Rubutu

Blogs » Abubuwan Al'ajabi » Ban taba rubuta fim ba, bani da sha’awar yi – Bello Hamisu Ida

Ban taba rubuta fim ba, bani da sha’awar yi – Bello Hamisu Ida

 • Filin Bakon Mako shiri ne da ya saba zakulo muku manyan marubuta da manazarta da mawaka don tattanawa da su. Yau filin namu zai tattauna da babban fasihin marubuci Bello Hamisu Ida. Ku biyo mu cikin tatraunawar wanda ni Hauwa’u Muhammad da Maryam Haruna za mu gabatar.

  T1. Muna son jin tarihin bakon namu.

  Bello Hamisu: Sunana Bello Hamisu Ida, wanda na fito daga tsatson Sarkin Fulani Yarima Inti da ya yi sarautar Ingawa. Kakana na biyu shi ne Muhammadu Bello. Ni da ne ga zuri'ar Saje Ida, sananne a aikin Dan doka, wanda ya yi rayuwarsa tsakanin garuruwan Katsina da kewayenta. Na taso a cikin Jihar Katsina inda na yi karatu tun daga matakin firamare zuwa Jami'a. Na nazarci harshen Turanci a Jami'ar Umaru Musa Yar’aduwa, kuma ni tsohon malamin makaranta ne inda na rike mukamin hedimasta. Na fara rubuce-rubuce tun a can baya inda na yi zurfi a cikin harkar.

  T2. Wace shekara ka fara rubutu kuma zuwa yanzu litattafai nawa ka rubuta?

  Bello Hamisu: Na fara rubutu a shekar 1999, ya zuwa yanzu ina da litattafai kamar 10 a kasuwa, mafi yawansu na koyarwa ne ga dalibai yan makarantar firamare. Amma dai ya zuwa yanzu na rubuta litattafai 48 daga cikinsu ne aka buga guda goma kuma suna kasuwa kamar yadda na ambata can baya.

  T3. Wadanne irin kalubale ka fuskanta a lokacin da ka fara rubutu?

  Bello Hamisu: Da yake lokacin farko da na fara rubuce-rubuce na fara ne da na soyayya, don haka mahaifana ba sa so, to na iya cewa wannan ne kalubale na, wato dai mahaifana ba su son ina rubuce-rubuce musamman na soyayya. To amma daga bisani da na juya akalar rubutana zuwa litattafan ilimi, to na samu amincewarsu suka kuma barni na ci gaba da wassafa ilimina. Sai kuma kalubale na biyu wanda kowane marubuci na fuskanta, shi ne na kasuwanci, inda kasuwar littafi ta ja baya sosai.

  T4. Wadanne irin nasarori ka samu a dalilin rubutu?

  Bello Hamisu: Babbar nasarar da na samu ita ce, ta lashe gasar adabi ta Aliyu Mohd Book Prize 2018 in da na zo na daya da littafina mai suna Sabo Da Maza. Nasara ta biyu kuwa, sanadiyar littafina mai suna Ilimin Hausa wani Kamfani mai suna Educate Series suka bani Babban Editor na kamfanin, wanda yanzu haka ima cikim jerin marubuta da suka samar da litattafan ilimi a karkashin kamfani. Nasara ta uku kuwa, shi ne sanin mutane da na yi sanadiyar adabi, musamman malamai da kuma yan'uwana dalibai da aminai da sauransu. Nasoriri dai basu iya faduwa cikin sanholom tawada daya, saidai a fadi abun da alkamami ya samu tazarar lissafawa.

  T5. Menene ya ja ra'ayinka ka fara rubutu?

  Bello Hamisu: Dalilin bai wuce na yawan karance-karance ba, ni mutum ne mai tsananin son karatu, to wannan ya dasa sha’awar son zama marubuci. Daga wannan kuma sai in ce na tashi kawai na samu kaina a ciki ba tare da sanin wani dalili ba.

  T6. Wanne jigo ka fi yin amfani da shi a rubutunka?

  Bello Hamisu: Mafi yawa na fi amfani da jigon soyayya da rayuwa da matsaloli. Haka kuma yanzu da na sauya salon rubutuna zuwa alkalamin yara ina amfani da salon jan hankalin yara. 

  T7. Wace irin gudummawa za ka bawa rubutu da kuma marubuta?

  Bello Hamisu: Ina bada gudummuwa ta bamgarori da dama, musamman ta bangaren ilimin yara na firamare, haka kuma ina ba da gudummuwa wajen zakulo tarihi da ingantashi da bambancin tarihi da tarihihi. Haka kuma ina bada gudummuwa wajen inganta adabin malam Bahaushe. 

  T8. Shin kana rubuta littafi a yanar gizo ko iya bugawa kake yi?

  Bello Hamisu: Bana daga cikin marubutan online, saidai ina sha’awar zama daya daga cikin musamman yanzu da nake inganta wata manhaja wacce za ta iya samar da kungi a online. Duk litattafaina na bugawa ne.

  T9. Wasu da dama suna son fadawa harkar rubutu, sai dai yadda wasu mutane suke kallon harkar rubuce-rubece a matsayin hanya ce ta bata tarbiyya. Me za ka ce game da haka?

