Makalu

Illolin yawon bariki

 • Idan aka ce bariki ana nufin karuwanci wanda wannan al’ada ta banza ita tai tashin gwauran zabi a wannan zamani. Abin ya kai ga ba banbanci tsakanin matan aure da zawarawa da kuma yammata, gaba daya an dulmiya. A zamanin da wadanda aka fi sani da yin wannan sha'ani sune manyan mata ko zawarawa wanda suka fi Karfin iyayensu. Wa 'yannan matan kan bar garuruwansu don komawa zaman kansu ko gidan karuwai. Dubi illolin amfani da magungunan mata ga mace

  Abin tashin hankali a wannan zamani shi ne yarinya ta na gidan iyayenta take yawon bariki. Kai bama anan gizon ke sakar ba, wata fa mahaifanta sun san da hakan kuma da kudin take ciyar da su.  Sabo da tsabar son abin duniya, irin wa'yannan iyaye ba su damu da tarbiyya ko kwaba 'ya'yansu ba, su dai kawai abinda suke samu a wajen irin wa'yannan 'ya'ya shi ya dame su.

  Wannan abin takaici ya kai ga yanzu in an tura yara makarantun jami’a don karatu, sai su zarce su zamo kananan karuwai a wannan gari da aka tura su, kai Allah wadaran wannan masifa! Har ila yau,  yanzu mata kanyi zaman kansu a garinda iyayansu suke, ba sai sun bar gari ba, wa iyazu billah! kaico da wannan rayuwa! Ga wasu daga cikin illolin tura mata makarantun kwana.

  Wai me ke jawo wannan fitina ne? Kuma me ne ne mafita?

  Abubuwan dake jawo hakan

  • Rashin kulawar iyaye
  • Talauci
  • Son abin duniya
  • Kwadayi
  • Zama da kawayan banza

  Tabbas iyaye na taka rawa babba a wannan fanni. Za ka ga mutum ya tura diyarsa a makaranta amma ya kasa bata kudin da zata magance matsalolinta na yau da kullum. Wani kuwa bai damu da kula da irin kawayen 'ya'yansa ba. In ba'ayi sa'a ba sai yarinya ta gamu da kawaye masu gurbataccen tarbiya inta biye musu a hankali sai kaga yarinya ta shiga yawon bariki, subhanallah!

  Akwai kuma wanda babu ke sa su hakan, domin kwata-kwata zuciyar mahaifansu sun mutu ba za su jajurce wajen nemowaba sai su maida yaransu a baben kasuwanci suna samun kudi ta hanyarsu. Kai wasu iyayenma koda diyarsu ta samu mutum nagari zai aureta sai su hanashi don wata kila baida kudi, amma da mai kudi yazo har barinta ake tana shiga motarsa suna fita duk inda su ke so, saboda yana basu. Daganan a ba ta mata rayuwa shikenan ta zama karamar karuwa.

  Sannan wata matsalar kuma wadda idan kaddara ta fada wa yarinya ta samu ciki ko dai ta hanyar fyade ko yaudararta da a kayi, sai ka ga iyayanta sun kyamaceta wasu ma su koreta, hakan sai ya sa ba tada wani madogara face ta tafi ta kama iyayen bariki, shikenan ta fada hanyar bariki.

  Illolin bariki

  • Yana jawo rasa daraja da mutuncin 'ya mace
  • Yana sawa mace kai har ma namiji ta dauko cututtuka
  • Yana lalata rayuwar mace gaba daya, ta kare a wulakance
  • Kuma kudin da ake samu ta wannan hanyar ba su da albarka

  Jan hankali

  Ina mai jawo hankalinku 'yanuwana mata akan jajircewa wajen ganin komin wahala ba ku bari rayuwarku ta wulakantaba. Ku yi hakuri da yanayin da kuka tsinci kanku, bayan wuya an ce sai dadi. Sannan ku sani rayuwar 'yamace gajerace, don haka muyi kokarin kiyayewa mu koma ga Allah domin shi ne mai bayarwa da kuma hanawa. Don haka ba mai azurta ki sai Shi. Sabo da haka mu dage da addu’a.

  Kuma iyayenmu mata ina kara baku shawara akan sufa yarannan na ku amanace gareku. Kuma ku sani ba ku kuka haliccesuba da zaku mai da su bayi ko kuma ince saniyar tatsa. Ku sani, wallahi Allah sai ya tambayeku yadda kuka tarbiyartardasu.

  Allah Ya sa mu gane mu gyara, amin.

No Stickers to Show

X

MAKALU DA DUMI-DUMIN SU

 • Jini Baya Maganin Kishirwa: Babi na Uku

  Posted Jan 12

  Ku latsa nan don karanta babi na biyu. Sakinah ta share hawayen da ke zuba kan kuncinta kafin ta ce. "Insha Allahu Umma zan yi aiki da dukkan abin da ki ka umarce ni da shi da yardar Allah, ba zan taɓa baki kunya ba". "Yauwa Sakinah Allah ya yi miki albarka". "Amin"...

 • Yadda ake baked awara

  Posted Jan 11

  Barka da sake saduwa a cikin shirin girke-girkenmu na Bakandamiya. A yau na zo maku da sabon girki wato yadda za ku hada baked awara. Abubuwan hadawa Awara Kwai Carrots Seasoning Cooked minced meat Muffin tray Albasa Yadda ake hadawa Farko za ki yanka a...

 • Bayanan masana game da ingantattun hanyoyin ƙayyade iyali

  Posted Jan 8

  Mene ne ƙayyade iyali? Ƙayyade iyali ko tazarar iyali ko kuma family planning a Turance wani mataki ne da ma'aurata kan dauka don hana mace daukan ciki domin rage yawan haihuwa akai-akai, ko ƙayyade yawan ‘ya’ya da za ta haifa ko dai ma don wasu dalilai na ...

 • Ma'aurata: Babi na Biyu

  Posted Jan 8

  Idan baku karanta babi na daya ba to ku latsa nan don karantawa. Ana kiran sallah asuba ta farka daga bacci addu'an tashi daga bacci tayi kafin tayi miƙa tana salati ga Annabi S.A.W kai dubanta tayi a gefen da Fahad yake kwance tayi, har yanzu yana nan yana bacci kamar...

 • Burina a shekarar 2020: Saurare na ya fi magana ta yawa

  Posted Jan 4

  Masana sun ce daga cikin abubuwan da suka sa dan Adam yin galaba a kan sauran halittu shi ne yadda yake iya hada kai. Don mutum shi kadai ba zai iya gwada karfi da zaki ko giwa ba. Amma idan ya hada karfi da sauran ‘yan uwansa babu kalubalen da ba za su iya t...

 • Yadda ma’urata ya kamata su bullowa matsalolin rashin lafiya idan sun taso a rayuwar aure

  Posted December 31, 2019

  Matsalar rashin lafiya matsala ce babba da ke taka muhimmiyar rawa wajen hargitsa zamantakewa da rayuwar iyali. Ba abu bane da mutum daya zai boye ma kansa ba tare da sanin aboki ko abokiyar zama ba. Saboda matsala ce babba da take bukatar shawara, tattaunawa a tsakanin...

View All