Rubutu

Blogs » Kagaggun Labarai » Tekun Labarai: Kaddara Ta Rigayi Dabara

Tekun Labarai: Kaddara Ta Rigayi Dabara

 • Ku latsa nan don karanta labarin Sharri Jakada Ne.

  An yi wani babban Sarki da ake kira Ibrahimu wanda ya kasance ƙarƙashinsa akwai sarakuna da dama da suke masa biyayya. Yana da runduna da yawa waɗanda duk garin da suka hara da yaƙi sai sun ga bayansa. To amma duk da kasancewarsa babban Sarki mai faɗa a ji, ya kasance ba shi da magaji, walau mace ko kuwa namiji. Wannan abu na matuƙar ƙona masa zuciya musamman idan ya tuna cewa dukan abin da ya mallaka fa ya zama iska ke nan, zai tafi baitulmali, mulkin kuma wani ya samu wanda ba jininsa ba. Ya nemi auren 'ya'yan sarakuna da na talakawa da dama, har ya daina aure - auren ya koma sayen kuyangi yana sa su ɗaka domin kwaɗayin samun magaji.

  Allah da ikonsa kuwa sai wata kuyangarsa ta samu ciki, Sarki ya yi ta murna ya sa aka riƙa kula da ita ana ba ta magani da abinci iri - iri. Yayin da watan haihuwarta ya matso, sai Sarki ya sa a ƙara kula da ita, ya kirayi masana ilmin taurari da masu bugun ƙasa suka riƙa duba masa halin da take ciki. Da lokacin haihuwar ya zo, aka zauna ana jiran zuwan jariri. Bayan wani lokaci sai kuyangar ta haihu. Ta samu ɗa namiji kuwa. Sarki ya cika da matuƙar farin ciki, ya sa aka buga masa taurari domin su gano sha'anin rayuwar yaron a duniya.

  Malamai suka duƙa suna haɗa alƙaluma suna tattaunawa tsakaninsu. Bayan wani lokaci babbansu ya duƙa gaban Sarki ya ce, "Allah ya ba ka nasara, hangen gaba ba shi da amfani, ya fi kyau a bar kaza cikin gashinta." Sarki ya ce, "ku faɗa min ko mene ne babu komai." Suka ce, "Ranka ya daɗe muna tsoron rayukanmu bisa ga abin da muka hango." Sarki ya ce, "na yi muku alƙawarin ba zan muku komai ba komai rashin daɗin bayanin."

  Bayan sun gamsu da kuɓutar rayukansu sai babban ya sake duƙawa ya ce, "abin da muka gano shi ne, bayan shekara bakwai ɗanka zai gamu da tsautsayi na harin zaki zai kashe shi, amma idan ya kuɓuta daga harin to nan gaba zai zama sanadin mutuwar ka."

  Da Sarki ya ji haka, sai yanayinsa ya sauya. Ƙirjinsa ya ƙuntata. Duk da haka ya kanne kamar bai ji zafin komai ba, ya ɗebo kyauta ya ba wa malaman ya sallame su. A ransa ya shirya yadda zai kauce wa faruwar wannan al'amari kamar yadda aka ce masa zai faru. A kullum ya tashi sai ya ji maganar na damun sa duk da cewa a karon farko ya ƙaryata malaman. Bayan an yaye yaron sai ya sa aka gina wani gida a can saman dutse, ya hana kowa zuwa wajensa daga shi sai mai rainon sa. Duk mako yake sawa a kai musu abubuwan da suke buƙata na daga abinci da sutura da sauran kayayyaki. Shi kuma Sarki ba ya zuwa sai bayan wata guda, sai a maƙala tsani ya taka ya hau, a kawo masa yaron ya yi masa wasa yana daga kan tsanin, sannan ya sauka.

  Hashim ɗan Sarki Ibrahim ya riƙa girma, yana ƙara wayo yana fahimtar al'amura. Sannu a hankali har tsoron nan ya fita daga ran mahaifinsa, ya sakankance maganar nan da aka faɗa game da ɗansa duk shifcin gizo ne. A lokacin kuwa shekararsa bakwai a duniya, saura wata ɗaya ya cike shekara ta takwas. Sarki ya ƙudure cewa zai dawo da ɗansa gida da zarar ya cika shekara takwas, domin hasashen da aka yi kansa bai tabbata ba.

