Rubutu

Blogs » Muhawarar Bakandamiya 2020 » Tsakanin neman kudi da neman ilimi wanne yafi muhimmanci?

Tsakanin neman kudi da neman ilimi wanne yafi muhimmanci?

 • A cikin jerin zazzafan muhawarar da kungiyoyin barubuta suka fafata a zauren Marubuta da ke Manhajar Bakandamiya, a yau zamu kawo muku karawa ta goma sha bakwai (K17) wadda ta wakana a ranar 10 ga watan Disamba, 2020. Inda wakilan kungiyoyin Haske Writers Association da Taurari Writers Association, suka fafata a bisa taken muhawara mai cewa: Tsakanin neman kuɗi da neman ilimi wanne yafi muhimmanci?

  Haske Writers Association

  Assalamu alaikum malaman muhawara, Alƙalai, abokai da masu kallo. Sunana khadijat Abdullahi Shehu, daga ƙungiyar HASKE WRITERS’ ASSOCIATION, na fito don na bayyana ra’ayi na akan cewa NEMAN KUƊI YAFI NEMAN ILIMI muhimmanci.

  Kuɗi sune abu na farko da ɗan’adam zai iya gina kowace irin rayuwa da yake son yi a cikin duniyarsa.

  A zamanin nan, daraja, ƙima, mutunci, faɗa aji, matsayi, girmamawa, kaffa-kafa, hatta zumunci sai kana da kuɗi kake samun su ga wani kadan daga taken kudi...

  Da ni ake iya tawaye, ana bin umarni saboda ni, ana ƙin gaskiya saboda ni, ana gudun ‘ƴan uwa idan aka sameni, ana sayen rigima saboda ni, babban abin al’ajabi shi ne yadda nake kaɗawa “SO” ƙararrawa, na karya farashinsa, sannan na mallakawa duk wadda ya same ni “ZUCIYA” Kuɗi ke nan, ilmi ba kuɗi! TARON NA AYYA GAYYAR...

  Hujja ta ɗaya: ALKHAIRI

  A TAYA ALLAH KIWO YAFI ALLAH NA NAN. Kuɗi suna taka muhimmiyar rawa wurin bawa mutum damar taimako, kamar su gina asibitoci, cibiyar bayar da magani kyauta, gina rijiyoyi da burtsatsai, sadaka, taimakawa marasa ƙarfi da gajiyayyu, gina masallatai da makarantun da ake ɗaukar ILMIN a cikin sa. Mai kuɗi na iya samun babban rabo tun a duniya, matuƙar ya yi aiki da su yadda ya dace. Mu ɗauki misali da sahabin manzon ALLAH (SAW) Abdurrahman bin Auf, dukiyarsa Ita ce tayi silar da ya samu aljanna tun a duniya, saɓanin mai ilmi, waɗanda yanzu suke fama da ci da addini, damfara, ci da ceto, riya da sauran su.  

  Hujja ta biyu: SAMAR DA AIKIN YI

  DOLE NE, CIN KASUWA DA MAƘIYI.

  Kuɗi suna taimakawa sosai gurin samar da aikin yi ga matasan. Misali idan wani attajiri ko mai hannu da shuni ya gina masana’anta ko wani kamfani sannan ya ɗauki mutanen dake kewaye cikin wannan yankin aiki, ya taimakawa mutane kuma ya taimakawa gwamnati domin za a rage yawan masu zaman banza, kuma miyagun laifuka zasu ragu irinsu sace-sace, ƙwace, garkuwa da mutane da sauran su. Har ila yau, komai ilmin mutum idan bashi da kuɗi zaka same shi ƙarƙashin wani attajiri ya ke, ba dai ka ga attajiri ƙarƙashin mai ilmi ba. 

   

  Hujja ta uku: INGANTACCEN ILMI

  FANKAM FANKAM BATA KILISHI.

  Kuɗi kan taka muhimmiyar rawa wajen samun ingantaccen ilmi ga yaran mu, idan ka yi la’akari da zamanin yanzu, yara da yawa na zaune a gida, saboda iyayen su ba su da kuɗin da zasu ɗauki nauyin karatun na su. Sai ka ga komai ƙoƙarin yaro an dakushe shi. Misali yanzu da gwamnati ba ta biya ma yara jarabawar neco da waec, zaka samu da yawa ta wannan hanyar karatun su ya tsaya saboda iyayen ba zasu iya biyan kuɗin ba. Wasu kuma masu kuɗin ne ke taimakon su, ga maganar makarantun gaba da sakandiri zaka samu ƴaƴan masu kuɗi ne, ba talaka ba. Wasu ma ko sun fara daga ƙarshe dole su datse.

  Sannan ko tunanin yaro da nagartar sa, tana tafiya ne dai dai da ingantacciyar rayuwar da ya samu. Haka ƙoƙarin sa na tafiya da irin kulawa da abincin da yake samu, kun ga ko anan an bar ɗan talaka a baya, wani ɗan talaka zai ta fi makaranta a yunwace, ga dauɗa, da kuma tunanin abubuwa barkatai a zuciyar sa. Saɓanin ɗan mai kuɗi da duk babu waɗannan, kuma hakan ke bashi damar yayi karatu cikin natsuwa.

   

  Hujja ta hudu:  LAFIYA

   Sau tari za ka shiga asibiti ka tarar da talakawa cikin mawuyacin hali, babu kuɗin magani, ga wanda ma aka kawo asibitin kenan, wasu ma saboda rashin kuɗi sai dai su matu a gida. Wasu kuma ciwon yunwa ke yin ajalin su saboda halin babu Saɓanin mai kuɗi da ke samun ingantacciyar kulawa a gida da asibiti

  Wannan kaɗan ne daga cikin alfanun kuɗi. A wannan lokacin kowa yasan yadda zai yi ya tashi ya nemi kuɗi, bawai ilimin ake fita nema ba. Malamai da Alƙalai harma da masu kallo nasan zasu yadda da wannan ɗan taƙaitaccen bayanin nawa. Idan ka nemi kuɗi a wannan zamani, to samun ilimi ba zai maka wahala ba. Na barku lafiya.  

  Khadijat Abdullahi Shehu daga kungiyar Haske Writers Association

  Taurari Writers Association ba su samu damar kawo hujjojinsu ba.

  Mu tara a muhawara ta gaba.

Comments

1 comment