Makalu

Matsalolin auren hadi a yau

 • Auren hadi wannan aure ne da yawanci iyaye ke hadawa tsakanin 'ya'yan abokansu ko 'yanuwansu ko kuma su aurama 'yarsu duk wanda yazo ta hannunsu ba tare da ra'ayin yaran nasu ba. Kai harma wasu iyayen aurar da 'ya'yansu su keyi ga tsofaffi sa'anninsu (iyayansu). Shi wannan ɗani'a na auren hadi na daga ciki matsalolinmu a wannan zamani wanda ya ke cike da rudani dangane da zamantakewa ta aure data yau da kullum. A wani bangaren kuma dubi wannan makalar da ta yi magana akan rike sirri shi ne ginshikin zaman aure.

  A binma ya fi muni wajen illata zuciyoyin kananan mata da kuma dasa musu cuta wadda tafi karfin shekarunsu. Ba ma anan gizo ke sakarba, sai ma ya zamanto wasunsu sun debi wata mummunar al'ada wadda hanya ce ta gurbacewar tarbiyyar data samu daga gidansu. wanda batai hakan ba sai dai agidan mazajensu wa iya zubillah. Wasunsu sukan shiga halin ha'ula'i a sakamakon shi wannan aure na hadi, amma sukan barshi a zuciyarsu saboda dalilai da dama. An ce "mai daki shi yasan inda ruwa ke zubar masa", tabbas hakane domin zuciya tamkar kabari ce na ciki yake fama.

  A yau mata dayawa na cikin matsananciyar rayuwa dangane da wani hali da suka shiga saka makon biyayya ga ra'ayin iyayansu. Tirkashi wannan aure ya zama cutarwa ga mata da yawa dukda addini ya bama iyaye damar su zaba ma yaransu mata miji nagari. Amma in ka lura a wannan zamanin hakan suna yinsa ne sabo da abin duniya ko kuma wani manufa tasu ta daban. Sau dayawa wannan lamari ya kan jefa mata a halin ni 'yasu, su kuma iyayen sanin cewa yaran basa son wadannan mazaje da aka hada su, koda ana cutar dasu ba sa sauraronsu, koda sun kawo kara ne, sai su ce aidama can bata son shi karya take.

  Matsalolin da auren hadi ke jawowa, sun hada da:

  • Hawan jini
  • Ciwon zuciya
  • Zaucewa
  • Tsanar aure
  • Zina da aure

  Wadannan kadanne daga ciki sabo da kodayaushe yarinya tana cikin damuwa domin kiyayyar dake zuciyarta akan mijinta. Jawo hankali ga iyaye; inayi wa iyaye tuni akan suji tsoron Allah su sani duk halinda yaransu suka shiga akwai hakki akansu sannan idan har sun musu irin wannan auren su dinga jawo su a jiki su ji damuwarsu tare da yi musu nasiha bakawai su watsar dasu ba. Sannan gare ku mata, ku dinga sassauta tsanar mazajanku ku rungumi kaddara da sanin matar mutum kabarinsa, wata bata auren mijin wata. Ku jajirce, in har Allah Ya dora muku irin wamnnan auren, ta yin la'akari da cewa sunnar manzon Allah s.a.w kuke kai. Ku tsarkake zuciyarku ku kyautata ma mazajanku insha Allah ba za kuji kunyaba duniya da lahira.A akwai matanda wannan kiyayya da shedan ke sawa su fada wani hali mara kyau wanda sakamakon rashin tawakkali ke jawo haka.

  Gare ku maza ku rage tirsasama mata akan sai sun aureku koda basu sonku domin gudun haifar dan da bashida ido, kuma ku rike amanarsu a hannunku kun in har Allah Yayi kunyi auren. Kun rabo su da iyayansu sannan kuma kuna kuntatamusu, hakan yakansa su shiga yanayin tsoronku da damuwa wadda zata saukarmusu da ciwo. Kar ku yawanta hantararsu ba kuna cin zalinsu kuji tsoron Allah. Kuyi kokarin kwantar musu da hankali domin mace bata da wahalar shakuwa koda batasonka da farko za tafara inhar ka iya da ita.

  Daga karshe fatanmu shi ne, al'umma za su taru wurin magance wannan matsalar don ceto mata dake cikin wannan yanayi mai cutarwa da wahalarwa.  Allah ya sa mu gyara ameen. Dubi makalar da ta yi bayani akan dalilan yawan sake saken aure da masha'a a afirka da kuma sirratattun matsaloli dake kawo cikas a shimfidar aure.

No Stickers to Show

X

MAKALU DA DUMI-DUMIN SU

 • Nakasar Zuci

  Posted Dec 7

  "Ki tafi gidanku na sake ki!" Runtse idanu na yi jin sautin muryar Adamu a kaina, yana furta kalaman da suka kusan sanya ni haihuwar cikin da ke jikina. Da sauri na dago jajayen idanuwana da suka gajiya da kuka na sauke a saitin sa. Wani irin tashin hankali da ciwon r...

 • Duk mace na bukatar sanin wadannan abubuwa guda 6 kafin ta yi aure

  Posted Nov 29

  Aure abu ne mai matukar muhimmanci a rayuwar mutum don ya zamo cikar mutuntaka ta dan adam. Allah madaukakin sarki ya halicci mata daga jikin mazaje domin su matan su zama natsuwa a gare su, ya kuma sanya soyayya da shakuwa a tsakanin wadannan jinsin guda biyu.  A...

 • Ko kun san adadin yawan nutrients da jikinku ke bukata?

  Posted Nov 24

  Samun abinci mai kyau da kara lafiya, wato good nutrition, ya dace ya zamo daya daga cikin burin kowani dan adam da ke raye.  Ya kasance mun san adadin yawan abinci mai kyau da jikkunanmu ke bukata, sannan mun san addadin yadda ya kamata mu rinka motsa jikinmu, kum...

 • Yadda ake hada buttered chicken

  Posted Nov 22

  Assalamu alaikum barka da sake saduwa a fannin girke-girkenmu na Bakandamiya. A yau insha Allahu zamu gabatar da shirin yadda za ki hada buttered chicken. Abubuwan hadawa Kaza Ginger and garlic paste (citta da tafarnuwa)  Albasa Yoghurt Butter Fresh cream ...

 • Yadda ake hada papaya drink

  Posted Nov 22

  Assalamu alaikum barka da sake saduwa a cikin shirin Bakandamiya a yau insha Allahu zamu gabatar da shirin yadda za ki hada natural papaya drink Abubuwan hadawa Papaya (gwanda) Sugar Ruwa Zuma (optional) Yadda ake hadawa Farko za ki yanka gwanda ki cire ma...

 • Alamomi 8 da za ki gane cewa namiji da gaske yake

  Posted Nov 22

  So wani irin yanayi ne da kan sa mutum ya tsinci kansa a cikin wani hali na daban. Sai dai mi? Abu ne shi mai dadi a kuma gefe guda abu ne mai matukar ban tsoro. Duk da kasancewar sa hakan bai zama abin ƙyama ga mutane ba. Da yawa kan rungume shi da hannun biyu. A gefe...

View All