  Da yake ƙaddara ta rigayi dabara, a wannan daren sai wasu mafarauta suka raraki wani zaki. Suka yi masa rauni a allon kafaɗarsa na dama da kibiya. Ya ji zafin harbin sosai, amma ya jure ya gudu domin neman mafaka. Mafarautan nan suka bi shi da gudu, sai ya tsere musu ta hanyar faɗa wa gidan nan da ake kula da Hashim ɗan Sarki Ibrahim. Yana shiga ya yi arba da Hashim yana wasa. Ya daka tsalle kansa ya yakushe shi a kafaɗa. Yaro ya ƙwalla ƙara mai firgitarwa ya faɗi sumamme. Uwar goyonsa na ciki ta ji ƙararsa, ta fito da gudu a gigice, zaki na ganinta ya ƙyale yaro ya daka tsalle ya banke ta. Nan take ta faɗi matacciya ko shurawa bata yi ba. Masu farauta suka iso wurin suka tarar da yaro kwance magashiyyan ga zakin ya kashe wata yana cin namanta. Yana ganin su ya yi gurnani ya juyo kansu a fusace. Nan da nan suka hau harbinsa da kibau sai da ya faɗi matacce. Suka binne ragowar naman uwar goyon Hashim, shi kuma suka tafi da shi tare da mushen zaki zuwa garinsu. Sai da suka gyara masa raunin da ya zakin ya ji masa a kafaɗa sannan ya farfaɗo, inda ya tsinci kansa a wani wuri dabam.

  Haka dai Hashim ya zauna a wurin mafarautan nan waɗanda ba farauta kaɗai suke yi ba, suna yin noma da kiwo, wani lokacin kuma suna fita hanya su yi fashi su koma ƙauyukansu kamar ba su aikata komai ba.  Yana nan wurinsu har ya kai shekara goma sha biyu. Ya koyi hawa doki da sukuwa da jefa mashi da wasa da takobi, da harbi da kibiya, sannan ya soma fita farauta da tare hanya tare da mariƙansa.

  Wata rana suka fita farauta ba su kamo komai ba, sai suka wuce kan hanya domin tsare hanyar fatake. Nan ma ba su samu nasara ba, domin kuwa ayarin da suka gamu da su jarumai ne, suka auka musu da yaƙi suna sara da sukan su, har suka karkashe su baki ɗaya. Hashim ne kaɗai ya rage wanda shi ma ba su lura da shi  ba ne amma sun yi masa rauni mai yawa. Bai samu kansa ba sai da sanyin asuba ya doke shi, ya tashi ya ga cewa shi kaɗai ne ya rage cikin mutanensa. Ya rarrafa ya tafi bai san inda za shi ba. A hanya ya gamu da wani mutum, ya tambaye shi abin da ya same shi. Ya faɗa masa komai daga farko har ƙarshe. Da mutumin ya ji zancensa sai ya tausaya masa, ya ɗora shi kan jakinsa ya tafi da shi garinsu ya yi ta jinyarsa har ya warke. To shi mutumin nan aikinsa shi ne tono ma'adinan ƙarƙashin ƙasa yana kaiwa garuruwa masu nisa yana sayarwa.

  Da ya lura Hashim ya warware, ƙarfinsa ya dawo masa, sai ya rarrashe shi kan ya riƙa bin sa suna harkar tonon tare. Hashim ya amince suka tafi da jakuna biyu zuwa cikin ƙungurmin daji, sai da suka shafe kwana biyu a dajin sannan suka samu wurin da suke buƙata. Wani waje ne a tsakanin duwatsu inda suka sami wata rijiya take zururu amma babu ruwa a cikinta. Bayan ya yi 'yan karance - karancensa sai ya zura igiya da guga cikin rijiyar, sannan ya ɗaura wa Hashim igiyar, ya zura shi cikin ramin. Da farko ramin ya kasance mai zafin gaske, har iska na ƙoƙarin wuyata ga numfashinsa. Amma a can ƙasa sai ya zamana da yalwa da iska mai daɗi tana huro masa ta ko’ina. A gefe guda kuma wasu irin duwatsu ne masu daraja manya - manya. Yaro ya riƙa ɗiba yana cikawa a guga mutumin yana ja yana juyewa a mangalar jakuna. Da ya cika managalolin ya ga sun ishe shi sai ya turo igiyar cikin ramin, ya yi tafiyarsa ba tare da ya fito da Hashim ba.

