Rubutu

Blogs » Girke-Girke » Yadda ake awarar waken soya

Yadda ake awarar waken soya

 • Yadda ake awarar waken soya za mu koya a darasinmu na yau.

  Abubuwan  hadawa

  • Waken soya
  • attarugu
  • albasa
  • ruwan tsami ko dan tsami
  • dandano

  Yadda ake hadawa

  1. Da farko zaki jika wakenki idan ya jiku, sai ki kai a markado miki.
  2. Idan an kawo daga markade sai ki dan diga manja aciki, ki dan kara ruwa saiki tace.
  3. Idan kin gama ki zuba a tukunya ki dora a wuta.
  4. Sai ki dauko attarugunki ki jajjaga ki yanka albasa.
  5. Ki dinga kula da wannan ruwan awararda ki ka dora idan ya fara tafasa saiki dauko ruwan tsaminki ki zuba a ciki, za kiga duk ta hade jikinta
  6. Sai ki zuba albasa da attarugu da dandano aciki, idan ta dan kuma dahuwa saiki samu abin tata ki juye awaran a ciki ki daure shi sosai ki samu abu mai nauyi ki danne ta ko kuwa ki rataye yadda ruwan zai dige daga jikin awaran.
  7. Idan kin tabbatar ruwan ya gama digewa sai ki dora mai a wuta ki fara suya.

  Shike nan awarki ta kammala. Sannan za a iya duba wasu girke girken, kamar: Yadda ake potato daughnut  da yadda ake madaran waken-suya da kuma Yadda ake milkshake na kankana da sauransu.

Comments

0 comments