Makalu

Sabbin Makalu

View All

Wainar semobita

 • Abubuwan hadawa

  1. Garin semobita
  2. Yis (yeast)
  3. Sukari
  4. Gishiri
  5. Albasa
  6. Man gyada
  7. Ruwan dumi

  Yadda ake hadawa

  1. Dafarko zaki zuba garin semobitanki acikin kwano mai fadi
  2. Sai ki zuba yeast da sikari da gishiri daidai misali kamar dai yanda zaki zuba idan dai zaki yi wainar shinkafa
  3. Sai ki kawo ruwan duminki ki zuba ki na mai juyawa da muciya a hankali har sai kwa6in ya yi daidai da kullin wainar (ruwan dumin yana taimakawa kullin wajen tashi da wuri amma idan akwai rana zaki iya kwabawa da ruwan sanyi). Sai ki yi ta juyawa har na tsawon minti 15.
  4. Idan yayi zaki ga ya yi mulmul yana kamshi, sai ki rufe ki barshi a rana har sai ya tashi
  5. Idan ya tashi sai ki yanka albasa a cikin kullin, sai kuma ki dora tanda ko kasko (frying pan)
  6. Zaki ga tayi washar da ita kamar wainar shinkafa
   Ana cinta da miyar taushe ka romon naman kan rago ko kulikuli

  A ci dadi lafiya. Sannan mai karatu na iya duba: Farfesun dankali da lemun abarba da kwakwa da sauransu.

Comments

0 comments