Rubutu

Blogs » Girke-Girke » Yadda ake kosai

Yadda ake kosai

 • A yau za mu koyi yadda ake kosai daki-daki.

  Abubuwan hadawa

  1. Wake kofi 3
  2. Maggi
  3. Gishiri
  4. Kayan kamshi
  5. Man gyada
  6. Attarugu
  7. Albasa
  8. Tattasai

  Yadda ake hadawa

  1. Da farko uwargida za ki wanke wakenki ki cire hancin ya fita tas. Sai ki jika shi kamar na minti goma.
  2. Idan ya jika sai ki zuba attarugu da tattasai, sai ki yanka albasa ki bayar a kai markade.
  3. Idan ankawo sai ki zuba maggi da gishiri da kayan kamshi.
  4. Sai ki dauko ludayi mai kyau babba sai ki ta bugawa, ya bugu sosai.
  5. Anan sai ki dora manki a wuta. Idan ya yi zafi, sai ki sa karamin ludayinki ki na diba ki na sawa a manki kadan kadan har ki gama, ammafa ki tabbatar ki na yi ki na bugawa.

  Za’a iya ci da kunu ko koko ko daima shayi. Da fatan kuna jin dadin ayyukannamu. Sai mun hadu a girki na gaba. Taku a kullum Rabiat Muhammad Babanyaya mai fatan jin dadinku a koda yaushe. Sannan za a iya duba: fanke (puff-puff) da dahuwar shinkafa da wake da makamantansu.

  Hakkin mallakan hoto (photo credit): jiji.ng 

Comments

0 comments