Makalu

Ba abinda gaggawa ke haifarwa a rayuwa sai dan da-na-sani

 • Gaggawa mummunar dabi'a ce da in dan adam ya kasance a cikinta to duk abin da zai yi ba zai zama ingantacce ba. Alal misali gaggawa a tafiya, ida ka dubi titunanmu za ka ga mutanenmu suna ta sheka gudu domin zuwa wani gurin da suke so su je, amma abin takaicin shi ne in ka dubi gaggawan da ake yi ba za ta cimma muradi ba. Gaggawa na iya faruwa a bangarorin rayuwa daban-daban, kamar a aikin gini, karatu, kasuwanci da makantansu.

  Misalin gaggawa a wajen karatu shi ne, sai ka ga ɗan adam daga lokacin da ya shiga makarantan shi ko iyayensa za su iya yin buri ko gaggawa cewa suna so ya yi gaggawa ya gama, ma'ana ba damuwarsu ba ce adadin karatun da ake so ya yi, a'a sai dai gaggawan kawai a ce dansu ya kamala karatu

  Sau da dama za ka ga a harkokin kasuwanci, dan kasuwa da ke da matsakaicin jari gaggawa ta sa shi ya yi asarar dukkan abin da ya mallaka. Abin nufi anan shi ne, kana da ‘yan kudin ka da kake juyawa a kasuwa, a maimakon ka bisu a hankali, sai ka ga gaggawa tasa mutum ya ciwo mummunar bashi wai din ya kara jari, daga karshe in ba a yi dace ba kudin mutane ya hau ka dan kasuwa, kasuwancin ta ruguje.

  Don haka bai kamata muyi gaggawa a cikin al'amuranmu ba. Hausawa na cewa sau dayawa ‘sauri kan haifar da nawa.’ Abinda suke nufi anan shine mai gaggawa za ka ganshi ya fita a guje da niyyan yin wani al'amari, amma wanda ya tafi sannu a hankali sai yaje ransa a huce bai cuci wani ba shima ba'a cuce shiba.

  Saboda haka mu kara yin nazari mu gane gaggawa ba abar yi bace, bakuma abar a makalemata bane don cimma muradin rayuwarmu na yau da kullum. Allah Ya sa mu dace. Amin. Sannan za a iya duba: Idan kana son rayuwarka ta yi albarka kula da tsofaffi

No Stickers to Show

X

MAKALU DA DUMI-DUMIN SU

 • Duk mace na bukatar sanin wadannan abubuwa guda 6 kafin ta yi aure

  Posted Nov 29

  Aure abu ne mai matukar muhimmanci a rayuwar mutum don ya zamo cikar mutuntaka ta dan adam. Allah madaukakin sarki ya halicci mata daga jikin mazaje domin su matan su zama natsuwa a gare su, ya kuma sanya soyayya da shakuwa a tsakanin wadannan jinsin guda biyu.  A...

 • Ko kun san adadin yawan nutrients da jikinku ke bukata?

  Posted Nov 24

  Samun abinci mai kyau da kara lafiya, wato good nutrition, ya dace ya zamo daya daga cikin burin kowani dan adam da ke raye.  Ya kasance mun san adadin yawan abinci mai kyau da jikkunanmu ke bukata, sannan mun san addadin yadda ya kamata mu rinka motsa jikinmu, kum...

 • Yadda ake hada buttered chicken

  Posted Nov 22

  Assalamu alaikum barka da sake saduwa a fannin girke-girkenmu na Bakandamiya. A yau insha Allahu zamu gabatar da shirin yadda za ki hada buttered chicken. Abubuwan hadawa Kaza Ginger and garlic paste (citta da tafarnuwa)  Albasa Yoghurt Butter Fresh cream ...

 • Yadda ake hada papaya drink

  Posted Nov 22

  Assalamu alaikum barka da sake saduwa a cikin shirin Bakandamiya a yau insha Allahu zamu gabatar da shirin yadda za ki hada natural papaya drink Abubuwan hadawa Papaya (gwanda) Sugar Ruwa Zuma (optional) Yadda ake hadawa Farko za ki yanka gwanda ki cire ma...

 • Alamomi 8 da za ki gane cewa namiji da gaske yake

  Posted Nov 22

  So wani irin yanayi ne da kan sa mutum ya tsinci kansa a cikin wani hali na daban. Sai dai mi? Abu ne shi mai dadi a kuma gefe guda abu ne mai matukar ban tsoro. Duk da kasancewar sa hakan bai zama abin ƙyama ga mutane ba. Da yawa kan rungume shi da hannun biyu. A gefe...

View All