Makalu

Blogs » Kasuwanci da Sana'o'i » Waiwaye kan Barnie Madoff: Jagoran madamfara a duniya

Waiwaye kan Barnie Madoff: Jagoran madamfara a duniya

 • Hausawa suka ce komai girman gona tana da kunyar karshe. Wannan magana haka take, domin kuwa a ranar 14 ga Afrilu na 2021, shahararren dan damfarar nan, Barnie Madoff ya sheka barzahu bayan ya sha fama da cututtuka a gidan yarin da yake tsare, inda aka yanke masa shekaru 150 a shekarar 2009.  Barnie ya mutu yana da shekara 82 kuma an kiyasta cewar ya shekara 40 da doriya yana aikata zamba cikin aminci da sunan kasuwancin hannun jari.

  Mardoff ƙasurgumin dilan hannun jari ne wanda ya soma sana'ar tun cikin 1960 kuma ya samu karbuwa sosai a hannun jama'a saboda yadda yake biyan kuɗin kamasho mai yawa. Saboda haka yayi ta samun ɗaukaka wajen mutane da gwamnati har ya zama ɗaya daga shugabanni a kasuwar hannun jarin da ake kira NASDAQ (National Association of Securities Dealers Automated Quotations), ita ce katafariyar kasuwar hannu jari ta biyu faɗin ƙasar Amerika.

  Sai dai abin da mutane ba su sani ba shi ne, duk abubuwan da yake biyan mutane, wayon nan ne na damfara da aka fi sani da Ponzi. A lokacin da asirinsa ya tonu a cikin watan Disamba na 2008, an ƙiyasta cewar mutane kimanin dubu 40 ne suka faɗa tarkonsa, kuma ya jawo musu asarar kimanin dala biliyan 65, watau misalin naira Tiriliyon 7 da doriya a wancan lokacin.

  Daga cikin fitattun mutanen da Barnie ya damfara har da Steven Spielberg, wani shahararren daraktan finafinai a masa'antar Hollywood. Hakanan ma wani fitaccen marubuci wanda ya taɓa lashe kyautar lambar Nobel ta zaman lafiya mai suna Elie Weisel ya faɗa tarkonsa na damfara.

  Masana kan gadon lissafi da bin ƙwaƙƙwafi sun sha zargin almundahana a cikin lamarin kasuwancin nasa, sai dai duk hujjojin da suke dogaro da su ba a samun dacewa. Sau takwas hukumar kasuwannin hannun jari ta Amerika na ƙaddamar da bincike akansa, daga bisani sai a wanke shi tsaf da sabulu.

  To sai dai a farkon shekarar 2008 alkadarinsa ya soma karyewa yayin da aka samu harkokin kudi inda mutane suka yi ta sayar da kadarorinsu har ta kai ba a iya samun masu zuba hannun jari. Ashe duk burgar da Madoff yake yi da kuɗin mutane yake yi. Kasuwancim da yake yi illa ikirarin cewar yana yi zuƙi ta malli ne. Idan mutane suka zuba kudi a kamfaninsa da nufin a sayo musu hannun jari, sai ya kwashe kuɗin duka ya zuba a wani asusunsa da ke bankin Chase da ke Manhattan. A wannan asusun yake samun kuɗin ruwa, idan wani ya buƙaci kuɗinsa, sai ya kwaso daga asusun a biya shi. Da haka ya jima yana shan miyarsa ba tare da ta ruɓe ba.

  Baya ga wayon da yake da shi na biyan wasu da kudin wasu, Madoff yana da ɗaurin gindi a kasuwar hannun jari, kuma yayi dabarar da ya dasa danginsa da abokansa da surukansa ke jan ragamar wasu bangarori na kasuwar. An ce mafi rinjayen ma'aikatan kamfaninsa danginsa ne. Babban akawunsa mai suna Peter Madoff shi ne yake jirkita lissafi domin ya dace da yadda mutane suke son gani. Shi ya samar da wata manhajar kwamfuta da ke iya jirkita bayanai zuwa yadda ake so a lokacin da ake so.

  Haka nan 'ya'yansa waɗanda kuma suka tona masa asiri watau Mark da Andrew sun kasance manyan manajoji a kamfanin duk da bincike ya nuna cewar ba su san irin wainar da babansu ke toyawa ba tsawon shekara da shekaru. Shi dai Mark ya rataye kansa ne a ranar 11 ga Disamba na shekarar 2010, watau bayan shekara biyu da kama babansu. Shi kuma Andrew ya mutu ne a ranar 3 ga Satumba 2014 bayan fama da jinya.

