Rubutu

Blogs » Girke-Girke » Yadda ake jellebi

Yadda ake jellebi

 • Abubuwan hadawa

  1. Filawa
  2. Madara
  3. Suga
  4. Leda
  5. Mai

  Yadda ake hadawa

  1. Ki tankade filawarki, ki sa baking powder kadan, ki jiqa suga da ruwa kadan, sai ki zuba madaran ruwa ki hade su wuri daya da filawar. Ki juya su hade sosai, kwabin ya yi kamar kwabin lallen zane.
  2. Sai ki dauko Leda da ake zanen lalle ki zuba kwabin ciki, ki dora kwanon suya ki zuba mai.
  3. Idan manki ya yi zafi ki dauko leda ki zuba kwabin a ciki, sai ki huda bakinta.
  4. Ki dauki wannan kwabi da ki ka sa a leda ki rika matsawa a cikin mai, zai yi cycle kamar igiya. Idan ya soyu ki kwashe ki koma yin wani irinshi har ki gama.

  Karin bayani

  Kina iya sa food color, amma yellow a kwabin in kina so, zai yi kamar na Indiyawa.

  Na gode. Sai mun hadu a girki na gaba. Sannan mai karatu na iya duba: lemun citta da lemun tsami a sauki da dambun masara dasauransu.

Comments

0 comments