Rubutu

Blogs » Hira da Mutane » Kamala Minna ya bayyana kalubalen da ya fuskanta a fagen rubutu

Kamala Minna ya bayyana kalubalen da ya fuskanta a fagen rubutu

 • Assalamu alaikum. Barkanmu da sake kasancewa a wannan fili na Bakonmu na Mako wanda ni Hauwa’u Muhammad tare da Maryam Haruna muka saba tattaunawa da hazikan marubuta, manazarta da mawaka don jin tarihinsu da irin hobbasar da suke yi wajen cigaban Adabi. Yau za mu tattauna da marubuci Kamal Muhammad Lawal, wanda aka fi sani da Kamala Minna. Ku biyomu cikin shirin.

  T1. Muna son jin takaitaccen tarihin bakonmu

  Kamala Minna: Assalamu alaikum. Ina yiwa al'umman wannan zaure barka da wannan lokaci tare da fatan alheri. Ina godiya da wannan gayyata da aka min a wannan zaure. Da farko dai Sunana Kamal Muhammad Lawal wanda aka fi sani da Kamala Minna. Ni haifaffen garin Gwada ne a yankin karamar hukumar Shiroro a Jahar Neja Minna.

  T2. Me ya ja ra'aayinka har ka fara harkar rubutu?

  Kamala Minna: Eh to da farko dai harkar rubutu zan iya cewa tsintar kai na yi a cikinta a matsayin baiwa. Don tun kafin na san wani abu Adabi a harshen hausa na kasance mai kaunatar rubuce-rubuce irin su ƙirkira.

  T3. Ka taba fuskantar kalubale a harkar rubutu?

  Kamala Minna: Kalubale ai wannan dole ga duk mai rai in dai yana cikin harkoki da zai haɗa mutane. Da farko dai ban fuskanci kalubale a harkar rubutu ba illa rashin daidaituwar Hausa da kuma wasu kalmomin Hausa da ban iya faɗin su ba. Kasancewa na tashi a yankin da Hausa ba ta yi girman da za ka iya a saukaƙe ba. Wannan kenan.

  Ƙalubalen da zan iya kallo a matsayin kalubale a harkar rubutu shi ne yadda a lokacin da na fito duniya ta san ina na dosa na fara cin karo da wasu abubuwa cikin dangi da kuma abokai akan na ɗauki sahun da bai da wata muhimmanci a rayuwata har ta kai ta kawo ana min kallon mutumin da yake kokarin canza rayuwa zuwa ta rashin tarbiyya da sanin ya kamata. Sannan kuma na bi sahun mutane na karya wanda ba su da aikin yi sai kokarin dulmiyar da mutane zuwa koyan rashin kunya da fitsara. Abu na gaba da na iya faɗin sa a abu mafi ciwo na kalubale har zuwa wannan lokaci shi ne yadda aka juyar min da tunanin wasu makusantana akan cewa abinda nake yi tamkar saɓon Allah ne kuma na kauce hanya.

  T4. Wadanne irin nasarori ka samu a harkar rubutu?

  Kamala Minna: Masha Allah nsarori kam ko yanzu na bar harkar rubutu ba abinda zan ce sai Masha Allah. Don nasarori kam na same su kuma ina kan samun su.

  T5. Wane jigo ka fi maida hankali a kai wajen yin rubutunka?

  Kamala Minna: Na fi maida hankali a jigon zamantakewa da matsalolin rayuwa.

  T6. Ka taba halartar taron marubuta?

  Kamala Minna: Eh na ziyarci taron marubuta da dama, musamman taron karshen wata da ake yi irin su HAF da ANA.

  T7. A wace shekara ka fara yin rubutu?

  Kamala Minna: Gaskiya ba zan iya cewa ga shekarar da na tsinci kaina a harkar ba, amma dai shekarar da na shigo harkar rubutu sosai aka sanni 2011 ce.

  T8. Kana da ubangida a harkar rubutu?

  Kamala Minna: Bani da ubangida a harkar rubutu.

  T9. Menene burinka a duniyar rubutu?

  Kamala Minna: Burina a duniyar rubutu shi ne ko bayan na mutu ya kasance rubuce-rubuce na ba su mutu ba, al'umma na amfanuwa da su.

  T10. Shin ka taba buga littafin da ya fita kasuwa?

  Kamala Minna: Eh na taɓa fidda littafi guda mai suna 'Abin Sirri Ne' wanda ya fita kasuwa a shekarar 2017.

  T11. Wace irin gudummawa za ka bawa marubuta masu tasowa idan ka samu dama?

  Kamala Minna: In na samu dama ya kasance duniyar rubutu ta kasance ta musamman ga al'umma, sannan ko mi za a yi ace duniyar rubutu tana kan gaba wajan cigaban al'umma da wayar musu da kawuna akan duk wasu matsaloli da kalubalen rayuwa.

  T13. A matsayinka na maruci wace hanya kake ganin za a bi wajen dakile rubutun batsa da ya zama ruwan dare a yanzu?

  Kamala Minna: Maganar gaskiya a yadda ake ciki a yanzu yadda rubutun media ya kasance wani takomashi ga makaranta, abu ne mai girma ace za a samu yadda ake so har a daƙile rubutun batsa. Saboda yawancin marubutan batsa din ba sanin su muke ba iyakar mu da su media; ba ziyartar tarurruaka suke ba bare a kalubalance su a nuna musu hanya da ya kamata ace su gyara.

  Amma dai an ce mai rai ba a rasa shi da motsi ni dai a hasashena kauracewa karance-karance rubutun batsar daga masu karatu wannan hanyar in dai aka bi za a samu raguwar rubutun batsar. In har marubutan suka ga ba a karantawa dole za su canza salo, su dawo alkiblar da ake so su gane nan ne daidai. Amma in har marubutar batsa za su cigaba da rubutu masu karatu na karantawa bana tunanin za a samu sassauci.

  T14. Kana cikin wata kungiya ne ta marubuta?

  Kamala Minna: Eh ina cikin kungiyar Zamani Writers ta nan online.

  T15. A cikin rubuce-rubucenka wanne ne bakandamiyarka?

  Kamala Minna: Ni duk rubuce-rubucena ina son su kuma zan iya kiransu bakandamiya ta, amma dai zan iya cewa Uku Bala'i shi ne zan iya cewa ya zama bakandamiya kamar yadda makaranta suke fi raja'a akan sa.

  Tsara tambayoyi da gabatarwa: Hauwa'u Muhammad tare da Maryam Haruna.

Comments

0 comments