Rubutu

Blogs » Muhawarar Bakandamiya 2020 » Tsakanin tsaro da kiwon lafiya wanne yafi muhimmanci ga al’umma

Tsakanin tsaro da kiwon lafiya wanne yafi muhimmanci ga al’umma

 • A ranar 12 ga watan Disamba, a gasar Muhawarar Bakandamiya 2020 da aka gabatar a Zauren Marubuta, kungiyar marubuta ta Zaman Amana Writers Association ta kalubalanci kungiyar Rumbilhak Writers Association akan maudu’i mai taken: Tsakanin Tsaro Da Kiwon Lafiya Wanne Yafi Muhimmanci Ga Al’umma?

  Ga yadda muhawarar ta kaya:

  Zaman Amana Writers Association

  Shuwagabannin gasa, alƙalai, masu duba lokaci, ƴan uwa abokan muhawara, masu kallo, Allah nake roƙo ya azurtaku da amincinsa da yardarsa.

  Aisha Saeed shi ne sunana, wakiliyar ZAMAN AMANA WRITERS' ASSOCIATION da take tsaye ƙyam ganin ta kawo gamsassun hujjojinta akan cewa "SAMAR DA ABABEN KIWON LAFIYA YA FI MUHIMMANCI GA AL'UMMA AKAN TSARO". To ina ma da haɗi?

  Ai lafiya ita ce dar, komai mutum zai yi a duniya tabbas sai yana da lafiya zai yi shi.

  Kafin nace komai bari na tambayeku masu sauraro, shin kunko san muhimmanci na lafiya ga al'umma kuwa? Kunsan ma shin menene lafiyar? 

  To lafiya itace ginshiƙin jiki da ruhi, wadda sai da ita mutum yake sanin wanene shi.

  Masu bada tsaron kansu da muke taƙama dasu ai sai suna da lafiya ne zasu ba mu tsaro. Ke nan shi kansa tsaron sai mutum nada isasshiyar lafiya sannan zai iya bada shi.

  A komai na rayuwar ɗan adam lafiya ita ce farko, domin ita ce garkuwar rayuwa. Na tabbata masu sauraro zaku yarda dani idan kuka ji hujjojin da zan bayar kamar haka:

  Hujja ta farko

  Babban tsaro ga rayuwar talaka ko me kuɗi shi ne ka tsare masa lafiyar sa, saboda itace ginshiƙinsa, sai da itane zai iya aiwatar da dukkan mu'amalarsa, shi yasa ya zama tilas a tanadi kayan aikin kiwon lafiya, domin ginshiƙin al'umma.

  Mene amfanin su kansu masu tsaron? Ai amfaninsu shi ne tsare lafiyar d'an adam.

  Duk sojoji ko ƴan sanda babban muhimmin aikinsu shi ne bada tsaro ga lafiya da  dukiya da kuma rayuwar al'umma.

  Shi yasa samar da ababen kiwon lafiya yake da matuƙar muhimmanci ga al'umma fiye da tsaro. To ai dama guntun goro yafi babban dutse...

  Hujja ta biyu

  Ina da ja akan cewa bada tsaro yafi kiwon lafiya muhimmanci gaskiya, ai babu ma haɗi sam. Wannan shi ake kira da sama ta yiwa yaro nisa...

  Ai mai lafiya ɗangata ne ko babu tsaro zai iya bawa kansa kulawa da iyalinsa, babu taimakon soja ko ɗan sanda, amma wallahi idan bai da lafiya rayuwarsa gaba ɗayanta tana cikin tashin hankali, haka Kuma ta iyalansa. Shi yasa ma wani mawaƙi ya ce "lafiya uwar jiki..."

  Saboda muhimmanci na lafiya a sojojin ma akwai likitoci, haka kuma a ƴan sanda, da zarar wani abu ya samu a gaggauta basu kulawa ta ɓangaren lafiyarsu. Wannan kaɗai ya isa mutum ya gane su kansu masu bada tsaro da lafiya suke taƙama.

  Hujja ta uku

   Illolin da rashin samar da ababan kiwon lafiya suke haifarwa na da matuƙar yawan gaske, ta yadda hakan ka jawo sanadiyyar wasu su rasa rayukansu, wasu abubuwan sai ace se an fita ƙasar waje, wanda da yawan al'ummar talakawa ne. Sedai mutum yana ji yana gani ya rasa wani ɓangare na jikinsa ko ma rayuwar baki ɗaya.

  Duk tashin hankalin da al'ummar da suka rasa tsaro suka shiga babban tunaninsu tsira da lafiyarsu, haka Kuma duk tsananin da mutum ya shiga na rashin tsaro yana ƙoƙarine ya kuɓutar da rayuwar sa da lafiyarsa.

  Hujja ta hudu

  Mene yake kawo gudun hijira? rashin tsaro. Amma sunan gudun hijira shine gudu domin tsira da rayuwa da lafiya

  Mazaje na had'a iyalensu suna bin jeji saboda su tsira da lafiyarsu.

  Duk tsananin talauci iyaye na iyakar k'ok'ari gun samar da lafiya ga yaransu, haka gwamnati.

  Shi yasa nake amfani da wannan damar nake kira ga gwamnatinmu, da ta taimaka ta samar mana ababan kiwon lafiya domin tsira da rayukanmu, base ance aje wata ƙasar ba, wannan ma ci gabanmu ne da na ƙasa baki ɗaya.

  Da waɗannan hujjojin nake so shuwagabannin gasa su amince cewa samar da ababan kiwon lafiya yafi tsaro muhimmanci ga al'umma.

  Assalamu alaikum wa rahmatullah!

  A’isha Saeed daga kungiyar Zaman Amana Writers Association

  Masu muhawara ta gaba ba su samu damar gabatar da ta su ba.

  Mu hadu a muhawara karawa ta Ashirin.

Comments

0 comments