Rubutu

Blogs » Muhawarar Bakandamiya 2020 » Yawan mace-macen aure: Rashin hakuri ko rashin tarbiya

Yawan mace-macen aure: Rashin hakuri ko rashin tarbiya

 • Barkanmu da sake kasancewa a wannan kafa da muke kawo muku jerin muhawararori da kungiyoyin marubuta Hausa suka fafata a zauren Marubuta da ke Manhajar Bakandamiya. Kungiyoyin sun baje hujjoji masu kare ra’ayinsu a kan batutuwa da suka shafi rayuwarmu ta yau da kullum. A yau zamu kawo muku  karawa ta goma sha takwas (K18) ne. Wannan karawa ta wakana ne a ranar 10 ga watan Disamba, 2020 Miladiyya. Karawa ce a kan taken: “Me ke janyo yawan mace-macen aure tsakanin rashin haƙuri da rashin tarbiya?” Zaƙaƙuran ƙungiyoyin marubuta na Potiskum Writers Association da kuma Dutse Writers Association ne suka yi wannan karawa. A biyo mu cikin muhawarar domin ganin yadda muhawarar ta wakana.

  Potiskum Writers Association

  Cike da girmamawa nake miƙa gaisuwata ga alƙalan gasa, mahukunta, mai duba lokaci, abokan gwabzawar mu da kuma masu kallo. Fatan mun wuni lafiya.

  Hujja ta farko

  Dariya ce fal bakina ganin cewa tsagin da na rika shi ne dahir sabanin wanda abokan karawar mu suka rika wato rashin gaskiya a matsayin sababin yawaitar mutuwar aure. Yo in banda abin su har yaushe ma za a ce mana rashin hakuri ke kawo mutuwar aure ba matsalar rashin tarbiyya ba? Na san ‘yan kallo da alkalai idanuwanku a bude suke idan na abokin karawata sun rufe. Na san masu girma alkalai da masu biye da mu a filin wannan muhawara duk kuna da masaniyar yadda matsalar rashin tarbiyya ta zama babbar damuwar al’ummar mu a yau, musamman wadanda suka kasance iyaye daga cikin mu za su fi saurin harbo inda jirgin nawa ya nufa bisa fadar hakan da na yi.

  Hujja ta biyu

  Mun dade da sanin cewa siffar mutum ba ta bayyana hakikanin halinsa wanda hakan yasa a dan gajeren lokacin da muke dauka tare da wadanda a karshe suke zama abokan rayuwarmu na aure karancin lokaci kan sa mu gaza fahimtar dukkan dabi’un su dari bisa dari kafin lokacin auren mu da su har sai bayan an daura. Bugu da kari kuma a yanzu muna wani zamani ne da yaudara ta zama ado wanda hakan ke sa wadanda muke so kan boye mana wasu dabi’un nasu har sai bayan anyi aure kafin muke kai ga gano su. Wato dai sukan kasance a gare mu tamkar kura ne a cikin fatar tinkiya, irin abin da Hausawa ke cewa, “Fir’auna a zuci, Musa a baki” idan irin hakan ta faru kuwa, to fa babu abin da zai dakatar da aure daga mutuwa domin tun daga tubalin da aka yi ginin auren daman tun farko an samu algus a ciki.

  Hujja ta uku

  Na san babu mai musa ni idan nace daku, iyaye ne ke taka rawa wajen samar da tarbiyyar ‘ya’yan da za su haifa ko ma dai a ce yaran kwaikwayo da kuma gadon irin dabi’un iyayen nasu za su yi. Masu girma alkalai shin me kuke tunanin zai faru idan kamilin miji ya gano cewa munin rashin tarbiyyar matar shi ya zarce kalaman cin mutunci da yi masa laluben aljihu tana hadawa har ma da shaye-shaye da bin maza a boye? Me kuma kuke tunanin kamilar mace za tayi idan ta gano cewa mijin da ta aura take kuma sa ran zai zama silar za su hadu wajen samar da zuria ta gari tantarin marar tarbiyya ne kuma ma’abocin aikata haramtattun abubuwa da addini ba ya so? Tabbas na san amsar ku ita ce batun rabuwa ne zai shigo. 

  Hujja ta hudu

  Rashin tarbiyya a na iya cewa shi ne a sahun gaba cikin abubuwan da suke bada gudumawa wajen mutuwar aure a wannan zamani duba da yadda tayi karanci. Domin tarbiyya wata jigo ce dake dora mutum bisa turbar da zai iya bambance abu mai kyau da marar kyau. Ta hanyar tarbiyya ce ake sanin fari da baki don hatta shi kan shi hakurin tarbiyyantar da mutum ake a dora shi akan sa. Idan aka rasa tarbiyya to kuma a nan ne matsalar rushewar aure yake zuwa. 

  MUSADDAM daga kungiyar Potiskum Writers Association.

  Dutse Writers Association ba su samu daman kawo hujjojinsu ba

  Mu hadu a muhawara ta gama.

Comments

2 comments