  Har ila yau Barnie mutum ne mai kyauta da shiga cikin harkokin kungiyoyi masu zaman kansu inda yake bada gudunmawa ta bajinta da kasaita. Don haka mutane ke masa kallon wani gwarzo mai abin mamaki wanda babu kamar sa.

  Tun kafin hukuma ta kai ga cafke Barnie Madoff, wani shahararren manazarci kuma mai bin ƙididdigar lissafin kuɗi mai suna  Harry Markopolos, ya sha faɗin cewar ikirarin karya Barnie yake yi kan hanyoyin da yake bi yana samun riba mai yawa fiye da kowanne dillalin kasuwar hannun jari. Ya kara da cewar bai ga ta inda za a hada biyu da wata biyun ta ba da shida ba. Da haka yayi ta kokarin wayar da kan mutane da hukumomi amma aka yi watsi da shi. Harry ya bayyana cewar tun shekarar 1999 da ya gano kutunguilar mutumin yake ta hakilo amma bai samu goyon baya ba, maimakon haka kullum sai barazana yake fuskanta da kuma gori daga wadanda ke amfana a jikin Barnie. Bai samu kansa ba sai da gumu ta yi gumu a shekara ta 2008 inda Barnie da kansa ya fallasa irin aika aikar da ya shekara da shekaru yana aiwatarwa.

  Kamar yadda na soma bayani, a lokacin da aka shiga ruguntsumin tattalin arziki, mutane suka yi ta sayar da kadarorinsu suna biyan bukatu, kuma aka samu ragowar masu sayen hannun jari, sai Barnie ya shiga hauma-hauma. Ya soma kwashe kuɗaɗensa daga bankuna da kasuwanni yana biyan mutane. Kodayake an ce a shekara 2005 ma saura ƙiris asirinsa ya tonu lokacin da mutane suka buƙaci cire dala miliyan 105 alhali dududu asusun bankinsa na Chase bai wuce dala miliyan 13 ba. Da yayi sa'a, sai ya samu lamunin dala miliyan 342 wadda ta sa ya farfaɗo.

  A cikin shekarar 2008 masu zuba hannun jari suka buƙaci fitar da dala biliyan 7 nan take. Nan ma dai ya shiga fudun-fuduma har ya sallame su ta hanyar lalubo wasu kudaden a wasu wuraren. Daga nan kuma wasu masu kudin suka buƙaci fitar da zunzurutun kudi dala biliyan 320, a lokacin kuwa dala miliyan 300 ne suka rage masa a banki, kuma daga su ba za a kara ba shi wani lamuni ba. Abokan sana'arsa da bankuna sun gaji da yi masa lamuni ba tare da cikawa ba.

  Mutane sannu a hankali suka soma zargin wani abu daga ayyukansa. Sai dai babu wata ƙwaƙƙwarar hujja da za ta tabbatar da zarginsu. Shi kuwa Barnie yana ta zuba labarin cewar duk da karayar tattalin arzikin da ta shafi duniya, shi bai girgiza ba. Sai ma ya sha alwashin zai kyautatawa ma'aikatansa fiye da yadda ya saba.

  A ranar 8 ga watan Disamba 2008, Barnie ya tara ma'aikatansa yayi musu albishirin cewar zai raba musu dala miliyan 170 domin su ji daɗin hutun shekara. Ma'aikata suka yi ta murna, amma 'ya'yansa na cikinsa da ke aiki tare da shi watau Mark da Andrew ba su yarda da sambatunsa ba. Don haka suka ja shi ɗaki su kaɗai suka tasa shi gaba da tambayar ina zai samo waɗannan maƙudan kuɗaɗen alhali ga masu ajiya ma ya kasa biyansu? Da ya ga yadda suka ritsa shi, sai ya fashe da kuka inda ya bayyana musu gaskiyar maganar cewar ZUƘI TA MALLI ce kuma ba shi da komai, tusa ta ƙarewa bodari!

  Suna jin haka, sai suka fita suka bar shi. Kai tsaye suka sanar da lauyansu sannan suka tafi ga hukuma suka sanar. Washegari aka zo da rundunar jami'an tsaro aka yi awon gana da Bernard Lawrence Madoff wanda aka fi sani da Barnie. Mutumin da ya shekara sama da 40 yana damfarar mutanen da suka haɗa da 'yan kasuwa, 'yan siyasa, ma'aikata, 'yan wasan kwaikwayo da 'yan fansho. Babu wani ɓangare na al'umma da bata shiga tarkon wannan mutumin ba.

