Makalu

Tsangwama da mata ke sha wurin mazaje a shafukan sada zumunta

 • Kamar yadda kowa ya sani, mata mutane ne masu yanci, da daraja, da kima, da girma, da mutunci, da karamci, tare da girmamawa a cikin al'umma. Amma irin tsangwana da suke fuskanta a shafukan sada zumunta, wato social media, wurin wasu mazaje al'amarin ba'a cewa komai. Watakila inda wadannan maza sun san dalilan dake kawo matan wadannan shafuka da za su basu uzuri.

  Mata sun kasu kaso shida a shafukan sada zumunta:

  1. Na farko sun zo social network ne domin su sada zumunta ga yan uwansu, kawayensu na makaranta, tare kuma da yin wasu sababbi na kawayewa daga nan gida Najeriya da kuma da kasashen ketare.
  2. Kashi na biyu kuma sun zo ne domin kawai sun ga kawayensu suna yi, ko kuma saboda jin labarinsa da  suke yi a gari da kuma kafafen yada labarai, wato dai suma sun zo ne su ga me ake yi a ciki.
  3. Kaso na uku kuwa sun zo ne neman saurayi dan kwalisa, mai iya kalaman soyayya, mai abin hannu (ga yammata kenan), ko kuma bazawari (ga zawarawa).
  4. Na hudu kuwa kawai sun zo ne domin neman ilmin addini, ko ilmin sana'a, ko kuma ilmin boko, domin kuwa babu kalar zaure, watau group din da babu.
  5. Kaso na biyar kuwa, kawai gasu nan ne, babu wata hujja ko dalili na zuwan nasu. In ta yi dadi suyi dariya, idan kuma ta baci suyi Allah wadarai.
  6. Kaso na shida kuwa sune wadanda suka hada biyu, ko uku koma hudu daga cikin hujjojin da aka lissafa a sama, wato dai su hujjar zuwansu tafi daya.

  Amma duk da wadannan hujjoji na zuwan matan social network, wasu mazan basa duba haka, burinsu kawai matan su tsaya su sauraresu, ko da kuwa abinda suka zo dashi ba mai ma'ana bane. Na kan tausayawa mata idan na tuna tarin sako cikin inbox nasu, kuma kowa muradinsa a mayar masa da martani, wato a yi masa reply. Haka na faruwa da mace musamman idan mace ta saka hotonta, ko kuma ta fiye yawan magana.

  Akasarin mazan dake yawan turawa mata irin wadannan wasiku, za ka samu kowa babban burinsa maccen ta saurareshi shi kadai, baya tunanin sauran masu irin halayyarsa. Idan kuwa aka samu akasin haka, to ranar zata sha zagi da tsinuwa.

  Baya ga aika wa yan matan da yawan wasiku, haka kuma, za ka ga ana dibarsu ana zubawa a zauruka, wato group daban-daban, mai amfani da mara amfani.

  Abin tambayar a nan shine, wai shin masu irin wannan halayyar an gaya musu saboda su matan suka zo social network ne
  Babu yan mata da zawarawa ne a garinsu ne? Ko kuwa wani mugun hali garesu da baza su iya neman na garinsu ba? Shin ko kun san da cewa akwai aljanun gaske a cikinsu kuwa? Ko kun san da cewa ba dukansu ne matan ba? Akwai maza da ke amfani da sunan matan? Ko kun san da cewa da yawa daga cikin matan suna da samarin da suke so?

  Wadannan tambayoyi da makamantansu suna nan jibge, amma fa sai anyi tunani. Don haka ya kamata mu gane kuma mu gyara.

  Mai karatu na iya duba: Illolin yawon bariki

No Stickers to Show

X

MAKALU DA DUMI-DUMIN SU

 • Yadda ake hada KFC chicken

  Posted Thu at 10:11 AM

  Assalamu Alaikum, barka da sake saduwa a cikin shirin girke-girken Bakandamiya tare da ni mai gabatar muku da shirin. A yau in sha Allah zan nuna mana yadda ake hada KFC chicken. Abubuwan hadawa Kaza Flour Man gyada Bread crumbs ko cornflakes Kwai Maggi ...

 • Yadda ake hada egg masala

  Posted Thu at 9:57 AM

  Assalamu Alaikum, barkanmu da sake saduwa a cikin shirin girke-girkenmu na Bakandamiya. A yau na zo mana da yadda za a hada egg masala a saukake. Abubuwan hadawa Dankalin turawa Albasa Carrots Maggi Mangyada Kwai Yadda ake hadawa Farko za ki wanke dankal...

 • Jini Baya Maganin Kishirwa: Babi na Uku

  Posted Jan 12

  Ku latsa nan don karanta babi na biyu. Sakinah ta share hawayen da ke zuba kan kuncinta kafin ta ce. "Insha Allahu Umma zan yi aiki da dukkan abin da ki ka umarce ni da shi da yardar Allah, ba zan taɓa baki kunya ba". "Yauwa Sakinah Allah ya yi miki albarka". "Amin"...

 • Yadda ake baked awara

  Posted Jan 11

  Barka da sake saduwa a cikin shirin girke-girkenmu na Bakandamiya. A yau na zo maku da sabon girki wato yadda za ku hada baked awara. Abubuwan hadawa Awara Kwai Carrots Seasoning Cooked minced meat Muffin tray Albasa Yadda ake hadawa Farko za ki yanka a...

 • Bayanan masana game da ingantattun hanyoyin ƙayyade iyali

  Posted Jan 8

  Mene ne ƙayyade iyali? Ƙayyade iyali ko tazarar iyali ko kuma family planning a Turance wani mataki ne da ma'aurata kan dauka don hana mace daukan ciki domin rage yawan haihuwa akai-akai, ko ƙayyade yawan ‘ya’ya da za ta haifa ko dai ma don wasu dalilai na ...

 • Ma'aurata: Babi na Biyu

  Posted Jan 8

  Idan baku karanta babi na daya ba to ku latsa nan don karantawa. Ana kiran sallah asuba ta farka daga bacci addu'an tashi daga bacci tayi kafin tayi miƙa tana salati ga Annabi S.A.W kai dubanta tayi a gefen da Fahad yake kwance tayi, har yanzu yana nan yana bacci kamar...

View All