Rubutu

Blogs » Muhawarar Bakandamiya 2020 » Me ke janyo ta’addanci tsakanin jahilci da talauci da zalunci?

Me ke janyo ta’addanci tsakanin jahilci da talauci da zalunci?

 • A cikin jerin zazzafan muhawarar da shafin Bakandamiya suka gudanar a tsakanin kungiyoyin marubuta, a wannan rubutu za mu kawo muku fafatawar karawa ta ashirin (K20) wadda ta wakana a ranar 12 ga watan Disamba, 2020, inda wakilan kungiyoyin Strong Pen Writers Association da Nguru Writers Association suka fafata a bisa taken muhawara mai cewa: Me ke janyo ta’addanciaan tsakanin jahilci da talauci da zalunci?

  Ga yadda muhawarar ta kaya daga alkalamin wakilansu:

  Strong Pen Writers Association

  Shugaban mahawara, Alkalan wasa,mai girma mai duba lokaci, abokan mahawara, masu saurare barkanku da wannan lokaci mai tarin albarka da dimbin daraja, Assalamu alaikum.

  Na tsaya agaban ku cike da kwarin guiwa ta dan in jaddada maku cewa zalunci jahillci suke kawo ta’addanci a cikin al’umma, saboda manyan dalilaina kamar haka.

  Hujja ta farko

  Dalilin da yasa nace jahillci shi ke kawo ta’addanci a cikin al’umma, saboda daga inda aka ce al’umma ta rasa ilimi to tabbas wannan al’ummar ta gurɓata ba wani jindadi da zai wanzu a cikin wannan al’ummar saboda bata da ilimin da zata yi amfani dashi dan gyara al’umma akan tafarki mai kyau, jahillci yana da illoli da dama da suke zama barazana a wajen al’umma baki ɗaya tun daga matasa, dattawa da sauran al’umma baki ɗaya.

  Ya Shugaban mahawara rashin ilimi yana kawo rashin aikimji da al’umma zasu dogara da kansu dan cigaban kansu da kansu idan akwai ilimi tabbas za’a yaƙi jahilla wanda hakan ba zai yuyuba saita hanyar neman ilimi. 

  Hujja ta biyu

  Ya Shugaban mahawara, hujja ta ta gaba zata yi magana akan rashin ilimi duk al’ummar da aka ce basu da ilimi tabbas sun yi babban rashin ta hanyar ilimi ne kaɗai za a samu ingantacciyar rayuwa a cikin al’umma saboda ko ta hanyar neman ilimin zamani kaɗai zaisa al’umma su daina zaman banza a cikin gari saboda ta hanyar zaman banza kaɗai zai sa matasa su afka harkar shaye shaye, da dabanci duk rashin ilimi shi ke kawo waɗannan abubuwan dan duk mai ilimi ba zai kasance jahili ba sannan da ilimi za a samu ingantacciyar rayuwa mai amfani idan har akwai ilimi za a samu aiyukan yi ga matasa duk al’ummar da ta samu tsabtataccen ilimi lallai wannan al’ummar ta gyaru.

  Hujja ta uku

  Kamar yadda na yi bayani akan rashin ilimi a baya yanzun zan taɓo amfanin ilimi da nasarorin dake ta’allake da neman ilimi, idan aka samu al’umma mai neman ilimi tabbas wannan al’ummar zata fita daga cikin dauɗa ta jahillci dan shi jahillci ba abinda bai sawa rashin aiki da ilimi shi ke sa matashi ya zama mai shaye shaye, bin matan banza yawan caca sata dan idan mutum nada ilimi zai dinga aiki dashi sannan zai kiyaye duk abinda baida kyau wanda zai iya afakar dashi a cikin danasani na rayuwa idan matashi nada ilimi zai samu abin yi cikin sauki kuma zai samu ingantattar rayuwa mai albarka

   

  Ya shugaban mahawara zanso in tambayi abokan mahawara ta shin basu san cewa rashin ilimi shi ne hassada matsalaloli a cikin al’umma ba daga inda aka ce ba ilimi a cikin al’umma aikin jahilcci zai tabbata a cikin wannan alummar da matasan dake cikin al’ummar. 

  Hujja ta hudu

  Ya Shugaban mahawara, ina da wata ƴar tambaya da zan yi maka, ina so in san cewa me ke jawo gurɓacewar tarbiya a cikin al’umma?

  Yadda naga ka yi murmushi hakan kaɗai ya tabbatar min dacewa badan baka da abin cewa ba sai dai dan kasan amsar da zan bayar kaɗai zai wadatar da tambayar da na yi maka.