  Sannu a hankali Barnie ya zauna yayi ta kwance bakin jakarsa yana faɗin irin aika-aikar da ya tafka. Sai a lokacin yake dana sani kuma yake neman gafarar jama'a. Abin da bai sani ba shi ne, mutane sama da dubu 400 suka cutu da aikinsa, daga ciki har da waɗanda ɓacin rai ya sa suka haɗiyi zuciya suka mutu. Wasu kuma sun durƙushe, wasu kuma bashi ya karye musu. An ƙiyasta cewar sama da dala biliyan 65 ne suka yi ɓatan dabo a lokacin da ya shiga hannu.

  Ba tare da yayi musu ba, Barnie ya amince da laifuffuka goma 11 da ake tuhumar sa da su. Ita kuwa kotu bisa adalcin ta, ta zartar masa da hukuncin ɗaurin shekara 150 a gidan gyaran hali. Lauyansa ya so ya nemi gafara domin a rage masa hukuncin zuwa shekara 12, bisa dalilin cewar Barnie ya riga ya tsufa, domin kuwa a lokacin ya kai shekara 72 a duniya. Kotu ba ta karɓi uzurin ba, aka hankaɗa shi ya soma girbar abin da ya shuka. A ranar 14 ga Aprilu na 2021 Barnie ya ja numfashinsa na ƙarshe a gadon asibitin ƙasa da ke garin Butna cikin jihar North Carolina.

  Haƙiƙa za a cigaba da tunawa da Barnie Madoff a matsayin ƙasurgumin madamfarin da ya daɗe a duniya yana sheƙe ayarsa, amma ƙarshensa ya zama irin na kifi, daga ruwan sanyi zuwa ruwan zafi.

  Darussan koyo

  Masu zuba hannun jari a kowacce irin kasuwar kudi da ke duniya, na bukatar nazarin da naƙaltar yadda Barnie ya ci kasuwar sa ya tashi. Tun daga yadda yake ta haɓaka da dukiyar mutane har zuwa lokacin da asirinsa ya tonu. Daga cikin waɗannan darussa sun haɗa da:

  1. Kowa tasa ta fisshe shi: A kasuwan hada-hadar kuɗi, ba a duban mutum da irin ayyukansa nan da nan a yarda da shi. Idan aka zo maka da wani abin hannu jari, kada ka yarda da mai ikirarin, je ka yi bincike na ƙashin kanka. Ko kuwa ka ɗauki hayar wani ƙwararren da zai bincika maka.
  2. Fankan-fankan ba ta kilishi: Duk wanda ya fiye nuna bajinta da tinƙahon samu fiye da kima a kasuwar hannun jari, wajibi ne a bincike shi. A halin yanzu da hankula suka karkata ga kasuwar jarin Cryptocurrency, duk da ɗumbin kuɗaɗe da aka ce ana samu a cikinta, ba kasafai ake samu ya wuce tunani ba. Duk wanda yayi iƙrarin haka kuwa, wajibi ne a bincike shi. Ta yiwu hakan ne ya sa kwanaki hukumar kula da hannun jari ta SEC ta shiga binciken attajirin duniya Elon Musk bisa ikirarin ribar da yake samu a kudin intanet mai suna Dogecoin.
  3. Wanda zai baka riga dubi ta wuyansa: Matasa da yawa na shiga harkar hannun jari ba tare da bincike ba, da zarar an kawo musu tallan wani abu da romon baka, sai su zuge dukiyarsu ciki. Sai dai a bar su da kallon waya suna hasashe da tunani mara kangado. A rayuwar Barnie, mun fahinci cewar harkar kudi ba kowa ake amincewa ba, domin kuwa duk shekarun da yayi yana ƙunsa tsiyarsa shi kaɗai, a ƙasa da awa 24 'ya'yansa suka tona masa asiri bayan ya amince ya tona musu cikinsa.
  4. Yau da gobe bata bar komai ba: In dai mutum zai taki rashin gaskiya, ko ba daɗe sai asirinsa ya tonu. Don haka gaskiya ita ce matakin nasara a kowanne lamari.

  Idan mun samu lokaci za mu yi waiwaye kan wasu shahararrun damfara da harƙallar da aka samu a tarihin duniya ta fuskar hada-hadar kuɗi da dukiya.

Comments

0 comments