Featured Create an Ad

Makalu

Blogs » Ilimin Kimiyya » Physics: Darasi game da general gas law

Physics: Darasi game da general gas law

 • A makala ta da ta gabata wadda na fara bayani dangane da Gas Law mun koyi mene ne gas law, sannan kuma mun ga yadda ake siffanta gas tare da abubuwa guda uku wato, da volume, da temperature da kuma pressure. Daganan na yi rubutu akan laws din gas guda uku wanda kowannensu yana dauke da bayani dangane da samuwarshi da kuma yadda ake lissafinshi a saukake. Wadannan laws din sune, Charle’s Law, da Boyle’s Law, da kuma Pressure Law. Mai karatu na iya duba su don tunatarwa kafin mu ci gaba da wannan karatun.

  A yau kuma zamu yi karatunmu ne a karkashin law wadda ta kunshi gaba daya laws din gas guda uku. Wannan law ba wata ba ce face GENERAL GAS LAW wadda akan kira da IDEAL GAS. Ga formulars na Pressure law, Charle’s law da kuma Boyle’s law, don tuni da kuma saukin aiki, kafin mu fada gadan-gadan kan maudu'in na mu.

  Ga pressure law:

  P α T or P / T = constant

  Sannan kuma, P1 / T1 = P2 / T2.

  P1 = initial gas pressure

  T1 = initial gas temperature

  P2 = final gas pressure

  T2 = final gas tempressure.

  Yana da kyau mu sani cewa idan zamu yi lissafi a karkashin pressure law in aka bamu temperature in degree Celsius (0C) sai mun canza shi zuwa Kelvin . Dubi cikakken bayani akan pressure law a wannan makala.

  Ga Charle’s law:

  V α T or V / T = constant

  Don haka zai zama V1 / T1 = V2 / T2 

  V1 = initial volume

  T1 = initial absolute temperature

  V2 = final volume

  T2 = final absolute temperature

  Wanda V1 da T1 initial volume ne da initial temperature wato volume da temperature na farko ko muce na ainihi, wanda kuma V2 da T2 sune final volume da final temperature na gas gaba daya.

  Akwai abinda ya kamata mu sani wajen lissafin Charles law shine temperatures are absolute temperatures ana measuring dinsu da Kelvin ne ba da ?C ko ?F. Kuma yana da kyau  koda yaushe a rika converting ?C zuwa K ta hanyar adding 273. Za a iya duba karin bayani akan wannan law din a nan

  Ga bayani da formula Boyle’s law:

  Boyle’s law states that volume (V) of a fixed mass of gas is inversely proportional to its pressure , provided the temperature remains constant.

  Wannan shine law din wanda yanzu zan kawo yadda ya ke a karkashin formula wato yadda za a samu saukin aiki da shi wajen lissafi.

  V α 1/P, yana nufin volume is inversely proportional to the pressure.

  PV = K, wannan yana nufin pressure ayi multiplyin din shi da volume zai zama constant k, wanda P tana matsayin pressure na gas, V tana matsayin volume na gas, sai kuma k yana matsayin constant. Dubi karin bayani akan Boyle’s law anan.

  Bayan mun ga bayanai da kuma formulolin na wadannan laws guda uku na gas, yanzu zamu je kai tsaye ga general gas law. A Turance akanyi bayaninsa a matsayin, a combination of boyle’s, charle’s and pressure laws results in the general gas law for ideal gas. Wato dai anan dai wannan law din hadakan wa’yancan laws guda ukun ne, suka hadu suka zama general law for ideal gas.

  That’s PV / T = constant

  Therefore, P1V1 / T1 = P2V2 / T2

  Yanzu zamu dauki misali mu yi lissafinshi wanda ya kunshi gas laws dukka.

  Misali na daya:

  At what value of X,Y, and Z is the equation, PxVyTz = constant, a statement of

  Charles’s law

  Boyle’s law

  Pressure law

  General gas law

  Amsar Tambaya:

  Wannan tambayar ana son mutabbatar da a wane law ne wannan statement din ya ke aiki a cikinsu. Duba da abinda aka bamu hakan yasa zamu dauko daga cikin laws na indices mu yi applying don solving problem din (further maths)

  1 /X = x-1

  X = X1

  X0 = 1

  Yanzu zamu dauki laws din muyi proving mu gani.

  Charle’s law, V / T = constant

  V / T = V1 / T1 = V1T-1

  Therefore, PxVyTz becomes P0V1T-1   or 1× V1T-1 = V / T

  Therefore, for x= 0 , y = 1 z = -1, PxVyTz   = constant is Charles’s law (any term P,V or T which is not present in the equation is assigned a superscript of zero, hence P0), tunda babu P a cikin equation din don haka wannan statement ba na charles’s law bane.

