Makalu

Physics: Yadda ake lissafin screw

 • A karatunmu na kimiyya da fasaha a gefen kimiyyar lissafi (physics), yau zamu duba daya daga cikin misalan simple machine. In baku manta ba, a baya mun yi bayani akan machine da misalansu. A cikin waccan makala na kawo muku screw a matsayin misalin simple machine, a kan haka ne, a yau zamu dora akan wancan bayanin na mu ta yadda zamu duba ko ince mu koyi yadda ake lissafin screw din.

  Misalan machines da ake kira da suna screw sune:

  1. Bolts and nut
  2. Car screw jack
  3. Engineer’s vice e.t.c

  Gaba daya screw suna da thread. Nisa (distance) dake tsakanin successive thread a jikin screw ana kiransa da its pitch for one complete revolution. Shi screw yana tafiya ne mai nisa wanda yake dai-dai da its pitch.

  Hakkin mallakar hoto: notesandsketches

  Yanzu zamu ga yadda ake samo formula da ake amfani da ita wajen lissafin screw.

  Work done = work output

  Effort × distance moved by effort = load × distance moved by load.

  Effort × circumference of handle = load × pitch

  E × 2πr = L × p

  Hence , the velocity ratio

  V.R = 2πr/p

  For a perfect friction-less screw , M.A = V.R

  Hence , M.A = V.R = 2πr/p

  For a screw jack, "r" shine length na handle ko tommy bar na screw jack.

  Yanzu zamuyi amfani da wadannan fomulolin domin amsa tambayoyi wanda zamu dauko daga jarabawan karshe tagama sakandire wato WAEC.

  Tambaya ta Farko:

  1. A screw jack whose pitch is 4.4mm is used to raised a body of mass 8000kg through a height of 20cm. The length of the Tommy bar of the jack is 70cm. If the efficiency of the jack is 80%, calculate:

  1. The velocity ratio of the jack
  2. Mechanical advantage of the jack
  • Effort required in raising the body
  1. Work done by the effort in raising the body [ = 10ms-2 ; π = 22/7] (WAEC 1993)

  Amsar tambaya:

  Yanzu zamu fara fitar da abubuwan da aka bamu kafin mu fara amsa tambayoyin kai tsaye.

  Data:

  Pitch, p = 4.4mm = 0.0044m;

  Mass, m = 8000kg; g = 10m/s2

  Load, L = mg = 800 × 10 = 80000N

  Distance load moved, l = 20cm = 0.2m;

  Length of Tommy bar, r = 70cm = 0.7m;

  Efficiency, £ = 80%

  A tambayar farko an bukaci muyi lissafin velocity ratio na jack din don haka zamu yi amfani da formula mu da muka samo, ga ta kamar haka: V.R = 2πr/p

  1. The velocity ratio, V.R = 2πr/p = [ 2 × 22/7 × 0.70 ] / 0.0044 = 4.4 / 0.0044 = 1000
  2. Ana bukatar mu nemo mechanical advantage na jack, daga £ = M.A/V.R × 100% zamu samu

  Mechanical advantage, M.A = £ × V.R/100 = 80 × 1000 / 100 = 800

  • Effort required in raising the body , M.A = load/effort = L/E     Effort = L/ M.A = 80000/800 = 100N
  1. Work done by effort = work input

  Efficiency = work output /work input × 100%

  Work input = work output/efficiency × 100%

  = load × distance moved by load / efficiency × 100%

  = load × distance moved by load / efficiency ×100%

   = L × l × 100 / £ = 80000 × 0.2 × 100 / 80

  = 1600000 / 80 = 20000J = 20KJ

  Tambaya ta Biyu:

  1. A screw jack with a Tommy bar of length 12cm is used to raise a car through a vertical height of 25cm by turning the Tommy bar through 50 revolution. Calculate the approximate velocity ratio of the jack. [ π = 3.14 ] (WAEC 2001 /2014)

  Amsar tambaya:

  Data:

  Length of Tommy bar , r = 12cm;

  Number of revolution, n = 50

  Height raised or distance load moved,  h = 25cm;

  Therefore, pitch , p = h/n = 25cm / 50 = 0.5cm

  Velocity ratio, V.R = 2πr / p = 2 × 3.14 ×12cm / 0.5cm = 75.36cm / 0.5 = 150.72 approximately 151

  Wannan shine kadan daga cikin misalan yadda ake lissafin screw. Da fatan mai karatu ya karu da wannan darasin. Sai mun hadu a makala na gaba, amma kafi nan, mai karatu na iya duba makalunmu na baya, kamar:  Yadda ake lissafin inclined plane da pulley machine da makamantansu.

No Stickers to Show

X

MAKALU DA DUMI-DUMIN SU

 • Duk mace na bukatar sanin wadannan abubuwa guda 6 kafin ta yi aure

  Posted Nov 29

  Aure abu ne mai matukar muhimmanci a rayuwar mutum don ya zamo cikar mutuntaka ta dan adam. Allah madaukakin sarki ya halicci mata daga jikin mazaje domin su matan su zama natsuwa a gare su, ya kuma sanya soyayya da shakuwa a tsakanin wadannan jinsin guda biyu.  A...

 • Ko kun san adadin yawan nutrients da jikinku ke bukata?

  Posted Nov 24

  Samun abinci mai kyau da kara lafiya, wato good nutrition, ya dace ya zamo daya daga cikin burin kowani dan adam da ke raye.  Ya kasance mun san adadin yawan abinci mai kyau da jikkunanmu ke bukata, sannan mun san addadin yadda ya kamata mu rinka motsa jikinmu, kum...

 • Yadda ake hada buttered chicken

  Posted Nov 22

  Assalamu alaikum barka da sake saduwa a fannin girke-girkenmu na Bakandamiya. A yau insha Allahu zamu gabatar da shirin yadda za ki hada buttered chicken. Abubuwan hadawa Kaza Ginger and garlic paste (citta da tafarnuwa)  Albasa Yoghurt Butter Fresh cream ...

 • Yadda ake hada papaya drink

  Posted Nov 22

  Assalamu alaikum barka da sake saduwa a cikin shirin Bakandamiya a yau insha Allahu zamu gabatar da shirin yadda za ki hada natural papaya drink Abubuwan hadawa Papaya (gwanda) Sugar Ruwa Zuma (optional) Yadda ake hadawa Farko za ki yanka gwanda ki cire ma...

 • Alamomi 8 da za ki gane cewa namiji da gaske yake

  Posted Nov 22

  So wani irin yanayi ne da kan sa mutum ya tsinci kansa a cikin wani hali na daban. Sai dai mi? Abu ne shi mai dadi a kuma gefe guda abu ne mai matukar ban tsoro. Duk da kasancewar sa hakan bai zama abin ƙyama ga mutane ba. Da yawa kan rungume shi da hannun biyu. A gefe...

View All