Rubutu

Blogs » Tarihi da Al'adu » Sammu: Dalilan yinsa a tsakanin al'umma

Sammu: Dalilan yinsa a tsakanin al'umma

 • Sammu magani ne, kuma asiri ne da wasu tsirarun mutane kan yi don kokarin lahanta wasu al'umma bisa wadansu dalilai. Ba dole bane mutum ya san wadda ya yi wa wani sammu ba, kuma yana yiwuwa a zuba wa mutum a ruwa ya sha, ko a abinci, ko kuma a binne a kasa ya taka, da dai sauran wasu hanyoyi da ake bi wajen aiwatar da shi.

  Yawanci dai sanin kowa ne, masu yin sammu su ne, malaman tsibbu. Idan aka yi wa mutum sammu yakan iya ksancewa a daya daga cikin wadannan halaye:

  1. Mutum na iya barin gari
  2. Yakan sa mutum ya rasa wani abin da yake da shi mai muhimmanci.
  3. Yakan sa mutum ya haukace
  4. Mutuwa

  Dalilan da suke sa a yi wa mutum sammu

  Akwai wasu dalilai da suke sa ayi wa mutum sammu, ko kuma muna iya cewa sanadojin sammu, wadannan kuwa su ne:

  1. Gaba
  2. Tsana
  3. Kiyayya
  4. Bakin ciki
  5. Kishi 
  6. Hassada

  Mai karatu na iya duba: Alamomi da yadda ake furta kandun baka cikin al'adun Hausawa da sauransu.

Comments

0 comments