  Ba abinda ke gurɓata tarbiya illa rashin ilimi duk al’ummar da bata neman ilimi sannan bata aiki dashi bako shakka za a samu zalunci mai yawa a cikin rayuwa sannan wannan al’ummar ba zata jikan junan su ba balle har su yima iyayensu ɗa’a

  Sannan rashin ilimi ko ince jahillci ko kuma nace zulinci shike sa matasa na faɗawa a halaka inda sunada ilimin bazasu dinga zaman banza ba, wanda hakan zai sa su dinga shaye shaye, da sata ko fashi da makami ba, da wannan hujjar zance kuga aikin jahillci ba abinda bai sawa a cikin al’umma.

  Hujja ta biyar

  Ya Shugaban mahawara ina san inyi amfani da wannan damar dan yima abokan mahawara ta wata ƴar tambaya taƙaitatta.

  Shin zanso abokan mahawarata su gaya mini rashin aikin yi na matasa me yake kawo shi? Jin shirun ku kaɗai ya tabbatar min da cewa ba ku da abincewa kenan toh ni zan baku ansar da kuka faskara faɗa mani.

  Da ace matasa zasu samu ilimi da ba zasu gaza samun aikin yi ba idan ilimin zamani suka nema ta hanyar shi ne zasu samu aikin yi na gwamnati ko kuma aikin yi na aikin kamfani waɗan nan bazasu samu ba saida ilimi kuma wannan ilimin shi ke korar zulinci da kuma jahillci, dan jahillci shi ke kawo ta’addanci mai ilimi ba zai ɓata lokacin shi ba akan ta’addanci saboda yana da abin yi da wannan hujjar zan sanar da abokan mahawara ta illar rashin aikin yi a cikin al’umma. 

  Hujja ta shida

  Shin ko abokan mahawara sun san cewa jahillci shi ke kawo da na sani duk inda zalinci yake zaku ga al’ummar wajen suna cin zarafin junan su, zasu dinga haiƙewa matan su wadanda ba maharraman su ba, sannan za su dinga addini ba a cikin tsari ba, ko Allah SWT ya ce ku bauta mani amman sai kun nemi ilimi taya za’ai mutun ya bautama ubangijin shi ba tare da ilimi ba kunga kenan jahillci ciwo ne a cikin zukatan al’umma kuma sannan yana tareda aikin da nasani wanda hakan zai kai mutun ga afkawa cikin ta’addanci na fashi da makami ko kuma shaye shaye da sauran su da waɗan nan hujjojin nawa zan ɗan taƙaita badan banda abin cewa ba ko hujjojina sun kare, aaa sai dan duba da lokaci na harararmu, da fatan shugaban mahawara da alkalan wasa zasu dubi hujjojina, na gode da lokacin ku mai amfani da daraja, ku huta lafiya.

  Abdul Alhaji Musa daga kungiyar Strong Pen Writers Association.

   

  Nguru Writers Association

  Jahilci da Talauci ne kan Jawo Ta’addanci a Cikin Al’umma.

  Masu girma shugabannin muhawara, alkalai, abokan fafatawa da sauran masu bibiyar mu, assalamu alaikum.

  “Jahilci mugun ciwo!”. Wannan magana haka take ba ja, wai kare ya mutu a saura.

  Dukkanin wata al’umma da aka ga ta ci gaba, ta yaki talauci kai har ma da zalunci, to sai da ta fara yakar jahilci kafin ta ci nasara. Wannan abu kuwa, tabbatacce ne koda kuwa a addinan da ke doron Kasa ne.

  Da yake shi ne addinin da Allah ya aiko tsakanin al’ummar Manzon Allah S.A.W kai har ma da al’ummomin da suka shude gabaninsa, jahilci suka fara yaka.

  A duk lokacin da ake maganar an yaki jahilci, to fa sai an ga lalle an tabbatar da ilimi. Domin da shi ne sinadarin da yake warkar da wancan baki tabo da jahilci ya kakaba a tsakanin al’umma. 

  Talauci kuwa, na daga cikkn abin da yake kassara kowace irin al’umma, hakan sai ya kakaba wa wannan al’umma wani mawuyacin halin da karshe al’ummar za ta zagwanye ta lalace har ma ta kai ga ta rasa tudun dafawa.

  Wannan ya sanya, duk kasar da ake son karyawa, to sai a sanya mata takunkumin yalwar arziki ta yadda talauci zai mamaye gurbin arzikin ta, karshe fitintinu da tashe-tashen hankula su maye gurbin ni’ima da wadatar da take da su a baya.

  Masu girma alkalai, shugabanni da masu bibiyarmu, na san za su yarda da ni kan abubuwan da zan zayyano a matsayin hujjar da take tabbatar da cewa ‘Talauci da jahilci ne sababin samuwar ta’addanci a cikin al’umma’.

  Hujja ta farko

  Duk wanda ya bibiyi al’amuran rikicin Boko Haram a jihohin Borno da Yobe, inda nan ne matsira ta wannan rikici, zai ga cewa talauci ne ya karfafi rikicin, yayin da jahilci ya zama tushen rikincin.

