Makalu

Ni’imomin dake cikin wadatar zuci 

 • Wadatar zuci na nufin ɗan adam ya wadata da kaɗan daga cikin ni'imomin da Allah ya ba shi, ma'ana ya daina hangen na hannun wani. Sau dayawa za ka ga mutumin da yake da arziki amma ya bi yana ta ta da hankalinsa har ya kai ga ya kaucewa hanyar addininsa, saboda yana hangen wanda ya fishi arziki. Duk burinsa ya ga ya fi wanda yake hangowa arziki.

  Masu irin wannan hali na hangen abin wani da rashin wadatar zuci, a kullum za ka same su cikin kunci. Talaka wanda bai da komai mai wadatar zuci ya fi su kwanciyar hankali da natsuwa, za ka ga rayuwarsa tana gudana yadda ya kamata ba tare da ya zubar da mutuncin sa a idon duniya ba.

  Idan an lura da abin da ake nufi da wadatar zuci, in mutum bai da wadatar zuci to ba zai taɓa ganin daidai ba a cikin abin da yake nema, sai ya zama ya mallaki gidaje da motoci, amma zuciyarsa talauci kaman wanda ba shi da ita.

  Har a yanzu, a rayuwa in Allah ya azurtaka da wadatar zuci to kai kam ka rabauta, amma in ka samu akasin haka, to mutum na iya fadawa cikin mummunar yanayin rayuwa, daga karshe ya taɓe. Allah Ya sauwake.

  Za mu ga a al'ummar da suka gabata mafiya yawan waɗanda suka fi wahala a cikinsu su ne waɗanda ba su da dukiya, amma zuciyarsu ta wadata da abin da Allah ya ba su.

  Wadatar zuci shi ne arziki matabbaci da ake bukata ɗan adam ya same shi, amma in ka sake zuciyarka ta mutu kana zaune kana jiran a ba ka, ko kuma kana da shi kai ba za ka iya amfani da ni'imar da Allah ya ba ka ba. Shin ma mene ne amfanin tarawa, idan hakan ba za ta biya bukata ba?

  Muna rokon Allah da Ya azurta mu da wadatar zuci. Amin. Sannan za a iya duba: Ba abinda gaggawa ke haifarwa a rayuwa sai dan da na sani da hanyoyi 8 da mutum zai bi ya samu wadatar zuci da sauransu.

No Stickers to Show

X

MAKALU DA DUMI-DUMIN SU

 • Duk mace na bukatar sanin wadannan abubuwa guda 6 kafin ta yi aure

  Posted Nov 29

  Aure abu ne mai matukar muhimmanci a rayuwar mutum don ya zamo cikar mutuntaka ta dan adam. Allah madaukakin sarki ya halicci mata daga jikin mazaje domin su matan su zama natsuwa a gare su, ya kuma sanya soyayya da shakuwa a tsakanin wadannan jinsin guda biyu.  A...

 • Ko kun san adadin yawan nutrients da jikinku ke bukata?

  Posted Nov 24

  Samun abinci mai kyau da kara lafiya, wato good nutrition, ya dace ya zamo daya daga cikin burin kowani dan adam da ke raye.  Ya kasance mun san adadin yawan abinci mai kyau da jikkunanmu ke bukata, sannan mun san addadin yadda ya kamata mu rinka motsa jikinmu, kum...

 • Yadda ake hada buttered chicken

  Posted Nov 22

  Assalamu alaikum barka da sake saduwa a fannin girke-girkenmu na Bakandamiya. A yau insha Allahu zamu gabatar da shirin yadda za ki hada buttered chicken. Abubuwan hadawa Kaza Ginger and garlic paste (citta da tafarnuwa)  Albasa Yoghurt Butter Fresh cream ...

 • Yadda ake hada papaya drink

  Posted Nov 22

  Assalamu alaikum barka da sake saduwa a cikin shirin Bakandamiya a yau insha Allahu zamu gabatar da shirin yadda za ki hada natural papaya drink Abubuwan hadawa Papaya (gwanda) Sugar Ruwa Zuma (optional) Yadda ake hadawa Farko za ki yanka gwanda ki cire ma...

 • Alamomi 8 da za ki gane cewa namiji da gaske yake

  Posted Nov 22

  So wani irin yanayi ne da kan sa mutum ya tsinci kansa a cikin wani hali na daban. Sai dai mi? Abu ne shi mai dadi a kuma gefe guda abu ne mai matukar ban tsoro. Duk da kasancewar sa hakan bai zama abin ƙyama ga mutane ba. Da yawa kan rungume shi da hannun biyu. A gefe...

View All