  Da ya fahimci abin da mutumin ya aikata masa, sai baƙin ciki ya kama shi ya yi ta kuka yana cewa, "na kuɓuta daga halakar zaki, na tsira daga sharrin mahara amma ga shi nan zan mutu  cikin rami a wofi, babu wanda ya damu da ni." Daga bisani dai da ya fahimci kuka ba zai masa magani ba, sai ya miƙa al'amarinsa ga Allah mai girma. Ya sa hannunsa yana cire duwatsun nan masu daraja yana ajiyewa.  Kwamfa yana wannan aikin da zummar ko zai samu wata ƙofa da za ta fitar da shi, ashe a jikin wajen kogi ne. Nan take ruwa  ya shigo da ƙarfinsa. Ya yi awon gaba da shi inda ya riƙa buga jikinsa da sassan garun duwatsu, ya jefa shi can wani wuri a waje a sume. Haka ya kasance a yashe har kwana sannan ya farfaɗo. Ya tashi ya ci gaba da tafiya bai san inda ya nufa ba. Bai jima ba ya isa wani ɗan ƙauye a galabaice, suka rirriƙe shi, suka kwantar da shi, suka yi ta ba shi magani suna lura da shi har ya samu kansa. Bayan ya warke suka tambaye shi labarinsa ya ba su. Suka yi ta mamaki, musamman irin haɗurran da ya tsallake a rayuwarsa. Daga nan suka tambaye shi mahaifinsa ya ce musu, "iyakar sanina da shi yana zuwa gare ni lokacin da ina saman dutse, amma ba zan iya shaida shi ba." Mutanen garin nan suka so shi sosai musamman da suka gane irin jarumtakarsa da kuzarinsa a wurin farauta.

  Game da Sarki Ibrahim kuwa, yayin da gari ya waye, ya tafi domin ya ɗauko ɗansa, aka sa masa tsani kamar yadda aka saba. Ya hau ya yi kiran matar nan amma ya ji shiru bata amsa ba. Ya sake kira bai ji motsin komai ba, sai ya sa aka shiga ciki. Babu kowa sai dai ga jini nan ko ina faca - faca babu kyawun gani. Mai dubawa ya dawo ya faɗa masa. Sarki ya shiga da kansa ya gani. Ya sauko yana mai baƙin ciki. Ya tafi wurin masu binciken taurari suka duba. Suka ce masa, "zaki ne ya cinye su kai kuma ka kuɓuta daga mutuwa ta dalilinsa. Da ma haka aka ƙaddaro babu makawa. Kuma bincikenmu ya nuna cewa sai da zakin ya raunata shi a kafaɗa kafin ya kashe shi." Sarki ya zauna yana mai baƙin ciki da mutuwar ɗansa. Aka yi makoki na mako guda sannan aka watse, aka manta da wannan abu.

  Hashim kuwa ya girma sosai a wajen mutanen ƙauyen nan har ya balaga ya isa munzalin mutum. Ya zamana duk wani abu da za a yi na gangami da nuna jaruntaka shi ne a kan gaba. Wata rana wasu 'yan fashi suka je birni suka yi ɓarna sannan suka taho da wani babban attajiri. A hanya suka kashe shi, suka jefar da gawarsa a wannan ƙauyen da Hashim yake. Sarki Ibrahim ya aiko da wasu dakarunsa domin su ƙwato wannan attajiri. Da suka iso ƙauyen nan sai suka tarar da gawarsa, lokacin kuwa alfijir na daf da ketowa, jama'ar ƙauyen ba su san abin da ke wakana ba.

  Ba tare da bin bahasi ba dakarun nan suka yanke hukuncin cewa ɓarayin a wannan ƙauyen suke. Suka shiga kisan mutane suna ƙona gidaje, suna lalata dukiya.  Hashim da abokansa masu tsaron gari suka ji labari, nan fa suka yi shirin yaƙi suka gamu da dakarun Sarki suka yi musu fata - fata. Babu wanda ya tsira sai mutum biyu da suka kai labari shajara - majara. Sarki ya fusata ƙwarai da wannan aika – aika. Nan da nan ya yi shiri da kansa ya tafi zuwa ƙauyen da dukan askarawansa. Hashim na cikin matasan da suka nuna jarumtaka ƙwarai da gaske, domin kuwa shi ya taɓe kwari da baka ya harbi Sarki a gadon baya.

  A ƙarshe dai aka kame dukan mutanen garin aka tafi da su. Harbin da aka yi wa Sarki ya yi masa rauni mai yawa. Duk da an yi masa magani amma raunin na ƙara yi masa ciwo ƙwarai. Ya aika aka zo da masu bugun ƙasa ya ce musu, "kun ce mutuwata na hannun ɗan da na haifa na cikina. Kuma kun sani a halin yanzu ba ni da magaji. Yaya aka yi mutuwar kuma ta faɗo hannun ɓarayi?" Suka ce, "wannan kam yana daga hukuncin Allah wanda bugun ƙasa bai isa ya gane komai kan haka ba. Amma iyakacin nazarinmu shi ne mutuwarka na da musabbabi daga ɗan da ka haifa." Sarki ya ce, "a yadda nake ji a raina, wannan ciwon ba mai warkewa gare ni ba ne. A zo min da ɓarayin nan duka." Aka shigo da mutanen ƙauyen nan dukansu a ɗaɗɗaure.