  Misali a nan, lokacin da BH ke mamayar mutane, sun yi amfani da bakin talaucin da mutanen yankin ke ciki, su bai wa matashi kudi da bindiga, shi kuma sai ya aikata abin da suka sanya shi na kisan kai ga wanda suke so a kashe, wanin ma ba BH ba ne, amma sai a ce su ne. Abin nufi dai, talauci ne ya sanya shi aikata wannan ta’addanci.

  Hujja ta biyu

  Talauci ya jefa mutane da dama cikin ayyukan fashi da makami, wannan ta sanya idan ‘yan fashi suka shiga gidajen mutane za ka ji suna cewa, su ma ba a son ransu suke yi ba; ba su da aikin yi ne! Rashin aikin yi kuwa, shi ke kawo hauhawar talauci a tsakanin al’umma.

  Hujja ta uku

  Duk wanda ke bibiyar al’amarin garkuwa da mutane, zai tarar mafi yawan wadanda ke yi, musamman na kasa-kasa, talakawa ne da talauci ya sanya su shiga harkar, duk da wannan din ba zai zama uziri ba a gaban Allah. Amma dai talauci da jahilci ne suka jefa su harkar, yayin da su kuma suka zama sababin jefa dubban al’umma cikin yanayi na rashin kwanciyar hankali.

  Hujja ta hudu

  Idan aka bibiyi rikice-rikicen da suke wakana tsakanin ma’aurata wanda har ake karkarewa a gaban alkali, da yawa sababin sa talauci ne, wannan sai ya sanya miji ya kasa ciyar da matarsa, karshe rikici ya shiga tsakaninsu.

  Hujja ta biyar

  Kowa ya san yadda ake amfani da sassan jikin mutane domin a yi kudi kamar yadda bokaye ke sa wa a yi. Wannan ya jefa al’umma cikin rudani, ta yadda hankalin mutum ba zai kwanta ba a yayin da ya yi dare, ko kuma ma ya ki bin wasu hanyoyi domin ta’addancin da yake tsoro za a yi masa.

  Hujja ta shida

  Yawaitar sace-sace wanda su ma bangare ne daga cikin ta’addanci, da yawan su idan aka bibiya za a ga talauci ne sababi.

  Hujja ta bakwai

  ‘Yan matan da suke zinace-zinace a yau, za a iske talauci ne da yawan su yake sanya su, wanda ita kuma zina kan haifar da lalacewar al’umma; ta zama sababin samuwar gurbatattun da kila su zama jagororin al’umma, karshe su jefa bala’i a cikin al’umma, wanda wannan kam addini ma ya tabbatar da hakan.

  Hujja ta takwas

  Talauci ya raba ‘ya’ya da iyayensu, ya sanya uba ya sayar da d’ansa! Uba ya aurar da ‘yarsa ga mai dukiya wai duk domin ya guji talauci. Hakan sai ya haifar da wata sabuwar fitina ga uban ko kuma ‘yar. Uba kan iya bayar da jinin dansa ko ‘yarsa a wurin matsafa domin ya fita daga talauci. Wannan ma babbar fitina ce da ta’addanci a cikin al’umma.

  Hujja ta tara

  Da mai tambaya zai tambayi ‘yan daba masu sare-sare da fadace-fadace game sa sababin abin da ya jefa su hakan, za su ba da amsa da cewa ralauci ne.

  Hujja ta goma

  Yan bangar siyasa wadanda ake yawo da su kwararo-kwararo, ba wanka bare ibada, duk wadannan talauci ne ya zame musu tsani, wanda kuma har kawo lokacin da suke wannan gararamba, ba su fita daga talaucin ba, sai dai ma kara sanya su da ya yi a cikin wani sabon ta’addanci. 

  Hujja ta sha-daya

  A tau, za ka ga yara kanana suna sace-sace, talauci ne ya sanya su hakan, wansa karshe za ka iske sun zama manyan ‘yan ta’adda.

  Hujja ta sha-biyu

  Talauci kan sa namiji ya nemi namiji, mace ta nemi mace, ko ma a yi tarayya da dabba, wannan wannan ma babbar fitina ce da zmtake haifar da tashin hankali a cikin al’umma.

  Hujja ta sha-uku

  Talauci da jahilci su ne sababin rushewar dauloli koda manya ne, amma yayin da aka sami ilimi sannan ga arziki, to dukkanin wata firina ta kau. Shi ya sa Manzon Allah S.A.W yake cewa, “Dukkanin wanda ya tashi yana da abin da zai ci, kuma yana da aminci, to tamkar an ba shi arzikin duniya ne gaba daya.”

  Da wannan nake cewa, masu girma alkalai, shuwagabanni da masu bibiyar mu, za su yarda da ni dari bisa dari kan abubuwan da na ambata.

  Wassalamu alaikum. 

  Jiddah Haulat Nguru daga kungiyar Nguru Writers Association.

Comments

0 comments