Makalu

Blogs » Zamantakewa » Rashin kulawa da tarbiyyar da namiji ba ya gyara na 'ya mace

Rashin kulawa da tarbiyyar da namiji ba ya gyara na 'ya mace

 • Kamar yadda kowa yasani tarbiyya tana farawa daga gida ne, musamman daga mahaifiya sannan kuma jigo mahaifi. Malaman makaranta da al'umma unguwa ko gari na taka babbar rawa a tarbiyyantar da yara. Sai dai kaico! A wannan zamanin an sama nakasu daga kowane bangare na tarbiyya, musamman TARBIYYAR DA NAMIJI, wanda shine a yau wannan makala tawa zata yi tsokaci a aki.  Mai karatu na iya duba rushe tarbiya ta duniyar yanar gizo.

  A wannan zamani, bisa dukkan alamu hankalin iyaye wajen kula da tarbiyar 'ya'yansu, kaso mai yawa, ya koma kan 'ya'ya mata wanda har ya janyo tabarbarewar tarbiyar 'ya'ya maza. Saboda wanna dalili sai ka ga wasu iyaye sun manta da wadanne irin abokanai dansu ke yawo ko zama da su; ba harkan abokai ba, kacokam sai su manta da irin halin da dansu ke ciki, musamman a lokacin da girma ya zo ma sa.

  Akwai abubuwa da dama a wannan zamani dake janyo rasa tarbiyyar da namiji:

  • Rashin kulawar mahaifi
  • Shagwaba yara ta hanyar kin nuna musu kuskurensu
  • Sangartasu tun suna yara ta yadda zai zama basu jin maganar mahaifiyarsu
  • Rashin sa ido ga iliminsu na addini
  • Rashin sanin irin makarantun da ake kaisu na ilimin boko

  Wadannan sune kadan daga cikin abubuwanda ke jawo rasa tarbiyyar da namiji.

  Tabbas tarbiyar da namiji na da wuya kuma yawanci ya rataya ne a wuyan mahaifinsa sakamakon mahaifiya koda yaushe tana gida, kuma idan yaro ya kai wani munzili dole zai zamana ya dan nisanta daga cikin gida. Maihaifi shi ke tare da shi a waje, kuma shi zai iya sanin halin da ya ke ciki a wajen. Har ila, shi yasa za ku ga da namiji yafi jin ko tsoron maganar mahaifinsa.

  Sau da dama, zaku ga iyaye maza din kuma saboda hidima na yau da kullum da ya yi musu yawa, sai kaga an samu nakasu wajen kulawa da yara.

  Jawo hankali

  Yana da muhimmanci iyaye maza su sani hakki ne a kansu da su sa ido ga yaransu ta kowani bangare ta yadda za su sami ingantaccen rayuwa, haka suma su zama iyaye nagari. Har ila yau, yana da kyau iyaye maza su kyautata dabi’unsu ta hanyar mu’amalarsu ta yau da kullum da iyayan yaran mata harma da mutanen gari, domin wasu yaran suna kallo yadda mahaifinsu ke zagin mahaifiyarsu haka suma ba za su taba ganin darajar matansu idan sun yi aure. Yaro har kullum yana koyi ne da abinda ya tashi ya gani ana yi a gidansu ko unguwarsu ko kuma garinsu.

  Daga karshe, zan so na kara jaddada cewa, lallai fa tarbiyar yaranmu ya rataya ne akanmu mahaifa, wajibe ne kuma amana ce Allah Ya dora mana, don haka dole mu dauke shi da muhimmanci. Idan yayanmu su ka yi kyau a'ummarmu baki daya zata gyaru. Kuma wajen kula dole mu kula da tarbiyar da na miji tamkar yadda muke kula da na mace. Dukkaninsu 'ya'yanmu ne kuma suna bukatar kulawarmu. Dubi shawarwari guda 8 don inganta tarbiyar yara.

Comments

1 comment