  Sarki ya ce musu, "ina so ku faɗa min gaskiya babu ɓoyewa, a cikinku wane ne ya harbe ni da kibiya?" Gaba ɗaya suka nuna Hashim. Aka matso da shi gaba ga Sarki. Duk da ya yi baƙi, kammaninsa na asali kusan sun ɓace amma sai da Sarki ya ji wani irin abu game da shi. Ya ce masa, "wane ne mahaifinka? Ka faɗa min gaskiya, ni kuma na yi alƙawarin yafe maka laifinka."

  Hashim ya ce, "bisa gaskiya ya shugabana, ban san mahaifina ba, domin kuwa a gidan saman dutse na girma har na yi wayo. Daga bisani zaki ya kashe mai raino na, na shiga hannun wasu mutane." Ya ba shi labarinsa kaf, tun daga farko har ƙarshe. Sarki na jin wannan labari sai ya yi kururuwa ya ce, "wallahi wannan shi ne ɗana!" Mutane suka dube shi da mamaki, shi kuwa ya ce da Hashim, "yaye kafaɗarka mu gani." Ya yaye sai ga tabon inda zaki ya raunata shi, ya yi daidai da yadda masu bugun ƙasa suka shaida masa.

  Sarki ya aika aka zo da kuyangarsa wadda ta haifi Hashim, tana ganin sa ta shaida shi, ta rungume shi tana kuka tana cewa, "dama ban fidda ran zan sake ganin ka ba. Yau ga shi Allah ya haɗa mu." Da wannan Sarki ya haƙiƙance ɗansa ne. Ya aika aka kirawo dukan manyan fada da attajirai da masu bugun ƙasa da talakawa. Ya ce da su, "ku sani Allah ya rubuta ƙaddara ta rigayi dabara wala fata. Yadda Allah ya tsara babu makawa sai ya tabbata. Komai dabarar mutum bai isa ya kauce mata ba. Kasancewar an ƙaddaro dalilin mutuwata na hannun ɗan da na haifa, to ga shi bisa hukuncin Allah hakan ya tabbata. Amma ku sani na yafe wa ɗana bisa aikin da ya yi bisa kaina cikin rashin sani. Kuma na gode wa Allah da zan bar duniya a cikin gidana gaban jama'ata ba a wani waje da za a mance da ni ba." Da ya kawo nan sai ya cire kambin sarauta ya ɗora wa Hashim, ya ce, "daga yau na mayar da ɗana ya zama Sarki gare ku." Jama'a duka suka ce, "mun yi biyayya!" Hashim kuwa sai kuka yake yi bai samu bakin magana ba.

  Sarki Ibrahim ya kwanta jinya, ɗansa na kula da shi, a kullum yana wajensa. Shi kuma ba abin da yake masa sai nasiha game da al'amarin sarauta da sha'anin jama'a. Bayan kwanaki tara Allah ya karɓi ran Sarki Ibrahimu. Hashim ya miƙe ƙafa a matsayin Sarki, ya mulki jama'a bisa gaskiya da adalci."

  Yaro ya ci gaba da cewa, "to ka gani ya Sarki, idan Allah ya ƙaddara bisa goshina cewa kai ne ajalina, to babu makawa komai wayona da dabarata ko ƙarfina, ban isa na guje maka ba. Ballantana ma ni da yanzu nake hannunka, sai yadda ka yi da ni. Amma ka sani aiki bisa adalci da daidaito shi ne sirrin tabbatar al'umma cikin mulkinsu."

  Da Sarki ya ji wannan labari sai zuciyarsa ta kaɗa ya shiga ruɗani. Ya yi shiru yana tunani. Can an jima ya ce, "ku mayar da shi kurkuku, yanzu dare ya kawo jiki, sai gobe ma duba al'amarinsa. Nufina na aikata masa mummunan kisa, ta yadda zai zama darasi ga masu surutu irinsa, su gane cewa hujja dabam labari dabam."

  RANA TA 10

  Wannan ranar ta kasance ana gudanar da biki na musamman a ƙasar, domin tunawa da ranar da Sarki Shamsuddin ya dawo kan kujerar mulkinsa. Mutanen birnin maza da mata, yara da manya sukan tafi fada gaba ɗaya su gaida Sarki. Su yi masa addu'a suna sake jaddada goyon bayansu gare shi.

