Rubutu

Blogs » Girke-Girke » Yadda ake gireba

Yadda ake gireba

 • Abubuwan hadawa

  1. Fulawa
  2. Suga
  3. Ridi (kantu)
  4. Man gyada

  Yanda ake hadawa

  1. Da farko uwargida za ki tankade fulawarki a roba mai dan fadi. Sai ki jika sugarki.
  2. Sai ki zuba man gyada kadan sai ki juyashi sosai zaki ga ya yi wara wara
  3. Sai ki dauko jikakken suga ki kwaba fulawarki kar ya yi ruwa, za ki yishi kamar na cincin.
  4. Sai ki ringa diba ki na sawa a hannunki ki na dunkulawa da dan fadi harki gama.
  5. Sai ki barbada ridi a kai sai ki dauko tiren oven dinki ki shafa man gyada sai ki jera kisa a cikin oven dinki ki gasa idan ya yi sai ki dauko ki kwashe. sai aci

   Na gode, sai anjima. Sannan mai karatu na iya duba: Lemon zakida madara da egg pizza da makamantansu.

Comments

0 comments