Rubutu

Blogs » Girke-Girke » Yadda ake kunun semovita

Yadda ake kunun semovita

 • Asssalamu alaikum warahmatullah. Barkanmu da warhaka da fatan kuna lafiya. Yau zamu yi kunun semonvita ne. 

  Abubuwan hadawa

  1. Semonvita kofi 1/2
  2. Madara cokali 6
  3. Suga dai dai dan dano

  Yadda ake hadawa

  1. Da farko uwargida za ki wanke tukunyarki, ki sa ruwa ki dora a wuta ya tafasa.
  2. Sai ki dauko semonki ki dama da ruwa ya yi kamar za kiyi talge.
  3. Sai ki duba idan ya tafasa sai ki zuba a kan ruwan ki juyashi sosai.
  4. Idan ya yi sai ki sauke ki zuba a kwano ki sa madara da suga sai ki juya ki zubawa kowa a kofi.

  A sha dadi lafiya. Na gode sai mun hadu a girki na gaba. Sannan za a iya duba Fanke (puff-puff) da lemun mangwaro da makamantansu. 

  Hakkin mallakan hoto (photo credit): onegreenplanet

Comments

1 comment