Makalu

Fa'idodin Habbatus Sauda ga mai matsalar haihuwa ko AIDS

 • Binciken Manyan Likitocin zamani ya tabbatar da cewar Habbatus Sauda tana karfafa garkuwar jiki. Don haka ana kyakyawan zaton cewar masu fama da cutar AIDS idan suna amfani da ita (mai ko gari) zasu samu karin lafiya sosai a jikinsu.

  A samu zuma mai yawa (kamar kofi 3) a sanya garin Habbatus Sauda cokali 7, da garin Zaitun cokali 4, da garin zogale cokali 3. Haka kuma a sanya citta da kayan kamshi a ciki, sannan a gauraya a rika sha cokali 2 safe da rana da yamma kafin cin abinci.

  Wannan fa'ida zata yi amfani ga masu fama da cutar AIDS, cutar SIKILA, TYPOID FEVER, da sauransu.

  Habbatus Sauda tana magance matsalar rashin haihuwa. Matar da take da wannan matsalar, ta rika soya 'ya'yan Habbatus Sauda tana gaurayawa da zuma tana taunasu tana cinyewa. Kamar cokali biyu safe da yamma a kullum. In sha Allahu koda tana da dattin mahaifa ko rikicewar jinin al'ada, komai zai daidaita.

  Har'ila yau, Habbatus Sauda tana maganin kurarrajin baki da na makogoro idan ana kurkura bakin da ita kuma ana hadiyanta bayan an dumamata kadan.

  Shan Habbatus Sauda da zuma tana maganin matsalar tsakuwar mara, watau appenditixs.

  Habbatus Sauda tana maganin basur. Idan aka hadata (garinta) da garin ganyen sabara, sai a tafasawa ana shan kofi guda na ruwan kullum da safe.

  Allah ya sa a dace. Sannan za a iya karanta:Amfanin man zaitun ga rayuwar bil'adama

No Stickers to Show

X

MAKALU DA DUMI-DUMIN SU

 • Jini Baya Maganin Kishirwa: Babi na Hudu

  Posted Fri at 4:38 PM

  Ku latsa nan don karanta babi na uku. Yana fitowa daga wankan kai tsaye gaban mudubi ya nufa, tun kafin ya kai ga ƙara sawa idanuwansa suka tsinkayo masa  ƙananan kaya ya she akan gado riga da wando,  da dukkan alamu Sakinah ce ta ajiye masa su, sai faman wan...

 • Yadda ake hada spring chin-chin

  Posted Thu at 10:16 AM

  Assalamu Alaikum. Barkan mu da warhaka. Ayau na sake zuwa mana da sabuwar makala ta girke-girke wacce ciki za mu koyi yadda ake soya spring chin-chin. Abubuwan hadawa Flour (4 cups) Baking powder (1 teaspoon) Butter (125grms) Mangyada Gishiri (1 teaspoon) Ya...

 • Yadda ake hada KFC chicken

  Posted Thu at 10:11 AM

  Assalamu Alaikum, barka da sake saduwa a cikin shirin girke-girken Bakandamiya tare da ni mai gabatar muku da shirin. A yau in sha Allah zan nuna mana yadda ake hada KFC chicken. Abubuwan hadawa Kaza Flour Man gyada Bread crumbs ko cornflakes Kwai Maggi ...

 • Yadda ake hada egg masala

  Posted Thu at 9:57 AM

  Assalamu Alaikum, barkanmu da sake saduwa a cikin shirin girke-girkenmu na Bakandamiya. A yau na zo mana da yadda za a hada egg masala a saukake. Abubuwan hadawa Dankalin turawa Albasa Carrots Maggi Mangyada Kwai Yadda ake hadawa Farko za ki wanke dankal...

 • Jini Baya Maganin Kishirwa: Babi na Uku

  Posted Jan 12

  Ku latsa nan don karanta babi na biyu. Sakinah ta share hawayen da ke zuba kan kuncinta kafin ta ce. "Insha Allahu Umma zan yi aiki da dukkan abin da ki ka umarce ni da shi da yardar Allah, ba zan taɓa baki kunya ba". "Yauwa Sakinah Allah ya yi miki albarka". "Amin"...

 • Yadda ake baked awara

  Posted Jan 11

  Barka da sake saduwa a cikin shirin girke-girkenmu na Bakandamiya. A yau na zo maku da sabon girki wato yadda za ku hada baked awara. Abubuwan hadawa Awara Kwai Carrots Seasoning Cooked minced meat Muffin tray Albasa Yadda ake hadawa Farko za ki yanka a...

View All