Rubutu

Blogs » Kagaggun Labarai » Dolaki Karambana (labari na daya)

Dolaki Karambana (labari na daya)

 • Awowina dubu daya da dari hudu da arba’in ina kutsawa a cikin dokan daji da kafa. Kwanaki sittin kenan ko nace watanni biyu. Na lashi tokobin gwara na mutu da na koma ba tare da na samu ganin boka kallamu ba. Kudi shine burina, wallahi na gaji da bakar talauci. Ni kenen kudi, mota kyawawan mata sai dai na gani ko na hanga? Da yammaci Allah ya bani sa’an isa kungurmin daji da yake. Naga abin mamaki, don manyan motoci suna kaiwa da kawowa a wajen sa.

  Dana bayyana a gabansa, kafin na fada masa damuwata ya karanta mini.

  ‘Kai ne Dolaki karambana, duk duniya baka da buri sai kudi, baka kaunar shiga Aljanna kamar da kake burin yin kudi’. Bokan ya fada mini. ‘Haka ne boka, don idan na samu kudin zan nemi Aljanna’. Na ba shi amsa. ‘Daga Najeriya kake ko?” ‘Kwarai kuwa’. Na bashi amsa. Yayi dan kulunboto. Can ya mika min usir. “Ga wannan idan ka sarrafa shi yanda ya kamata babu kai babu talauci”. Na kalle shi. “Ya kai boka, nifa ba dan kwallo bane, yaya zaka bani usir?”.

  Ya kalleni “kaga masu manyan motoci dake zuwa nan, ba wanda na bashi abin da zai yi saurin azurtawa kamar wannan. Kaje kasarka najeriya duk wanda kasan ya sati dukiya, ka hura gwannatin kasarka zata raba dukiyar ta baka kaso daga ciki”.

  Ban yi kasa agwuiwa ba na dawo kasata Najeriya, na bincika labarin ya tabbata. Nanfa na dukufa wajen neman barayin gwannati. Allah ya bani sana nayi kyakyawan kamu, an kuma sami kudin aka sa ranar da za a bani nawa kason. A safiyan ran da za’a bani wasu jami’an tsaro suka daukeni ina murna. Suka kai ni wani gida, na samu wasu kattin attajirai. "kaine Dolaki karambana naira.com?’ ‘nine ranka shi dade ai ni na yi shunen’. Na bashi amsa ‘yayi kyau ku buge shi!”.

  Kafin na bude baki na ji sanduna suna rige-rigen sauka a jikina. Ban san kwana nawa nayi ba, na farfado na jini cikin wani matsatsi, ina nade. Gumi na bulbula a duk jikina. Na yi yunkuri na tashi na gagara, nunfashina na kokarin sake yankewa. Nan take na sanar da kaina idan ban fita daga nan ba babu shakka zan kwana kabari. Na yi yunkuri da karfin Allah, na ji abu kamar itace ya mai da ni. Can naji kamar tafiyar mutane. Nasaurara sai na ji kamar ana tononi. Bai dau lokaci ba na fara ganin haske. Bai jima ba aka tsamoni waje aka warware likkafani da ke jikina, nan ne na gane wa idanuna a makabarta nake na tashi zan gudu….

  Ku dannan nan don ci gaban labarin.

Comments

4 comments