  Tun cikin dare Wazirai  suka riƙa bin manyan mutane suna shirya musu abin da za su faɗa wa Sarki game da yaro. Da gari ya waye kowa ya ci ado aka hallara ƙofar fada. Bayan gaisuwa da addu'a sai Sarki Shamsuddin ya ce, "jama'a ko kuna da wata buƙata gare ni?" Sai babbansu, wani dattijo mai yawan shekaru ya miƙe tsaye ya ce, "Allah ya taimaki Sarki, ya tsare shi daga dukan abin ƙi. Mu a wajenmu ka kasance abin yabo, saboda adalcinka da yadda kake hukunci tsakaninmu bisa gaskiya da kyautatawa, kuma ka kasance mai taimakonmu a duk lokacin da muka nemi haka. To amma game da al'amarin wannan yaro, ya Sarki muna ganin ka yi sakaci. Ka bari kullum yana cika maka kunnuwa da hauragiya da soki burutsu, alhali kai ne ka tsamo shi daga halaka, ka mutunta shi, ka gyara halinsa. Amma da yake ɗan jemage ne, ga shi nan ya koma halinsa da ya taso a cikinsa na ƙarya da cin amana. Na tabbata ba ka san abin da jama'ar gari ke faɗa  game da cin amanar da ya yi maka, da kuma sakacin da ka yi a kansa, har yau ba ka yanke masa hukunci ba." Daga nan dattijo ya zauna.

  Sarki ya ja dogon numfashi ya miƙe tsaye ya ce, "ya ku jama'a, haƙiƙa ba na kokwanto ko kaɗan bisa irin ƙaunar da kuke min, kuma kuna kishi bisa duk wani abu maras daɗi da ya same ni. Na gode muku, Allah ya yi muku albarka. Kuma na tabbata bisa ƙarfin ikona, da zan sa a kashe rabin mutanen da ke wurin nan, ba zai wuyata a gare ni ba. To don me zan kasa yanke wa ɗan ƙaramin yaro hukunci? Wanda na tabbata bai wuce sa'an ɗan da na haifa ba? Na ƙyale shi ne ba domin labaran da yake bani ba sai domin na ƙara samun hujjoji masu ƙarfi a kansa yadda babu wanda zai ji wani abu a ransa bayan na zartar da hukuncin kisa a kansa." Daga nan ya sa aka shigo da yaro gabansa. Ya faɗi ya yi gaisuwa Sarki bai amsa ba ya hau magana yana cewa, "kaiconka, duba nan ka gani, duk mutanen nan sun zo gare ni, kuma sun yarda na zartar maka da hukunci bisa abin da ka aikata. A zatonka zan yi biris da maganar su ne na sake ka ka tafi?"

  Yaro ya ce, "Allah ya ba ka nasara, ni dai a iyakacin yarda ta, waɗannan dattijan mutanen kirki ne, babu komai tsakanina da su sai alheri, kuma basu san komai da faruwar lamarin nan ba. Amma waɗannan waziran naka, su ke shirya komai. Na yi imanin ma su ne suka ƙulla wannan makircin a kaina, domin su nuna cewa jama'a duka sun san zancen. Kuma da sannu sharrinsu zai koma kansu. Ga ni dai a hannunka ya Sarki, kamar tsuntsun da ke cikin tarko sai yadda ka yi da ni. Ni dai na yi imani da cewa Allah shi ke da ikon komai, idan ya zartar da abu to babu makawa, komai wuya komai daɗi sai ya faru, a lokacin da ya so, a wurin da ya so, bisa yadda ya so. 

  Shi ɗan adam a kullum yana aikata aibu bisa tsammaninsa na kautar da wani abu da ba ya ƙaunar sa, amma idan Allah ya ce sai abin ya tabbata, to bai isa ya hana ba. Ka ga ɗan Sarki Sulaiman duk da makircin da ya ƙulla wa ɗanuwansa da ɗan ɗanuwansa hakan bai sa ya tabbata a mulki ba lokacin da hukuncin Allah ya zo."

  Sarki ya yi tsaki ya ce, "kai wai ba za ka rabu da surutun nan ba? Faɗa min wane ne Sarki Sulaimanu? Me ya faru ga 'ya'yansa? Yi maza ka faɗa mana kada ka ɓata mana lokaci, domin yau za mu halaka ka." Yaro ya yi murmushi ya ce, "Allah ya ba ka nasara ga labarinsu:

  Ku latsa nan don ci gaban labarin.

  Danladi Z. Haruna

Comments

0 comments