari a makarantu, sai a yi abin da zai kara rikirkita su. Sannan littafan da ake rubutawa duka masu gajeren zango ne, idan littafi ya fito wannan shekara, da an shekara biyu ko uku, sai a neme shi a rasa, ya bata bat, wani lokaci har a wajen marubucin ba za a samu kwafi ba. Shi kuwa littafi tamkar wata ma'ajiya ce ta al'adun zamanin da aka...

  T10.  Shin kana da wani maigida da ya ke nuna maka harkokin rubutu?

  Bukar Mada: Eh, a'a. Na zama marubuci ta dalilin wata makaranta da Farfesa Ibrahim Malumfashi ya bude a facebook mai suna MAKARANTAR MALAM BAMBADIYA. Manufar bude makarantar kuwa shi ne domin samar da sabbin marubuta da kuma kara wa tsofaffin marubuta ilmi. To ina cikin sabbin marubutan da makarantar ta kyankyashe. Idan har ina da maigida a rubutu, zan iya cewa Prof. Malumfashi ne maigidana kuma Malamina.

  T11. Wace shawara za ka ba marubuta masu tasowa yanzu?

  Bukar Mada: Ni ma ai karamin marubuci ne. Shawarar da zan ba ire-irenmu shi ne, mu tsaya mu rubuta abin da zai amfani al'ummarmu, ya kuma amfane mu ko bayan ranmu. Sa'annan duk rubutun da za mu yi mu rika yin bincike a kan abin da ba mu sani ba kafin mu rubuta shi, ban da rubuta karya ko shaci fadi a cikin labari. Kodayaushe marubuci ya kasance shi ke juya akalar mai karatu, ba wai mai karatu ya kasance shi ke juya marubuci ba.

  Tsara tambayoyi da gabatarwa: Maryam Haruna tare da Hauwa'u Muhammad

Comments

0 comments