  Bello Hamisu: Abin da zan ce a nan, duk mai sha’awar adabi kawai ya tsunduma cikin harkar musamman in ya inganta iliminsa, saidai ya zabi alkibla mai kyau. Haka kuma rubutu hanya ce ta isar da ilimi amma dai wasu ko in ce kadan daga cikin marubutan adabi ne ke bin salo ko alkiblar bata tarbiyya, wadannan kuma karara suna daga cikin marubutan da ake kyamata sosai kam. 

  T10. Shin kana da ubangida a harkar rubutu?

  Bello Hamisu: Bani da maigida a harkar adabi, asalima sai da na kammala koyon dabarun rubutu da dadewa sannan aka sanni a matsayin marubuci. Sai dai ina da malamai masu bani ilimi a fagen wassafa harkokin adabi.

  T11. Wace irin shawara za ka ba wa marubuta masu tasowa da ma wadanda suke son fara rubutu?

  Bello Hamisu: Kafin su fara koma bayan sun fara su rika inganta iliminsu, su nemi masana wadanda za su rika saita masu hanyar da suka dauka a cikin adabi. Kuma in sun fara kar su tsaya har sai sun kai bantensu.

  T12. Wanne irin cigaba adabin Hausa ya samu a yanzu?

  Bello Hamisu: Shi adabi ai tun farkon kafuwarsa a kowane karni kuma yana samun ci gaba. Saidai zamani ya bambanta, misali ace a wannan zamani an samu ci gaban adabi ta bangaren yanar gizo, inda aka kirkiro hanyoyin isar da ayyukan adabi a yanar gida, wato ana yin dab'i a yanar gizo. Kusan yanzu duk wani marubucin duniya ya koma yin rubutu a yanar giza don aikinsa ya zagaye fadin duniya cikin kankanen lokaci. 

  T13. Shin kana da wani gwani ko gwana wadanda rubutunsu ya ke birgeka?

  Bello Hamisu: Da yake ni makaranci ne sosai, ko yanzu ina karanta litattafan wasu marubuta, wasu a online wasu kuma hardcopy. Don haka, kusan na iya cewa duk marubuta gwanayena ne. Ina da shauki sosai wajen karanta labarai na marubuta.

  T14. Wanne littafi ka fara wallafawa? Wanne ne na karshe cikin jerin littattafanka da suka shiga kasuwa? Wane littafi ne yake gab da bayyana daga jerin littattafanka 48?

  Bello Hamisu: Littafin dana fara wallafawa shi ne Hikimarka Jarinka. Na karshen su kuwa shi ne Ilimin Hausa 1 To 6. Yanzu kuwa wanda ke gab da fitowa shi ne Sabo Da Maza. Amma akwai wasu da muka rubuta wanda na jagoranta amma wadannan na makarantun firamare ne, ina tsammani za su riga fitowa saboda aikin kamfani ne.

  T15. Shin ko kana yin rubutun fim? Idan ba ka yi kana da sha’awar farawa nan gaba?

  Bello Hamisu: Ban taba rubuta fim ba. Bani da sha’awar yi, saidai ku sani, idan aka ce kai marubuci ne, wasu za su yi ta jawo hankalinka wajen rubuta masu fim. Yanzu haka ma dai wasu actors a Kannywood sun ci karfina, zan fara yi masu rubutun series film. Saidai ban sani ba ko abum zai daure, domin dai bana da sha’awar rubutun fim din gaskiya.

  T16. Ka taba yin wani rubutu da ya baka wahala? Wanne ne?

  Bello Hamisu: Rubutun da ya bani wahala biyu ne, Littafin Ilimin Hausa 1 to 6 kusan tun 2015 nake rubuta shi, amma ko jiya saida na yi updating wani bangare saboda shi littafin ilimi yana da wahalar sha’ani saboda ana so a hakaito abun da malami zai koyar in ya shiga aji, a nan dole sai marubuci ya gamsar da dalibi kuma ya gamsar da malami. Wannan shi ne rubutun da ya bani wahala. Sai shi littafin Sabo Da Maza wanda ya lashe gasar Gusau Institute a shekarar 2018, littafi ne mai kalmomi dubu dari, kalma dubu dari kuwa ba nan take ba.

  T17. A baya ka yi batun cewar kana gab da kaddamar da wani rumbu ko manhajar da za ta taskance littattafanka, hakan ya nuna kai masanin na'ura mai kwakwalwa ne. Shin kana da wani kamfani na dab'i ne da ya kamata marubuta su sani?

  Bello Hamisu: Ina da madaba'a mai suna MELON PUBLISHERS na yi mata rigista haka kuma ina buga wasu litattafan nawa a karkashin wannan kamfani. Ta bangare computer, ni dalibi ne da ke koyom hanyoyin sarrafa manhajar komfuta, na kware wajen sarrafa manhajar MS Word, Corel Draw, Adobe Photoshop, Adobe after effect, video maker, da Internet Explorer da sauransu, haka kuma ina koyon 3D da 2D Animation da manhajar Blender da android studio. Ina koyon Programming Language na C++ da Java, da Python. Amma ta bangaren programming Language da yake tsantsan Science ne ni kuma dalibin art ne, na kan sha wahala kafin koyon, saidai ina maida hankali domin abun yana daukar ra’ayina sosai.

  Tsara tambayoyi da gabatarwa: Hauwa'u Muhammad tare da Maryam Haruna.

Comments

1 comment