Makalu

Physics: Bayani kan conservation of linear momentum

 • A darasinmu na kimiyya da fasaha a bangaren kimiyyar lissafi (physics) a yau, za mu yi dubi ne zuwa ga maudu'i mai suna conservation of linear momentum. In mai karatu na biye da mu zai ga cewa a durrusanmu da suka gabata mun yi bayani tare da kawo misalai akan linear momentum, za a iya dubawa kafin mu ci gaba. 

  Conservation of linear momentum shima wani law ne wanda aka same shi daga laws guda biyu, wato Newton’s law na biyu da kuma na uku wanda aka fitar da law of conservation a karkashinsu. Ga abinda aka ce game da shi wannan law din:

  Law of conservation state that, when two or more bodies  act upon one another, their total momentum which remains constant, provided no external forces are acting. Dubi wannan don karin bayani.

  Akwai misalai da zamu dauka yanzu wadanda za su taimaka wajen bayanin wannan law din sosai, wadanan misalan daga cikin jarabawar karshe ta gama sakandire zamu dauko su. Kuma misalan zasu nuna mana yadda momentum, velocity da kuma kinetic energy na colliding body  ake lissafinsu.

  Misali na farko                 

  1. An object of mass 5.0kg moving with a velocity of 12ms-1 due North hits a stationary body of mass 7.0. if they stick together after collision and move with velocity v due North, calculate the magnitude of v. NECO 2005

  Akwai abinda ya kamata musani wanda yana da mahimmanci wajen amsa tambaya a karkashin law of conservation,

  Momentum before collision = momentum after collision

  Fig 6.2

  Idan muka duba fig 6.2 ya fitar mana da data da muke bukata sai mu yi amfani da fomula wajan lissafin kai tsaye

   m1 v1 + m2v2 = (m1 + m2 )v

  5×12 + 7× 0 = (5 + 7 )v

  60 + 0 = 12v

  V = 60/12 = 5ms-1

  Misali na biyu

  A tractor of mass 5.0 × 103 kg is used to tow a car of mass 2.5×103 The tractor moved with speed of 3.0ms-1 just before the towing rope becomes taut. Calculate the:

  1. Speed of the tractor immediately the rope becomes taut.
  2. Loss in K.E of the system just after the car has started moving.
  3. Impulse in the rope when it jerks the car into motion. WAEC 2003

  Wannan tambayar ta hada abubuwa uku, velocity, kinetic energy da kuma impulse don haka zamu bi su daya bayan daya mu amsasu kamar yadda aka jera tambayoyin, amma da farko zamu fitar da data tukuna.

  Amsar tambaya       

  Kafin mu fara amsa tambayoyi zamu fara fitar da bayanan da aka bamu daga cikin tambayar, abu na farko shine mass na tractor , m1 = 5.0 × 10kg:  velocity tractor na ainihi , u1 = 3.0ms-1

  Mass na mota , m2 = 2.5 × 10kg;  velocity mota na ainihi , u2 = 0ms-1

  Zamu dauki 'v' a matsayin velocity na mota da tractor

  Gudun tractor a yayinda igiyar ta zama taut shine velocity na tractor da mota a lokacin da dukansu suka fara tafiya.

  Momentum kafin su fara tafiya = momentum bayan sunfara tafiya

  m1u1 + m2u2 = ( m1 + m2 )v

  yanzu zamu dauko a cikin bayanan da muka fitar kowanne mu sa shi a cikin matsayinsa a wannan fomula sannan mu yi lissafinsu.

  5.0 × 10× 2.5 × 103 × 103 × 0 = (5.0 × 103 + 2.5 × 103 × 10)

  1.5 × 104 = 7.5 × 103 v

  v = 1.5 × 10/ 7500 = 2ms-1 

  Loss K.E = final K.E – initial K.E

  A wannan tambayar zamu yi amfani da fomula ta kinetic energy da ta momentum

  initial K.E = K.E na tractor da ke tafiya = ½ m1 ( from KE = ½ mv)

  = ½ 5.0 × 103 × 32  = 2.25 × 104J

  Yanzu mun samo amsar kinetic energy na ainihi saura mu nemo kinetic energy na karshe

  Final energy = K.E na tractor da mota da ke tafiya shine zai zama = ½ (m1 + m2)v2

  = ½ (5.0 × 103 + 2.5× 103 )× 22

  = ½ (7500) × 4 = 15000 = 1.5 × 104J

  Yanzu tunda mun nemo initial K.E da final K.E sai musa su a cikin fomulamu, wato:

  Loss K.E = final K.E – initial K.E

  Loss in K.E = 1.5 × 104 - 2.25 × 104 = - 7500J

  = 7500J

  Negative sign din yayi signifaying loss in K.E

   

  • Impulse = change in momentum

  = final momentum – intial momentum

  = (m1+ m2 )v – (m1u1 + m2u2)

  =7500 × 2 – 1.5 × 104 + 0

  = 1.5 × 104 -1.5 × 104

  = 0Ns ko kuma 0 kgms-1

  Wadannan kadan ne daga cikin misalan lissafi na conservation of linear momentum. Insha Allah a makala ta gaba zan kawo wasu misalan wanda za su gamsar sosai susa a fahimci yadda ake yin kowannensu. Na gode, sai mun hadu a makala ta gaba.

No Stickers to Show

X

MAKALU DA DUMI-DUMIN SU

 • Duk mace na bukatar sanin wadannan abubuwa guda 6 kafin ta yi aure

  Posted Nov 29

  Aure abu ne mai matukar muhimmanci a rayuwar mutum don ya zamo cikar mutuntaka ta dan adam. Allah madaukakin sarki ya halicci mata daga jikin mazaje domin su matan su zama natsuwa a gare su, ya kuma sanya soyayya da shakuwa a tsakanin wadannan jinsin guda biyu.  A...

 • Ko kun san adadin yawan nutrients da jikinku ke bukata?

  Posted Nov 24

  Samun abinci mai kyau da kara lafiya, wato good nutrition, ya dace ya zamo daya daga cikin burin kowani dan adam da ke raye.  Ya kasance mun san adadin yawan abinci mai kyau da jikkunanmu ke bukata, sannan mun san addadin yadda ya kamata mu rinka motsa jikinmu, kum...

 • Yadda ake hada buttered chicken

  Posted Nov 22

  Assalamu alaikum barka da sake saduwa a fannin girke-girkenmu na Bakandamiya. A yau insha Allahu zamu gabatar da shirin yadda za ki hada buttered chicken. Abubuwan hadawa Kaza Ginger and garlic paste (citta da tafarnuwa)  Albasa Yoghurt Butter Fresh cream ...

 • Yadda ake hada papaya drink

  Posted Nov 22

  Assalamu alaikum barka da sake saduwa a cikin shirin Bakandamiya a yau insha Allahu zamu gabatar da shirin yadda za ki hada natural papaya drink Abubuwan hadawa Papaya (gwanda) Sugar Ruwa Zuma (optional) Yadda ake hadawa Farko za ki yanka gwanda ki cire ma...

 • Alamomi 8 da za ki gane cewa namiji da gaske yake

  Posted Nov 22

  So wani irin yanayi ne da kan sa mutum ya tsinci kansa a cikin wani hali na daban. Sai dai mi? Abu ne shi mai dadi a kuma gefe guda abu ne mai matukar ban tsoro. Duk da kasancewar sa hakan bai zama abin ƙyama ga mutane ba. Da yawa kan rungume shi da hannun biyu. A gefe...

View All