  Boyle’s law: PV = constant

  PV = P1V1

  Therefore, PxVyTz becomes P1V1T0 or P1V1 = Therefore, for x = 1, y = 1 and z = 0,

  PxVyTz = constant is Boyle’s law.

  Pressure law: P / V = constant

  P / V = P1 V1 / T1 = P1V1T-1

  PxVyTz becomes P1V1T-1   = PV / T

  Therefore, for x = 1, y = 1 and z = -1, PxVyTz = constant is general gas law.

  Tun da mun amsa tambaya wanda ke dauke da dukkanin gas laws din yanzu zamu dauki misali wanda yana karkashin general law ne kawai mu ga yadda ake lissafi da ideal gas formula.

  Misali na biyu:

  The volume and pressure of a given mass of gas at 270 C are 76cm3 and 80cm of mercury respectively. Calculate its volume at STP  WAEC 2000

  Amsar Tambaya:

  00C (273K) and 760mmHg (1.013 × 105 Nm-2 are called standard temperature and pressure, usually abbreviated as S.T.P

  Data

  Initial gas volume, V1 = 76cm3

  Final gas volume, V2 = ?

  Final gas temperature, T2 = 273K

  Initial Pressure, P1 = 80cmHg

  Initial gas temperature, T1 = 270C = (27 + 273) = 300K

  Final gas pressure, P2 = 760mmHg = 76cmHg

  Yanzu za mu dauki data dinmu da aka bamu musa su cikin ideal gas equation

  P1V1 / T1 = P2V2 / T2 we have, 80cm Hg × 76cm3 / 300K = 76cmHg × V2 / 273K

  Therefore V2 = 80cm Hg × 76cm3 × 273K / 76cmHg × 300K = 72.8cm3

  Wannan shine karshen wannan makala, sannan kar a manta kamar kullum, ina kara jan hankalin dalibai su rika neman wasu textbook din physics domin kara neman sani da kuma fahimta sosai. Allah Ya bamu sa’a, amin.

  Hakkin mallakar hoto (photo credit): lumen learning

No Stickers to Show

X

Da Dumi-Dumin Su

 • Cutar mantuwa na Alzheimers dai cuta ce da ita ce gaba-gaba wajen janyo cutar nan na dementia kuma ita ce ta fi yawa a cikin ire-iren cutar neurodegenerative disorders. Cututtukan neurodegenerative disorders wasu cututtuka ne da suka shafi rashin yin aiki ko matsala na wani bangare na kwakwalwa. A k...
 • Ku latsa nan don karanta babi na bakwai. Zare hannunta ta yi daga riƙon da ya yi mata ta ce "Wai lafiya ya Habeeb?" Idanunsa da suka fara kaɗawa izuwa launin ja ya buɗe a hankali, tare da jifar ta da wani mayen kallo, wanda sai da jikinta ya ɗan yi sanyi. "Fateema" ya kira sunanta cikin kasalalli...
 • Thu at 7:22 PM
  Posted by Bakandamiya
  Ku latsa nan don karanta babi na bakwai. Bata iya komawa bacci ba tunda ta tashi daga wannan mafarkin. Ta yi kuka har sai da idanunta suka fara yi mata zafi, gangar jikinta da zuciyarta suna yi mata rad'ad'in da ita kad'ai ta san yanda take ji. Ƙirar sallahr asuba yasa ta mik'e cikin hanzari, tana...
 • Mece ce cutar mantuwa (amnesia)? Idan aka ce mutum na fama da cutar amnesia dai to ana nufin cutar da ke sa mutum ya manta abubuwa kamar abubuwan da su ke zahiri, da kuma bayanai game da wani abu ko kuma manta abinda ya faru da su da makamanta ire-iren wannan mantuwa. Mutane da su ke dauke da wanna...
 • Ku latsa nan don karanta labarin Saurin Fushi Na Kawo Da Na Sani. A wani ƙauye akwai wani mutum  ana kiran sa Abu Sabiru, ya kasance mai tsananin haƙuri da kawar da kai akan wasu al’amura. Dalilin da ya sa ma ake kiransa Abu Sabiru kenan. Yana zaune tare da matarsa kyakkyawar gaske ...
 • Ku latsa nan don karanta darasin rana ta uku. DARASI NA 1 Matakan rubutun gajeren labari A jiya mun yi bayani akan matakan da ake bi wajen tsara labari, yau kuma za mu bayani a takaice kan matakan da ake bi wajen rubuta ingantaccen labari. Waɗannan matakai ba tabbatattu ba ne, ma'ana ba wajibi ne...
View All