Rubutu

Blogs » Girke-Girke » Yadda ake dafa faten tsakin masara

Yadda ake dafa faten tsakin masara

 • Assalamu alaikum warahmatullah, barkanmu da sake haduwa a cikin wannan fili mai albarka. A yau zamu yi fatan tsakin masara.

  Abubuwan hadawa 

  1. Tsakin masara
  2. Manja
  3. kayan Miya
  4. Albasa
  5. Kayan kanshi.
  6. Nama ko kifi
  7. Dakakkiyar gyada
  8. Maggi
  9. Gishiri
  10. Yakuwa da alayyahu

  Yadda ake hadawa 

  1. Da farko uwargida za ki wanke tsakin masaranki ya fita tas ki sa a matsami ki tsame shi.
  2. Sai ki wanke namanki ki yanka albasa ki sa maggi ki tafasa shi.
  3. Sai ki jajjaga kayan miyarki sannan ki   kwashe naman sai ki zuba manja ki sa albasa ki soya naman,
  4. Sai ki zuba kayan miyarki ki soyashi sama sama. Idan ya yi sai ki zuba ruwa,
  5. Ki sa maggi da gishiri da kayan kamshi,  sai ki rufe,
  6. Ki yanka yakuwa da alaiyahu ki wankesu saf, sai ki duba Idan ruwan ya tafasa sai ki zuba tsakin masaranki da ki ka wanke.Ki juya shi sosai sai ki rufe.
  7. Ki bashi minti ashirin sai ki duba idan ya yi sai ki zuba  ganyanki ki juya ki rufe ya yi minti biyu.
  8. Sai ki sauke ki zubawa kowa na shi. Fate abincin marmari ne, a gwada a gani.

  Na gode, sai anjima. Sannan mai karatu na iya duba: Yadda ake hada egg pizza da kuma yadda ake kunun alkama da makamantansu.

  Hakkin mallakan hoto(photo credit): imgrum

Comments

0 comments