Makalu

Idan kana son rayuwarka ta yi albarka: Kula da tsofaffi

 • Da anyi maganar tsufa wannan yana nuna cewa shekaru sun tsala kenan, wasu na ganin shekarun tsufa kan fara ne daga shekara sittin (60), wasu kuma suna fadin cewa tsufa (musamman a wajen mace) na farawa ne daga shekara hamsin(50) ko hamsin da biyar(55).

  Sabo da tsofaffi sun yi gwagwarmaya iri iri a rayuwarsu na duniya, sun ga faruwan abubuwa da dama da ya amfanesu harma da akasin hakan. Sabo da haka sun fahimci makamar rayuwa ta yau da gobe. Sabo da aukuwan al'amura bisa idanunsu wani bayan wani,sun tara ilmi da sani da kwarewa wajen hangen nesa.

  Muhimmancin su a cikin al’umma

  Babu ko tantama, tsofaffi suna taka rawar gani a al'ummar da suke cikinta. Tsofaffi ne ke aza  yara da manya bisa hanyoyi na gari kyawawa wajen basu shawarwari nagartattu da zasu amfane su a harkokinsu na yau da kullum. Sukan dauki matsayin alkalai a cikin gidajensu da unguwanninsu da garuruwansu, musamman tayin sulhu da sasanta tsakani.

  Tallafa musu wajibi ne

  Don muhimmancinsu mafi yawan al'umman duniya sukan ba tsofi girma. Yara da manya kan ba tsofaffi girma da daraja a matsayin su na tsofaffi, da taimakonsu da akini karfi. Misali in ka duba tashen nan da aka yi wa lakani da “Tsoho da Gemu,” za ka ga yadda ake mutunta tsoho a cikin al’umma. Ga tashen:

  Tsoho da gemu
  Ya tsufa
  Baban su Alhassan
  Ya tsufa
  A tallafa mashi 
  Ya tsufa 
  A agaza masa 
  Ya tsufa 
  A ba shi sadaka 
  Ya tsufa. 

  Ko ta wannan wasan tashe mun san cewa tsofaffi suna da muhimmanci a cikin mu,
  Kuma wannan wasan tashen yana dasa kyakkyawar dabi'ar nan ta tallafawa mutumin da ya tsufa wanda karfinsa ya kare.
  Muna rokon ALLAH ya bamu ikon tallafawa tsofaffinmu. 

  Sannan mai karatu na iya duba: Ba abinda gaggawa ke haifarwa a rayuwa sai dan da na sani

No Stickers to Show

X

MAKALU DA DUMI-DUMIN SU

 • Nakasar Zuci

  Posted Dec 7

  "Ki tafi gidanku na sake ki!" Runtse idanu na yi jin sautin muryar Adamu a kaina, yana furta kalaman da suka kusan sanya ni haihuwar cikin da ke jikina. Da sauri na dago jajayen idanuwana da suka gajiya da kuka na sauke a saitin sa. Wani irin tashin hankali da ciwon r...

 • Duk mace na bukatar sanin wadannan abubuwa guda 6 kafin ta yi aure

  Posted Nov 29

  Aure abu ne mai matukar muhimmanci a rayuwar mutum don ya zamo cikar mutuntaka ta dan adam. Allah madaukakin sarki ya halicci mata daga jikin mazaje domin su matan su zama natsuwa a gare su, ya kuma sanya soyayya da shakuwa a tsakanin wadannan jinsin guda biyu.  A...

 • Ko kun san adadin yawan nutrients da jikinku ke bukata?

  Posted Nov 24

  Samun abinci mai kyau da kara lafiya, wato good nutrition, ya dace ya zamo daya daga cikin burin kowani dan adam da ke raye.  Ya kasance mun san adadin yawan abinci mai kyau da jikkunanmu ke bukata, sannan mun san addadin yadda ya kamata mu rinka motsa jikinmu, kum...

 • Yadda ake hada buttered chicken

  Posted Nov 22

  Assalamu alaikum barka da sake saduwa a fannin girke-girkenmu na Bakandamiya. A yau insha Allahu zamu gabatar da shirin yadda za ki hada buttered chicken. Abubuwan hadawa Kaza Ginger and garlic paste (citta da tafarnuwa)  Albasa Yoghurt Butter Fresh cream ...

 • Yadda ake hada papaya drink

  Posted Nov 22

  Assalamu alaikum barka da sake saduwa a cikin shirin Bakandamiya a yau insha Allahu zamu gabatar da shirin yadda za ki hada natural papaya drink Abubuwan hadawa Papaya (gwanda) Sugar Ruwa Zuma (optional) Yadda ake hadawa Farko za ki yanka gwanda ki cire ma...

 • Alamomi 8 da za ki gane cewa namiji da gaske yake

  Posted Nov 22

  So wani irin yanayi ne da kan sa mutum ya tsinci kansa a cikin wani hali na daban. Sai dai mi? Abu ne shi mai dadi a kuma gefe guda abu ne mai matukar ban tsoro. Duk da kasancewar sa hakan bai zama abin ƙyama ga mutane ba. Da yawa kan rungume shi da hannun biyu. A gefe...

View All