Featured Create an Ad

Makalu

Blogs » Ra'ayoyi da Tahalili » Rushe tarbiya ta duniyar yanar gizo

Rushe tarbiya ta duniyar yanar gizo

 • Ko mun taba tunani tare da tambayar kanmu da kanmu illar shudanya da yanar gizo ga ‘ya’yamu? Mun kuma taba tambaya meyasa bayan mun tarbiyarta da ‘ya’yanmu kan tarbiya na gari sai a wayi gari munanan halaye da dabi’u su bayyana garesu? To ga duk iyalan da suka dauki yanar gizo a tafin hannunsu, amsar wannan tambaya itace YANAR GIZO.

  Idan muka dauke ilimantarwa da shafukan yanan gizo keyi acikin al’umma, akwai gurbatattun tarbiya wanda ke tafiya tamkar wutar daji cikin al’umma. Babban kuskure da iyaye keyi a yau shine mallaka wa ‘ya’yansu daga shekaru goma zuwa sha.., manyan wayoyi. Yara kan iya samun ilimi da damar iya shiga shafuka daban-daban na yanan gizo, adalilin hakan. Haka kuma kuruciya kan iya daukansu zuwa ga:

  1. Abota da ‘yan iska ko ‘yar isaka; cikin sauki za su koyi kalaman batsa masu rasa jiki da haifar da shauki.
  2. Yara kan gina gobensu cikin burin rayuwa ta sharholiya da bushasha.
  3. Samo sabbin dabi’u sabanin na al’adu ko addininsu.
  4. Damar ganin hotunan mace ko namiji tsirara, don haka yara kan iya siffanta tsiraicin mace ko namiji babba ko karami dogo ko doguwa, gajere ko gareruwa.
  5. Sukin iya samun adireshin bidiyo na fina-finan batsa, don haka sukan kalla alokacin da suke bukata. Wannan shike basu ilimin sanin duk wani lungu dake jikin mace da duk wani mahadi dake jikin namiji.

  A yayin da balaga ya tasamma yaro ko yarinya, tuni suna da hanyoyi tada sha’awa, za su fara hikimanta yanda bukata zata biya. A wannan mataki ne:

  1. Suke fara kwarewa da hirar batsa ta waya ko yanan gizo.
  2. Kokarin tallata surar halittarsu ta hanyar sanya hotuna mai bayyana surar halittarsu.
  3. Zina ta waya ko yanan gizo. Sukan iya kulle kansu a daki suke wasa da al'aurunsu da kuma yin musayar kalaman batsa har bukata ta biya.
  4. Kulla kawance don yin madido tsakanin mace da mace.

  A irin wadannan boyayyun tarbiyar duniyar yanan gizon, sakamako da iyaye da al’umma ke samu sune:

  1. Kin rabuwa tsakanin kawaye da suke madigo koda ace sun yi aure.
  2. Amfani da azzakarin roba ga mace don biyan bukatarta, ko ta yi aure mijinta ba damuwarta bane.
  3. Shiga na batsa da kallon babba a tsakiyar ido
  4. Yin zina da abokin mahaifi, ko kanwar mahaifiya (budurwa).
  5. Iya sanin surar mace ko namiji (ba sai a tsiraraba) ko da mahaifine ko mahaifiya.

  BABU SHAKKA YANA DA KYAU ‘YA’YANMU SU KASANCE MASANA KAN DUNIYAR KIMIYYA DA FASAHA, AMMA, YA ZAMA DOLE MUSAN ILLOLIN DAKE CIKINSA. Sannan mai karatu na iya duba: Kuruciyar bera a kasata Najeriya da makamancin hakan.

No Stickers to Show

X

Da Dumi-Dumin Su

 • A karkashin ilimin kimiyyar lissafi wato (physics), yau zamu yi karatu ne akan wata maudu’i mai matukar mahimmanci. Wannan maudu’in kuma ba wata ba ce face heat. Idan muka tuna a makalar da ta gabata mai suna energy mun ce heat nau’i ne daga cikin nau’ukan energy. A yau zamu ...
 • A wannan makala dalibai za su ga yadda za a yi bayani game da work da kuma power dama yadda ake solving mathematical problems. Workdone ko work a physics yana nufin a yi multiplying na force da displacement. Sa’annan aikin yana gudana ne a direction na force. Idan har W ya kasance work, F kum...
 • Vanilla cupcake kalar cupcake ne da yara kar harma manya su ke so sosai. Na san muta ne da dama suna sha'awar koyon yadda za a sarrafa shi. Saboda haka a yau muka kawo muku yadda ake yinsa domin mai sha'awar koyo. Wannan recipe idan kin bi shi yadda ya ke, za ki samu cupcakes guda 20 ne dai dai. Ab...
 • Ku latsa nan don karanta babi na takwas. Ga ɗaurin Zahra Buhari. Ni dai ban iya ɗaurin ba. Yayata ke kafa min in zan je biki. In kuwa fita yawo ne ɗaurin 'yan Hausa na ke yi mai lankwasa a gaban nan. "Mama!" Ta furta cikin mamakin ganin ta. Bata saurareta ba bare ta amsa, cikin hanzari ta isa bak...
 • A kwanakin baya na ga wani tattaunawa a social media game da zuwa aiki ga mata, musammam matan aure da kuma mata masu yara. Abinda na lura shi ne yawanci mazaje ba su fiya son matansu na zuwa aiki ba duk da cewa yawancin mazan na so a ce matansu sun yi karatu sosai kuma sun waye da sanin abubuwan ra...
 • Ku latsa nan don karanta labarin Mai Haƙuri Ya Kan Dafa Dutse. A ƙasashen ƙetare an yi wani ɗan Sarki ana kiran sa Bihizadu. Ya kasance kyakkyawa ne, kuma yana da kirki domin kuwa yana zama tare da talakawa da fatake da attajirai. Mutane suna son sa, sai dai yana da saurin ƙagauta a al'amuran ...
View All